YAR MALAM EPISODE 2. hsusa film analysis
Bayan Ladidi ta fito daga gidan Malam Idi, sai Dogo — ɗan gidan Malam Idi — ya tareta a hanya da nufin wulakanta ta.
Duk da abincin da ya kwace a cikin gida bai isaba Ladidi kuwa ta dage da addu'a, taki tsayawa. Cikin ikon Allah sai ga wani bawan Allah ya bayyana ya kawo mata ɗauki. Ya doke Dogo har ya fadi ƙasa. Da ya duba, sai ya ga wani saurayi tsaye.
Saurayin ya daka masa tsawa, yana tambaya:
“Me ya haɗaka da ita?” Dogo yana kallon sa a fusace
Ya amsa da cewa 'yar uwarsa ce. Saurayin ya ce:
“To me ya sa zaka ci zalinta?”
Sai ya kore shi ya tafi.
🧕🏼 Ladidi da Sani
Sai saurayin ya tambayi Ladidi me ya faru. Tana kuka, ta bashi labarinta. Ya tausaya mata sosai har ya ba ta kyautar ₦500, sannan ta koma gida, shi kuma ya tafi.
🏡 Gida: Tattaunawar Ladidi da Mahaifiyarta
Da ta isa gida,Mama ta ga Ladidi cikin wani irin yanayi na tausayawa ta tafiya da kyar sai ta kura mata ido tana so taji abin da ya faru.
Ladidi tazauna da gajiyawa tace:
Ladidi:
"Mama ai lamarin yayi zafi, korar kare Baba yayimin, Dogo kuma ya kwace abincin da Inna ta bani." Tana kallon Ladidi da jimami.
Mahaifiyarta ta ce:
“Dama abinda muke gudu ke nan, gashi yanzu ya faru. Na dade da fahimtar halin Malam Idi.” Ladidi tana jin yunwa sai Mama taga kudi a hannunta tace:
"wannan Kudin fa?. Ladidi ta kalli kudin itama sai tace:
"Ai wannan kudin wannan saurayin ne yabani su."Mama ta girgiza kai sai tace:
"Ta ce ta sayo mana ƙwaki da wannan kuɗin da aka baki." Ta fita kasuwa domin sayen kwakin.
🪖 Shigowar Soja da Mutuwar Malam Nomau
Wani bawan Allah mai suna Soja, ya iso gari, ya nufi gidan Malam Nomau. Sai suka ci karo da Malam Idi. Malam Idi ya sanar da shi cewa Malam Nomau ya rasu. Soja ya yi mamaki da jin wannan labari:
“Yanzu na shigo gari, kai! Allah ya jikansa.” Inji soja.
Malam Idi ya ce:
“Bari dai ba wannanba, ina gonakin da kake kula da su? Zan tattara su, domin yanzu dukiya ta koma hannuna. Gobe nake so ka kawo komai.” Soja ya kalleshi da mamaki.
Soja ya ce zai kawo, amma ya nemi lokaci. Amma Malam Idi ya dage Da Adobe yake so akawomasa komai.
Hoton soja da Malam Idi
🤐 Amman Soja..
Ashe shima Soja mugun ƙansa ne. Yana shirin kwace dukiyar marayu — dukiyar Malam Nomau. Ya fara nuna goyon baya da soyayya na karya ga iyalin Ladidi, yana ba su ‘yar kyauta, amma a zuciyarsa da nufin mallakar komai dake gunsa.
⚔️ Rikici Tsakanin Soja da Malam Idi
Malam Idi bai yarda da Soja ba. Ya ce ba zai barshi ya kwace dukiyar marayun ba. Soja ya dage da cewa zai shiga cikin lamarin. Haka rikici ya kaure tsakanin su biyu.
👑 Malam Idi Ya Je Gaban Mai Gari
Malam Idi ya garzaya wajen mai gari don kai ƙararsa. Bayan ya gama bayani, sai mai gari ya ce:
“Wane ne Soja? Aiko ba zai yiwu ba. Garin nan nawa ne. Idan ya kawo wata gardama sai in kore shi.”
Soja ya iso daga nesa, ya hango Malam Idi. Ya yi masa wata irin harara ya karaso. Ya zauna, ya gaishe da mai gari. Ya amsa sama-sama.
Mai gari ya daka masa harara ya ce:
“Kai Soja! Fita daga idona. Kai fa yaron marigayi Malam Nomau ne, ba dan uwansu ba. Me ka ke nema? Meye naka na shiga maganar gadonsa.”
Soja ya ce:
“Ni dai ina so in rabawa magada hakkinsu ne ba wani abu ba.”
Mai gari ya ce:
“To ba kai ne dan uwansu ba. Kar ka sake shiga lamarinsu domi ba dangin iya babu na Baba.”
Soja ya ce:
“Ba matsala. Zan dawo da komai da ke hannuna, ba tare da wata gardama ba mai gari ayi hakuri.”
A zuciyarsa kuwa ya ce:
“Toh, ku ci gaba da shirmenku. Zan nuna muku! Nima nasan me nake” Ya tafi yana kukuni.
SOJA YAJE GURIN ABOKINSA GWAZA
Ya isa gurin abokinsa gwaza suka gaisa sai soja ya fara fada masa yadda sukai da me gari da kuma Malam Idi.
Soja yace:
"wai ni malam Idi zai kai kara gurin Mai gari." Gwaza yana sau raronsa gami da kallonsa sai yace:
"To akanme ya kai kararka? Kaddai ace daboda wannan gonakin ne?" Soja ya bashi amsa da cewa: "eh !akan hakane wai narike na hanshi kuma shine a hakku wajen tattara kadarori na Malam Nomau tunda shine dan uwansa."
Gwaza yace:
"Kai rabu dashi in shine dan uwansa to meye waye bai san cewa so yake ya danne musu gadoba." "Wallahi Mai gari ya dau zafi" inji Soja "to amma nine dai-dai da su na ishesu domin suma so suke su danne musu hakki.
Gwaza ya jinjina wa ya na kara zuga Soja.
Gwaza yazo gurin soja
Gwaza mazigi ga abokinsa Soja yazomasa da wata shawara akan Matar Malam Nomau wato Mama inda yakada baki yace:
"yau nazo maka da wata gagarumar shawara" soja yana sauraronsa, "ai kamata yaui ka auri matar Malam Nomau kawai kowa ma yahuta." Soja ya zaro ido ya jinjina lamarin sai yace:
"Kai Gwaza Baban Makani lallai kayi tinani mai kyau to kaga in,na aureta sai na mallake komai dika inyaso saj muga ta tsiya"
Gwaza yace:
"In ya san wata bai san wataba mu za'ai wa lalata muna 'yangari to on akai auren sai muga yanda zasuyi"
soja yace: ya balle da dariya
"Wai wannan Malam Idi har kai karata yake shi ga wanda yake takama da mai gari" Gwaza yana ta kyal kyala dariya, shima Soja yana dariya suka tafa.
Ladidi tazo gun Soja
Ita kuma Ladidi sai tazo gun soja domin neman tai mako don gida babu abinci, take shaisa masa sun kwana basuci abinciba.
Soja yayi mamakin jin wannan al amari sai yakada baki yace:
"To ina Malam Idi yake?"
Ladidi:
"yana nan ai danaje gidansa nafada masa halin da muke ciki korar kare yayimin" korar kare inji soja ya sa hannu a aljihunsa ya dakko wasu yan kudi ya bata ta karba tayi godiya ta tafi.
Soja yaci gaba da magan lallai lamarin na idi ya wuce kima ace mutane komai nasu yana hannunka amma ka hanasu, do dani yake zan cen zan kara daura damarar yaki dashi mara mutunci.
🌀 Cigaban Shiri...
Haka shirin Yar Malam ke ci gaba da ɗaukar salo mai cike da makirci, soyayya, zalunci da adalci. Ku ci gaba da kallon sa a tashar mu ta YouTube: NishadiSport.
Muna godewa duk masu kallon shirin da bibiyar tashar mu a:
- YouTube
- TikTok
- X (Twitter)
- Blog: http://nishadisport.blogspot.com
Na ku: Sadik Yusuf
📧 Sadiku854@gmail.com
📞 07082643256
Comments
Post a Comment