Rikicin daba a kano
GABATARWA
Rikicin ‘Yan Daba a Kano, a ga ya za'a kamo bakin zaran.Daga Sadik Yusuf, Kano Nigeria Zami duba da wannan matsala da kuma wasu al'amura na yau da kullum. Dafatan za'a kasance damu.
Daga Sadik Yusuf – Kano, Nigeria
Tuntuba: sadiku854@gmail.com
Shafinmu: nishadisport.blogspot.com
Abin Da Ke Faruwa a Kano
Ya kamata mu fuskanci abinda ke faruwa mu fadawa kanmu gaskiya, game da matsalar da ke addabar jihar Kano – wato rikicin 'yan daba.
Wannan matsala da take nema ta gagari Kundila ta shafi unguwanni da dama a jihar ta kano , kamar irinsu Dorayi, Sheka, Dala, Zage, Kofar Mata sharada, ja'in da kuma kurnar Asabe da dai sauran su.
A bin yazama kamar annoba.Yara da basu kai shekaru 15 zuwa 18 ba suna haduwa suyi gungu suna fada a da makamai a tsakaninsu, suna kai hare-hare a inda suke so.
Suna amfani da makamai masu hadari irin su adda, barandami, fafalo, da kuma kayan maye da suke shaye-shaye. Sau da dama.
Suna aikata laifuka masu tsanani, har da kisan kai. Basu jin tsoron Allah balle hukuma, har ma in 'yan sanda sunzo sai su rika jifan 'yan sanda da duwatsu suna futo na futo da hukuma.
Wasu lokutan har suna jikkata jami'an tsaro ko ma fararen hula, da basu san hawa da sauka ba. Wannan yanayi yana kara tsananta tsoro da fargaba a zukatan al'umma.
Musamman in kabiyo ta inda suke fada da juna lamarin yayi tsamari yaran basa jin bari, basa ganin girman manya da dattijan unguwa.
Kuma hukumar 'yansanda yakamata ta dauki mummunan mataki a kan yaran da suke aikata fadan daba a Kano.
Haka suma alkalai, su bada tasu gudun mawar wajen kawo karshen wannan lamari, ta hanyar hukunci mai tsanani ga wanda duk aka kama. Ya yabawa aya zakinta.
** Tasirin Iyaye da Gwamnati
Masana harkokin yau da kullum suna ganin cewa:
- Iyaye su daina kare yaransu idan suka aikata laifi.
- Hukuma kuma ta rika ɗaukar hukunci mai tsauri, ba tare da nuna son kai ba.
- Gwamnati ta sanya ido sosai wajen hana siyasa shiga cikin shari’a, domin ana zargin wasu ‘yan siyasa da hana hukunci kai tsaye ga bata-gari ta hanyar shisshigi daga alkalai.
- Da bada toshiyar hanci don a saki yaran saboda suna yimusu aiki lokacin zabe.
Har yanzu, akwai unguwanni da 'yan daba ke shiga har cikin gida suna karya ƙofofi don satar wayoyi da kaya. Wannan matsala ta zama abin ƙin ji a cikin al’umma. Dole ne kowa ya tashi tsaye wajen addu’a da aiki don samun zaman lafiya da tsaro me dorewa.
A sasu a makarnta don rashin karatu ba abin da baya sawa, shaye-shaye da sauran muna nan laifuka, rashin imani, da zalunci, karatu yana saita mutum, Allah ya sawaka.
** Hanyar yadda za'a gyara matsalar
Ana baiwa gwamnatin Kano shawara ta dauki matakai masu amfani kamar:
- Samar da ayyukan yi ga matasa.
- Ba da ilimi mai inganci da horo kan sana’o’in hannu.
- Tattaunawa da matasa a unguwanni daban-daban don sulhu.
A lokacin gwamnatin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, an yi amfani da manyan mazauna unguwanni wajen yin sulhu tsakanin kungiyoyin matasa.
Wanda basa jituwa da juna da kuma masu fadan daba. Wannan salon ya rage yawan rikice-rikice. Ya kawo zaman lafiya a unguwanni.
Muna fatan gwamnatin yanzu ta Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf za ta koma kan irin wannan tsarin, don samun mafita.
Dole ne gwamnati da al’umma su hada kai wajen tunkarar wannan matsala domin yaran sun shiga halin, da, ba sa jin magana ko tsoron hukuma.
Sai kaga irin wannan yara suna bi suna cire kayan da gwamnati tasa, don al'umma kamar irin su fitulin kan titi da dai sauran mahimman abubuwa.
** Matsalar ‘Yan Adaidaita Sahu
Wani bangare na wannan rikici shi ne ‘yan adai daita sahu. Wasu daga cikinsu suna hade da ‘yan daba. Suna daukar fasinja suna yi masu dabara don su sace masu wayoyi ko kaya.
Daga nan sai su ce sun manta hanyar, su sauke mutum, su gudu. Hakan tasha faruwa a titunan jihar kano.
Haka chan lokacin gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta sa dokar hana 'yan adaita sahu yin aiki daga goma na dare zuwa shida na safe.
An samu sauki kadan bayan da gwamnati ta takaita ayyukan adaidaita sahun daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe, amma har yanzu akwai bukatar kara sa ido sosai akansu, kuma gwamnati ta tantancesu asan suwaye sukejiharn Adaidaita Sahu a jihar.
Domin wasu suna kwararowa jihar ta Kano, domin yin aikin adaidaita sahun, basu da wajen kwana a cikin babur din suke kwana.
Kaga irin wa 'yan nan zasu zama barazana ga zaman lafiya. Koma ace sune suke aikata laifuka, da kuma wasu masu irin askin banza a kansu, da masu sa gajeren wando suna aiki, da lika hotunan banza, duk wannan yakamata a hanasu aikata hakan Allah ya a sawake amin.
Alhakin magance hakan ya ratayane kan gwamnati, ya kamata ta farka.
Matsalar yara masu gwan-gwan
👉 Kammalawa
● Matsalar 'yan daba a Kano na kara tsananta. Sai an hada karfi da karfe tsakanin gwamnati da al’umma kafin a iya magance wannan gagarumar matsala.
● Hadi da ta 'yan adaidaita sahu da kuma ta yara masu yawon gwan-gwan Muna rokon Allah ya kawo sauki.ya kawo dauki baki daya Amin.
Tuntuba:
- Daga Sadik Yusuf – Kano, Nigeria
- Email: sadiku854@gmail.com
- Shafin Blog: nishadisport.blogspot.com
- Waya 08148166212
Allah yakawo mafita
ReplyDelete