YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review
Shirin Yar Malam Kashi na daya, shirine da yake nuna rashin rike amana na wani mutum da dan uwansa ya mutu ya bar masa dukiya ,kamar irinsu gonaki dabbobi, da kuma kudi, da gidaje , kuma mutimin mai suna M Nomau, mutumin kirkine ya temaki dan uwan nasa amma yaci amanarsa ga kadan daga cikin episode one.
Ladidi na zaune a kusa da mahaifiyarta ta tashi don ta kaiwa babanta ruwa sai tasameshi a kwance ya kasa tashi, Sai nan danan ta durkusa gabansa tana Kuka ta Yar da kofin dake hannunta shiko yakama yimata nasiha cewa taji tsoron Allah.
Saiyace takiramasa Dan uwansa nan ta tashi ta ruga babarta tana mata magana amma tayi gaba ta garzaya ta kirashi yazo da sauri ya durkusa gabansa, nan M Nomau yabashi amanar iyalinsa da Kuma dukiyarsa nan take ya mutu suka kama kuka shiko Malam Idi yatashi ya futa da alamar murna a fuskarsa, sukuma sunata kuka.
Ya hana Zaman makoki ya samu abokin Malam Nomau wato Soja kan batun dawo da kadarori da suke a gunsa, Soja yayi mamakin wannan lamari yace to zai kawo ya tafi abinsa.Ashe shima gafiyane tsira dana bakinki gonaki dake gurinsa so take ya cinyesu shikenan suka shiga takun saka tsakanin Soja da M Idi kowa Yana ganin kowa macuci oh, Allah sarki Ladidi macuta sun kewayeta.tanata famadasu.Ga Kuma dansa Dogo wato da Ga M Idi Shima yabi sahun ubansa wajen muzgunawa Ladidi.haka ta rayu har saida uwar itama ta rasu kaka kara kaka ya ya Ladidi zata kasance a chikin wannan hali na kuncin rayuwa, haka wani lokaci taje neman taimako amma M Idi ya koreta yai mata fata fata har matarsa tana taremata amma yarufeta da fada, tayi shiru abinta ta zuba ido, dansa wato Dogo shi kuma ya biyewa ubansa aka cigaba da wulakanta Ladidi.
Dogo da Abokinsa.

Dogo da abokinsa wanda shi kuma yake zuga Dogo don su chimma burinsu shi da Babansa domin ganin an mallake wa Ladidi kudinta da gonaki, shanu, gidaje,da sauransu ko tsoro basa ji ga ukuba daga Allah, saboda Allah yai hani da haka akwai azaba da ya tanada ga mai cin hakkin marayu kuma tun daga Duniya zai fara fuskantar matsala.
Sudai su Dogo da abokinsa, haka da mahaifinsa ko ajikinsu,wai an yakushi kakkausa suka ci gaba da muzgunawa Ladidi duk fai don taji wahala ta sadudu.ko kuma ta mutu gabaya a huta bisa zugar Maga takarda abokin sa. Shikuma M Idi yayiwa mai gari alkawarin bashi gona daga cikin gonakin Ladidi a zuwan toshiyar baki don ya bashi hadin kai komai yatafi yanda suka tsara
Gefe daya kuma mai Gari yana da wani da shi kuma mahaukacine in yaga galala dai yabika da duka haka ake ta fama da shi acikin garin ,amma idan kace dashi in anbi Rabbana sai yace ba wahala nawa ,sai ya kyaleka katafi ba abinda zai maka,shikuma kaji nasa salon na mahaukata fuka dai cikin wannan kaya taccen shiri namu na Yar Malam.
Sai kubiyomu a tashar tamu wato nishadisport a manhajar youtube. In kun shiga shafin youtube kuka rubuta nishadisport,tasharmu zata bayyana sika kalli duk wanda kake so daga shirye shiryenmu na zamani , suna da kyau ga ilmantarwa, ga Nishadantarwa gami da ban dariya maganin hawan mini ga logon tashar
By Sadikyusuf
Http://nishadisport.blogspot.com. a tuntubemu ta wannan adireshi, sadiku854@gmail.com
Comments
Post a Comment