SADIK YUSUF
Gabatarwa daga Sadik Yusuf Garba Ni sunana Sadik Yusuf Garba, an haife ni a unguwar Jakara, Tudun Makera, dake cikin birnin Kano, a karamar hukumar Dala, a shekara ta 1974. Na fara karatuna da karatun Alkur’ani mai girma, sannan na ci gaba da karatun Islamiyya. Haka kuma na yi karatun boko daga matakin firamare har zuwa sakandire. Na yi aure ina da shekara 25 a lokacin, yanzu kuma ina zaune a gidana tare da iyalina. Ina da ’ya’ya hudu — uku maza da mace daya. Harkokina na Yanzu Ina zaune a unguwar Goron Dutse kusa da hanyar gidan gyaran hali (prison) dake kusa da hanyar Kansakali. A nan ne nake gudanar da harkokin kasuwanci, musamman: Sayar da bakin mai Sayen duro da yamti Sayar da man mota da sauran mayuka daga kamfanonin cikin gida da na kasashen waje Harkokin Lafiya da Wasanni Na dade ina cikin harkar motsa jiki, musamman wasan kareti, inda na kai matakin bakar damara (black belt). Har ila yau muna gudanar da horaswa da tsalle-tsalle a Goron Dutse Sport Center, dake hanyar Jakara. H...