📰 Matsin Rayuwa da Karin Albashi: Ra’ayoyi Daban-daban daga Talakawa
Daga Sadik Yusuf — NishadiSport.blogspot.com
🔹 Mafi Karancin Albashi: Naira Dubu 62?
Har yanzu haka, ana ci gaba da cece-kuce a fadin Najeriya dangane da sabon mafi karancin albashi da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da shi a bikin Ranar Dimokradiyya da aka gudanar a ranar 12 ga Yuni a Eagle Square, birnin tarayya Abuja.
A wajen bikin, shugaban kasa ya bayyana cewa Naira dubu 62 (₦62,000) zai zama mafi karancin albashi, bisa la’akari da matsin tattalin arzikin kasar. Wannan sanarwar ta jawo martani daga bangarori daban-daban.
Talakawa musamman ma'aikatan Nigeria na cigaba da tofa albarkacin bakinsu don nuna takaici da abinda ke faruwa, a harkar kasa Nigeria, mu n zanta da wani ma'aikaci inda ya bukaci a sakaya sunansa yake cewa: "Gaskiya talakawa suna shan wahala a wannan lokaci na mulkin Bola Ahamad Tinubu muna fatan samun sauki daga garesu."
🔹 'Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi da Sabon Tsarin
Ƴan ƙwadago sun bayyana cewa wannan adadi bai yi musu ba, inda suke fafutukar ganin an ɗaga albashin zuwa ₦250,000 (naira dubu dari biyu da hamsin). Sai dai gwamnatin tarayya na ganin hakan ba zai yiwu ba a yanzu, saboda tsadar gudanar da gwamnati da rashin kudade. Da faduwar darajar mai a duniya baki daya.
🔹 Talakawa Sun Bayyana Matsayinsu
Wasu daga cikin talakawa da muka tattauna da su sun bayyana cewa kawai a rage farashin kaya, ba wai a ƙara albashi ba. Saboda matsalar da hakan kan haifar. Wasu na ganin cewa idan aka ƙara albashi, kaya ne zasu kara hauhawa su kara tashi, a shiga wanj mawiyacin halin kuma.
Amma gwamnati tana bigin kirji cewa jama'a su kara hakuri da halin da ake ciki ana daukar matakan da suka dace domin komai zai koma daidai, kamar yadda ake fada talakawa nacewa:
“An baka da dama, an karɓa da hagu”. Idan kashiga kasuwa sayen kaya xaka ga duk kudin sun kare.
Wani matashi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
“Gara a rage farashin kaya, ko ba a ƙara albashi ba. Abinci da magani su sauka, za mu samu sauƙi sosai.”
Shi kuma Malam Ibrahim, wani dan kasuwa daga Kano, ya ce:
“Idan dai litar man fetur da dala sun yi tsada, babu yadda za a yi kaya su sauka. Don haka dole ne a sauke farashin su Saukar farashinsu shine samun sauki inji shi.”
🔹 Ƙananan Ma’aikata na Cikin Wahala
Wani ƙaramar ma’aikaci ya bayyana cewa ₦62,000 ba zai ishe shi ba, ya ce:
“Kwano ɗaya na shinkafa dubu biyar ne. Mai dubu biyu da ɗari biyar, kudin makarantar yara, kiwon lafiya, kudin mota… sannan ga iyali suna jiran ciyarwa. To me mutum zai yi da dubu 62?”
Ya kammala da cewa:
“Allah ya kawo mana sauƙi kawai daga wannan masifa da ta tunkaromu fon tun hawan Buhari mulki muke fama kullum gwamnati na bugun kirji cewa zamu samu sauki.”
🛢️ Dangote ana masa zagon kasa kan Tace Mai a Najeriya
A wani bangare kuma, ana cigaba da zargi wasu manyan 'yan kasuwa da kokarin hana matatar mai ta Dangote ta fara aiki. Attajiri Aliko Dangote na fama da matsaloli da ake ganin ana hana shi samun danyen mai domin tacewa a cikin gida.
A cewarsa, akwai wasu da ke son a ci gaba da shigo da mai daga waje saboda suna samun riba ta biliyoyi a nan. Amma idan Dangote ya fara tace mai a Najeriya, ana sa ran farashin man fetur zai sauka zuwa ₦550 ko ƙasa da haka.
Wasu na ganin gwamnatin tarayya bata kyautawa idan har zata ci gaba da barin shigo da man da hana samar da mai a gida, domin:
“Idan Dangote ya fara, to farashin kaya zai sauka, abinci zai yi sauƙi. Talaka zai samu sassauci.”
🙏 Addu’ar Jama’a: Allah Ya Kawowa Talaka Sauƙi
Al’umma da dama sun bayyana cewa ci gaba da wahala a fannin abinci, sufuri, lafiya da ilimi ya sanya rayuwa ta zama mai wuyar gaske.
“Ci uku ya gagari mutane. Idan mutum yana da yara biyar kuma baya samun dubu goma a rana, to yana cikin matsala,” in ji wani da muka zanta da shi.
Tsokaci
To gaskiya yana da kyau masu hannu da shuni surika temakawa al'umma na kasa dasu da abinda zasu ci a wannan rayuwa da muka samu kanmu a ciki ta rashin samun abin kaiwa baka.
kuma mutane suna fama da rashi kudi abi yakai kanada san'ar yi amma saika wayi gari ka chinye jari saboda tsadar kaya, kai kuma baka samun abinda zai isheka to kaga taya jari zai kai labari?.
Ya kamata gwammnati tasan cewa mutane suna fama ita yadace tayi duk mai yiwuwa taga mutane sun samu sauki,don inganta lafiya da tsaro.
Sai fannin lafiya
Haka zalika wani lamari shi kuma na fannin lafiya shima yana da kyau gwamnati ta rika duba akai, a kullum domin bangaren yana da rauni ba ma'aikata ba magani ba tsafta, da dai sauran matsaloli wanda yakamata gwamnati ta rika kai ziyarar ba zata domin ganin yadda abubuwa suke gudana.
Wannan shawarace I zuwa ga hukumomin da abin ya shafa Allah yasa a gyara amin.
A ƙarshe, mutane da dama na roƙon Allah ya kawo sauƙi ga talaka, da kwanciyar hankali a Najeriya.
Good
ReplyDelete