LADIDI TA SHIGA TASKU

    Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu na nishadisport. 

Mahaifiyar Ladidi ta kamu da rashin lafiya.

Tofa ana cikin tufka da warwara, Mama mahaifiyar Ladidi kuma takama rashin lafiya, gaba kura baya Siyaki, ga shi basu da kudi ko ruwan sha Babu agidan nasu, haka Ladidi ta fita neman tai mako tahadu da Dan gurgu.

 Gurgu yanasan Ladidi: 

Yana mata magana amma ta manta dashi taki kulashi ya dauki kudi ya bata amma taki karba wai ita bata sonsa, haka ta tafi tabarshi da zaton wani ne yake huremata kunne, "yayi kwafa."

Kaji batan basira irin na rashin so. To hakane man kin futo kjna neman taimako kuma kin samu amma don bakya son mutum sai ki ki karba, to ki karba mana ki saiwa Maman ki magani, hum Allah ya rabamu da son wanda baya sonmu.

Gurgu yace:

  "zasu gamu."

 Wani lamari sai rashin kauna ace mutum Yana cikin matsala abashi kudi yaki karba to allh ya sawake.

 Sani yana neman gidansu Ladidi: 

      Shiko Sani har yanzu Yana Fadi tashin ganin gidan su Ladidi bisa umarnin mahaifinsa wato (Malam), da kuma te makon mahaifiyarsa duk Wanda ya tambaya sai ace dashi ba'asaniba. Sai ya gaji ya koma gida.

  Sukuma su Dogo suna ta faman ya zasuyi suzubar da cikin da maman Ladidi take dashi. To mma abin yaci tura saboda su, su Ladidi  sun dogara ga Allah, kuma Allah Yana tai makonsu har dai Dogo yagaji.

 Rannan da kansa Dogo yaje gidan su Ladidi. Dan ya ba Mama  ta sha maganin da yakaimata na zubar da ciki, amma da taimakon Ladidi magani  ya zube.

Ita Ladidi,  da taga Mama zata sha wannan magani sai ta kwallah kara Mama ta firgita, magani ya zube, haka Ladidi tayi murna kuma Mama ta yadda da abin da Ladidi take fadamata na kar ta yadda da su Dogo.

Shikuma haka yafita daga gidan, da borin kunya ya bar gidan Maga Takarda na masa magana amma yai gaba yaki saurarensa. Magadanka yabishi yana kokarin tsaidashi yaki suka rankaya.
  Ladidi da Mama da Dogo 

Dogo bai kakura:

  Amma duk da haka Dogo bai hakuraba. Maga takarda yacigaba da ziga Dogo sunata kitsa yadda zasu zubar da cikin mama mahaifiyar Ladidi amma Allah Yana karesu Suna tsallakewa domin sun dogara Ga Allah tabaraka wata ala.

Domin duk Wanda ya dogara Ga Allah, Allah ya isar masa. Akokarin Dogo  na ganin ya zubar da cikin Mama, ma haifiyar Ladidi,  ya je ya samo wani magani ya kaiwa inna ma haifiyarsa don taje ta kaiwa Mama ko tafi yadda da ita saboda su bazata amince da suba,  a sakamakon shawarar Magatakarda. 

Yaje kamar mutimin kirki ya ba inna maganin itako taki karba ta zubar ta koreshi ya tashi ba nauyi yaje yagayawa Magatakarda, kamar yadda ya saba yadorashi kan cewa yanzu yaje da kansa yayi yan dabaru yabata ta tasha a gabansa yako amince yatafi .

Dogo:

  Yayi sallama, "salamu alaikum"

Mama:

 Ta amsa "wa alaikumussalam" tayi mamakin ganinsa a wannan lokaci. Saboda tun rasuwar mijinta baizo gidanba, sai yanzu ashe yazo zalincine.

Dogo:

"Daman nazo ne inkawo muku taimako naji ance baki da lafiya." Ta kalleshi kallo na mamaki. Tace "yaushe rabonka da gidan nan tun rasuwar Malam."

Dogo:

"Ai Umma abubuwane sukayi yawa shi'isa ba'aganinmu to amma yanzu zaki rika ganina akai-akai, shi'isa yanzu ma nazo miki da wani taimako domin ki samu lafiya."

Mama:

Ta kalleshi, "to bakomai ina matukat godiya da wannan taimako naka Allah ya bar zumunci yakar arziki mai amfani ya rabak da iyayenka lafiya amin." Tasa hannu ta karbi maganin, shi kuma ya tashi ya tafi.

Sai ga Ladidi ta shigo gidan ta hadu fashi a soro, sai ta kama rabewa a jikin bango. Shi kuma sai yace da ita.

Dogo:

"A kanwata ladidi ki saki jikinki ni yanzu nazama naku bani da wata matsala da ku wallahi ba komai" yana ta murmushi. Itadai sai kallonsa take tayi tana sulalewa ta shiga gida.

Ta iske Mamanta zaune da magani a hannunta, Ladidi ta sawa Mama ido tace.

Ladidi:

"Yanzu Mama keh! Kin yar da dashi kinsan fa irin kyamatar mu da sukeyi, amma yanzu ace wai shine zai dakko magani ya kawo miki wai yana jin tausayinki haba Mama wannan lamarifa abin dubawane" ita dai Mama tana kallon Ladidi tace :

"Ni ina ganin Dogo ya zubar da makamansa kinga fa har naira (1000) ya dauka yabamu mu sai ruwa ni ina ganin ba wata matsala kinsan mutum yana iya chanzawa ya zubar da makamansa." 

Ladidi tace:

"To shikinan Allah yasa ya gane gaskiya domin Dogo hadarine ni injin tsoronsa." Mama tace: "amin."

Dogo yanba Magatakarda labarin yanda sukayi da Mama:

Magatakarda:

"Yaya bani na sha nakagu naji yanda kuka yi da Mama kasan taurine kaine da'ita." Dogo yayi dariya ya numfasa.

Dogo:

"Ai intasan wata bata san wataba nagama da ita ta amince dani na nuna mata bawata matsala yanzu a tsakaninmu kuma nace duk abin da suke nema su gayamin zan basu."

"Lallai ka iya tuggu" inji Magatakarda: "ai a haka zamu samu ta amince ta dakai tasha wannan magani, kaga dazarar tasha shikenan angama sai dai wani cikin ba wananba." Dogo ya girgiza kai alamr ya gamsu.

Dogo:

"Ai da cikin ya zube shikenan mu munsamu yadda mukeso kaga dan abin da za'a basu bashi da yawa tuda bamu san abinda zata haifaba." 

Magatakarda: "to kagani in ta haifi na miji ya cinye komai ko kar fanfana bazaku samuba shi isa nakeso ayi kaimi wajen ganin cikin ya bare." Doho ya zaro ido alamar kaduwa.

 Kaji rigima irinta dan Adam mutane da hakkinsu ace lallai sai ancinye bagaira ba dalili anata kashe kudi ana kokarin ganin lallai sai an zubar da ciki don kar abasu gadonsu.

Sai a bimu a wani sharhi na gaba muna godiya da bin wannan shafi namu na (nishadisport), a youtube da kuma blogs, sai ayimana (subscribe) a yimana like da sharhi akan abinda muke wallafawa.

 
  Wanda ya wallafa, Sadikyusuf

Tuntuba ta imel. sadiku854@gmail.com 

      Nishadisport.blogspot.com 
Na! Gode.

Comments