Rayuwar Ladidi ta kara tsananta!

๐Ÿง•๐Ÿพ Yar Malam - Kashi na 5 | Cigaba da Shirin NishadiSport

Assalamu Alaikum jama'a masu bibiyar shirin Yar Malam na tashar NishadiSport a YouTube. A yau ga yadda cigaban labarin ke tafiya cikin rudani da sirrika.

๐Ÿ›ก️ Saurayi Ya Ceto Ladidi

Allah ya kawo wa Ladidi taimako ta hannun wani saurayi wanda ya kubutar da ita daga hannun Dogo. A lokacin da Ladidi taje gidan malam Idi domin neman taimako basu da abinci,tayi sallama. 

Inna ta amsa:

"ladidi taho mai yafaru na ganki haka baki da alamar kuzari." Ladidi jikinta yana kyarma.

Ladidi:

"wallahi inna bamu da abinci a gida, komai namu ya kare shine nazo ki temaka ki sammana abincinci." Inna ta kamota tana rarrashi, sai ga Malam Idi ya futo yako dirammata ta inda yake shiga ba tanan yake futaba.

Malam Idi:

yace. "Wato kinzo ki zagenine ko kuwa mai yakawoki wannan gidan nawa banace kar ki kara zuwa nanba munafuka al'gunguma ki maza ki fice tun kafin na fara zabga miki bulala." Inna tace. "Ah! Malam ba hakabane."

ya katseta "baruwanki a wannan lamari inkika kara samana baki sai na ladabtar dake ehe domin banga abinda zaisa ki samana bakiba.

" Inna taja baki tayi shiru tana kallon sarautar Allah tana jimantawa Ladidi. Ya koreta ta fita.

Daman Dogo yana waje yana jiran ta ta futo fitarta ke da wuya sai ya taremata hanya, yanacemats: 

"ke ba anhanaki zuwa nan gidanba me kikazo yi banza mara zuciya walahi sai jikinki yayi tsami inna sake ganinki a nan." Itadai Ladidi batace masa komaiba kawai addu’a takeyi tana tafiya.

 Sai Dogo ya daga hannu zai mareta, kawai sai yaji andokeshi ya fadi kasa dam!,yana dubawa sai yaga wani saurayi tsaye a gabansa sai Dogo yataso da hargowa sai wannan saurayai ya daka masa tsawa. Nan Dogo ya dakata saurayi yace: 

"mai ya hadaka da'ita."

Dogo:

"Kanwatace ina ruwanka."

Sani:

"To in kanwarkace sai kaci zalinta haka akeyi, to ware kabar nan mugun banza." Sai Dogo ya tafi. 

Ita kuma Ladidi tayi murna ta godewa Allah, nan taba Sani labarinta ya tausaya ya bata wasu yan kudi ta tafi.


Saurayin ya fadawa mahaifinsa (Malam) irin taimakon da ya yi wa Ladidi, Malam kuwa yayi matukar farin ciki, ya kuma bukaci ya ci gaba da taimaka mata har a ga inda al'amari zai tsaya.

Sani kuwa, ya godewa Malam bisa irin hadin kai da ya bashi, ya cigaba  da addu’a.

 Mahaifiyar Sani itama tayi addu’a Allah ya kare Ladidi daga duk wani sharri na wa 'yannan 'yan uwa nata, Allah ya kyauta da mugaye.

๐Ÿฒ Wahalar Da Ladidi Da Mahaifiyarta Ke Fuskanta

Su Ladidi da mahaifiyarta sun shiga mawuyacin hali. Har abinci sai sunyi roko kafin su samu abinda zasu ci. Rayuwarsu ta koma cikin duhu da tsanani. Saboda zalinci na su Dogo.


♿ Munzali: Gurgu Mai Soyayya

A gefe guda kuma akwai Munzali (gurgu), wanda yake matukar son Ladidi, amma ita ko kallonsa bata yi. Duk kokarin da yake yi na yaga ya  taimaka mata amma ita tana ki. 


Yana ci gaba da fama da ita yan nuna mata soyayyarta amma  kuma taki amincewarta.


 Wata rana ya taho gidansu Ladidi kamar yadda ya saba sai ga Ladidi ta fito tana sauri an aiketa debo ruwa sai gurgu yake mata magana.


Gurgu:

"Ladidi tsayamana gunkifa nazo yin dazu ke nake jira" ta zabga masa harara tayi gaba abinta shiko sai binta yake amma taki ta kulashi, ta tafi abinta haka fai ya tsaya yana kwafa.


     Sani da Ladidi suna tsaye                 Sani  da Ladidi 


๐Ÿ” Sani Na Neman Ladidi

Sani ya fito neman gidansu Ladidi, amma ko ina ya tambaya sai a ce ba a san inda suke ba. Har ya hadu da wata mata da kamar zata fadamasa, daga karshe tace bata sani. Dole ya hakura ya koma gida.

Wannan irin rayuwa me yasa mutane ke boye gaskiya? Shin tsoro ne ko halin rashin tausayi? Allah yana son masu taimako, don haka mu gyara halayenmu, domin rayuwa tana da sakamako.

๐Ÿ’” Soyayya Ko Taimako?

Cigaba da shirin ya nuna yadda Sani ke kokarin taimaka wa Ladidi. Amma kanwarsa ta ce shi dai so yake, ba taimako ba. Sani ya shaida mata cewa shi dai yana aikata abinda Malam ya umurta. Amma kanwar ta dage: "Wallahi sonta kake, ba wani taimako ba."

Sani ya harareta, yace:

“Sai kiyi, tunda kin kasa fahimta!”

๐Ÿ˜ด Mafarki Mai Firgita

Sani yayi mafarki yana ganin Dogo da Magatakarda da yaransu sun tare Ladidi suka ce sai ta shanye ruwan da ta debo. Ruwan kuma  gidansu dogon zata kai. Kawai sai Sani ya farka daga wannan barci nasa. Sai ya danar da Malam Babansa abinda ya gani a cikin baccinsa , Malam yayi mamakin wannan mafarki. Sai yace da Sani.

Malam:

"To yanzu abinda za'ai kai maza kaje kaga halin da take ciki domin wannan  mafarkin, yana nuna cewa akwai matsala." 

Sani ya tashi ya tafi aiko qbin mamaki. Sai yaga abin da yagani a mafarki ya tabbata ya duro yayi musu duka, ya korasu, sannan ya rakata gida. 

A hanyane take bashi labarin cewa mahaifiyar ta ta rasu


Sani:

"kai na tausaya miki bisa rasuwar mahaifiyarki to yanzu ya kenan."

Ladidi:

Tayi gwauran numfashi, tace: "ai ingayama yanzu na koma gidan kawu da zama, wato gidan su dogo Sani ya girgiza kai ya jijina lamari, yace: "to Allah ya kyauta ya kawo maki mafita daga sharrin muta nan-nan, tunda yanzuma ni na kwaceki daga hannunsu." Ladidi tace: "amin na gode da taimakon da ka yimin bacon zuwankaba da ban san yadda zasuyiminba."

"Ai bakomai" inji Sani ya rakata suna tafiya sai ga MalamIdi yako diramma Ladidi da masifa ya koreta har yakusa dukanta da sanda ta goce, ya dawo kan Sani ya yimasa fata-fata. Ya koreshi. Nan Sani yarasa damar ganin gidansu Ladidi ya tafi abinsa.

Shi kuma Malam Idi yabi Ladidi gida, wayyo yako zaiwa Ladidi? Abin sai wanda yagani.


๐Ÿ•ต๐Ÿพ‍♂️Cigaba da Binciken gidan su Ladidi    

Mahsukaci dx sanda
 Hoton Mahaukaci 

Sani ya ci gaba da neman Ladidi amma har ya kai
unguwarsu ba wanda ya gaya masa inda take. A haka har ya hadu da wani mahaukaci da yake kokarin tambaya, sai kawai ya taso masa.yana neman duka aiko   Sani ya buga shi da kasa! Tun daga wannan rana, mahaukacin ke tsoransa — duk inda suka hadu da ya kyalla yaga Sani, sai ya ruga da gudu.

Kuma a haka wannan mahaukaci tsoransa ake a garin.

๐Ÿ“บ Shirin Ya Ci Gaba

Haka shirin ke kara daukar sabon  salo da tashin hankali. Ku ci gaba da bibiyar Yar Malam a tashar NishadiSport a YouTube. Muna godiya ga dukkan masoya da suke bibiya a Facebook, TikTok, X, da blogs.


✍️ Mawallafi: Sadikyusuf

๐Ÿ“ž Tuntuษ“a: 07082643256
๐ŸŒ https://nishadisport.blogspot.com



    

Comments