Yar Malam ta koma
Salamu alaikum masoya wannan Shiri naku mai farinjini wato Yar Malam Muna sanar daku cewa yanzu haka ananan ana cigaba da daukar Shirin inda ya chanza sabon salo wanda baku taba ganiba to zaku ganshi a cikin wannan Shiri namu in Allah yaso ,da Kuma sabbin fuskoki Wanda da babu su zakuga yadda ake cigaba da ganin lallai Sai an batar da hankalin marainiya Yar Malam Nomau amma Allah yana kareta tana tsallake duka Wani tuggu chikin Ikon Allah. Kuma zakuga yanda yaran Munzali gurgu sukaci amanarsa zasu yimasa duka Sai Sani yazo ya kwace shi mai makon gurgu yayimasa godiya Sai ma kara tsanarsa yayi shidai Sani yayine domin Allah baice masakomaiba. Shikuma kamaye awon igiya ashe akwai dukiyar Malam Nomau a hannunsa ba wanda yasani sai shi Sai ya yanke shawara yaje ya kaiwa magada abinsu Kuma da yaje Sai ya fahimci cewa za'a cinyemata Sai yaje gurin mai gari don ya kafa shaidu Amma mai gari yace yaje ya cigaba da rikewa har Sai annemeshi,Wanda hakan baiwa Malam...