Yar Malam ta koma

    Salamu alaikum masoya wannan Shiri naku mai farinjini wato Yar Malam Muna sanar daku cewa yanzu haka ananan ana cigaba da daukar Shirin inda ya chanza sabon salo wanda baku taba ganiba to zaku ganshi a cikin wannan Shiri namu in Allah yaso ,da Kuma sabbin fuskoki Wanda da babu su zakuga yadda ake cigaba da ganin lallai Sai an batar da hankalin marainiya Yar Malam Nomau amma Allah yana kareta tana tsallake duka Wani tuggu chikin Ikon Allah.


   Kuma zakuga yanda yaran Munzali gurgu sukaci amanarsa zasu yimasa duka Sai Sani yazo ya kwace shi mai makon gurgu yayimasa godiya Sai ma kara tsanarsa yayi shidai Sani yayine domin Allah baice masakomaiba.
  Shikuma kamaye awon igiya ashe akwai dukiyar Malam Nomau a hannunsa ba wanda yasani sai shi Sai ya yanke shawara yaje ya kaiwa magada abinsu Kuma da yaje Sai ya fahimci cewa za'a cinyemata Sai yaje gurin mai gari don ya kafa shaidu Amma mai gari yace yaje ya cigaba da rikewa har Sai annemeshi,Wanda hakan baiwa Malam Idi dadiba Har yasa yara subi shi su kwato a kan hanya shiko tsohon ma harbine yanuna musu Basu Isa komaiba,kaka yaje yacigaba da ajewa,haka Kuma su Dogo suka kulle Ladidi cikin daki wai ruwa kawai zasu rikabata har Sai tasa hannu a takardu Kuma ta amince da auren wani mai kusunbi itako taki.


    Karshe Inna ta budeta ta fita ta gudu basu saniba suna zaune wai su suna gadi saida daya daga cikin yaran Dogo  yaga Ladidi  tana sauri  sannan yaje yafadawa Dogo  yaganta, nan da nan  Dogo yaruga cikin gida don ya gani ko gaskiyane, shima yana isa yaga daki ba kowa  ya taho da gudu ya gayawa Maga takarda  ba Ladidi  ,suka umarci yaransu da garzaya su kamota.


  Suka wanna suka duba koina basu gantaba har suka hadu da Fatima amma tace musu bata gantaba, alhali karya take ta ganta.


  Suka dawo ba Ladidi  ba labarinta su Dogo da Magatakarda suka rikice suka rasa inda zasu sa kansu sai sukace akamomusu Kawa, wato Kawar Ladidi yaran suka garzaya suka zo da ita kuma tace bata gantaba.


   Chan ashe M Idi kuma yafadi kasa shima da yaduba bai ga Ladidi ba a garin gudu ya fadi kasa har yasamu karaya a Kafa shima yana ihu ba wanda yazo yaga halin da yakeciki yana ta murkususu shi kadai. 


 Itako Ladidi Fatima ta tafi da ita ta boyeta, gefe daya kuma ta yiwa su dogo waya domin suzo su tafi da ita,daman yar hannunsuce tayimusu waya suka zo suna dubawa basu ga Ladidi ba Allah ya bata sa'a ta gudu ba labarinta ta bazama cikin daji.


  Duk dahaka su Dogo basu daddaraba suka kara tura yara domin akamota ,tana gudu taga anbiyota sai ta labe a wata duhuwa sukai ta bulayi basu gantaba chan sai taga kamar za'a ganta sai ta futo , suka ganta suka bita tana gudu har suka kamota suka tsarata suna ta yimata dariya.


  Aiko tarihi ya maimaita kansa saiga Sani nan ya duro ya kwaceta yai musu duka suka gudu, shiko sani yatafi da Ladidi gidan su.


  Suka isa Malam ya karbeta hannu biyu yabata guri ta zauna aka bata kaya masu kyau tasa tayi fes da ita tasamu hutu da nutsuwa tayi kyau sosai suka ci gaba da hutawa abinsu,har Ladidi taga tana son Sani.


  Sani shiko baya ta tata itako tana ta kokarin ganin ya fahimceta amma ina abin yaci tura.


Su Dogo kuma sunata neman Ladidi basu gantaba, sai sukai tunanin lallai tana gun Sani, suka ko binciko garinsu suka dira garin suka nemo inda gidansu Sani yake , suka nemi su Sani subasu Ladidi,  Sani yaki akaje ga Malam. 

 
 Malam ya tambayi Ladidi ko ta sansu, tace eh! Dan uwanta ne , Dogo yayi farat yace kanwatace kuma Babanmu bashi da lafiya yace in nemota in koma da ita domin bashi da lafiya yana so ya nemeta da gafara komai ya wuce. 

  
  Malam ya juya gun Ladidi ya tambayeta ko zata koma gidansa shi M Idi, Ladidi tace bazata koma ba domin kasheta zasuyi. 
Mungode da ziyartar mu 07082643256
 Daga sadik yusuf  kano Nigeria. 
  nishadisport.blogspot.com 
 Sadiku854@gmail.com
 

Comments

Popular posts from this blog

YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review

Burinsa ya cika

Nigeria a yau