M IDI YAHADA KAI DA MEGARI DOMIN....

    M idi so yake ya cinyewa iyalan Nomau dukiya da kadarori baki daya Kuma ta hanyar tir sa sawa da zalinci karfi da yaji, Kuma yaje yahada kai da mai gari domin a cinyewa Ladidi hakki da uwarta ,me gari ya bada hadin kai yagoyi da bayan m idi, Amma yakafa masa sharadi za'a bashi kaso mai tsoka indai yasamu haka to lalle zai san yanda zaiyi a sa hannu a takardun filaye da gidaje na Nomau ko Kuma a cahanza takardun Baki daya shiko m idi ya amince da Jin hakan yayiwa mai gari alkawarin bashi kaso mai tsoka suka rabu.Duk da haka dai M Idi bai tsaya ananba Kuma yaje gurin Wani boka da zummar a kashe wa su Ladidi Baki its da mahaifiyarta Kar suce komai kan gadan nasu,boka yace bakomai aiki mara wahala Kawai yabada dubu dari biyar M Idi yace bakomai zai bayar.

 Wata rana Inna taje gidan su Ladidi sai taga Mama tana ta kwara amai a bakin rariya ta kamo hannunta suka zauna kan tabarma ,sai Inna ta fahimci cewa Mama tana da juna biyu nan dai tabata hakuri da abinda ke faruwa Mama tace bakomai Allah yana bayan mai gaskiya lomai kuma yana da karshe ta tashi ta tafi kafin tafiyarta ta ba Mama dan wani abu ta tafi ,shi kuma Malam Idi ya koma gida baiga Innaba yadinga kaiwa da komawa yana jiranta 
tazo ta ganshi yana jira ta karasa shi kuma ya zura mata ido ,yace daga ina take ,tace gidan makota taje ,yace karyane ba inda ban duba akace byakyanan saboda haka
ina kika je,Malam inju Inna abar kaza cikin gashinta kar 
Garin tone tone, ta tono abinda zai kasheta, ta tono din inji Malam Idi ayankata sai kin fada ,to kade kunnenka kasha labari gidan naje kuma kaji abida bazai maka dadiba matar Malam Nomau waro Mama tana da juna biyu
yauwa wannan shine abinda kake son ji ko to kaji sai muga yanda zakai, Malam Idi yayi mamaki ya jinjina ya  fita bashi da bakin magana .
    Hoton Inna da Mama 



   Oh!! kajifa Wani Batan basira idan m Idi yakwwntar da hankalinsa Shima Yana da gado a Wannan sabga Amma ya gwammace  yabi ta hanyar da bazata bullemasaba wato hanyar haram kowa Kuma yasan yanda hakkin maraya yake a gun Allah ta'ala du Wanda yacihakkin maraya Kamar yaci wutar jahannamane yakiyayi Ga muwarsa da allah, Ina masu ba mutane masu irin wannan Hali da si tuba sudena su ba marayu hakkinsu tun kafin gamuwarsuda Allah, ku ziyarcemu a YouTube channel namu mai Suna nishadisport Dan Kuga yanda wannan Shiri yake kasancewa mungode a sha kallo lafiya.
 Zan cigaba da sharhi kan yadda wannan shiri yake kasancewa a YouTube channel namu,Inna  matar M Idi ita kadaice take zaune da Ladidi lafiya ,kuma take riketa da gaskiya da amana take temakamata take bata abinci take kwantar mata da hankali a gidan Malam Idi, to ammafa Malam Idi bai saniba domin in yasani akwai matsala sai ya ci mutuncinta a boye take duk abin da take ,watarana
Dogo yazo shiga gida yaji Inna tana ma Ladidi magana bai
me suke cewaba sai yalabe yaga suna magana sai yakoma da baya yaje yagayawa Malam Idi, shi kuma yashigo yadunga bala'i kamar zai daki inna sukai shiru ita da Ladidi yagama yafuta ya barsu, kai marainiyar Allah  haka kawai ake mata wulakanci akan wata aba wai dukiya kuma dukiyarnan tatace.



      Sani matemaki Ga Ladidi yayi mafarki yaga anawa Ladidi wulakanci ta debo ruwa Amma su Dogo sun hada zuga suka tare hanya wai2 Sai ta shanye wannan ruwa itako tana ta basu hakuri Amma Suna daka mata tsawa Wai Sai ta shanye ruwa chikin jarka ita dai tana ta addu'a aiko Allah ya amsa mata addu'a sai Ga Sani ya zo ba zato ba tsammani yako kawo mata dauki ya koreshi yasamu ya rakata gida. Mun godewa masu bimmu sai ayimana sharhi.
     By Sadikyusuf.
 nishadisport.blogspot.com

Comments

  1. Muna maraba da masu ziyartarmu tashar tamu mai farinjini wato nishadisport

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review

Burinsa ya cika

Nigeria a yau