Yan wasan da suka wakilci jihar Kano a wani wasan da aka fafata a jihar Enugu, yayin dawowarsu gida sun gamu da hadarin mota. Wannan mummunan hadari ya yi sanadin mutuwar mutane 22, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata. Ciki harda masu horaswa,da 'yan wasa, drebobi, da sauransu.
Jama’a da dama da suka jikkata suna karbar magani a asibiti inda ake basu kulawa ta musamman. Wadanda suka rasa rayukansu kuma an yi jana'izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini tare da jajantawa iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano. Haka zalika, ya sha alwashin daukar nauyin kula da lafiyar wadanda suka jikkata tare da fatan Allah ya kare afkuwar irin haka a gaba.
Amma gwamnatin Kano yayi abin yabawa domin ta kai daukin gaggawa inda abin ya faru. Nan akafara bawa wanda suka jikkata kulawar gaggawa bisa jagorancin kwamishinan wasanni na jihar kano Mustafa Rabi'u Musa.
Mustafa Rabi'u Musa kwamishinan wasanni na kano.
fadar shugaban kasa ta aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Kano da daukacin al’ummar Najeriya. Muna rokon Allah Madaukaki ya gafarta wa wadanda suka rasu, ya kuma ba jikkatattu lafiya, ya hana faruwar makamancin hakan nan gaba.
SHARHI
Yanada kyau gwamnati ta kula da abubuwan da suke haddasa hadura a kan titunan Nigeria musamman manyan hanyoyi saboda kullum ance anyi hadari a chan ache anyi hadari a nan kuma asamu rasa rai da kuma muna nan raunuka harda rasa dukiya baki daya.
Wannan lamari ya rataya kan hukuma itace ke da alhakin lura da hanya da kuma lodin da masu mota keyi. Na ganganci.
Sukuma masu motoci, drebobi manya dana kanan motoci, suma su kula da hakkin hanya su daina gudun wuce sa'a su dena login da ya wuce kima domin kowace mota akwai adadin abin da zata dauka, doramusu kaya dayawa yana sabbaba hadari. Sai kaga har a but din mota wajen zuba kaya amma mutane ake turawa,har wajen zaman dreba mutane ake zubawa don Allah mu gyara ko asamu sauki.
GAME DA CIN ZARAFIN DABBOBI – MU KULA DA HAKKINSU
A halin yanzu ana ta hada-hadar jigilar dabbobi daga gari zuwa gari, amma abin takaici shi ne yadda wasu ke nuna rashin tausayi da imani wajen mu'amala da dabbobin. Wasu mutane kan daure dabbobi a kafafunsu, su zauna a kansu a kan babur ko mota, suna tuka su ba tare da jin tausayinsu ba.
Wasu kuma su sasu amota a daure suyi tafiya mai nisa dasu kasa-kasa gari ya gari ba maganar cin abinci bare kuma ruwa haka zasu isa a galabaice, wasu kuma su rasa ransu a hanya.
Idan ankaisu inda ake bukata sai kaga wasu basa iya tafiya sai sun huta, wasu ma sai sunkwana sun wuni kana zasu iya tashi, wasu kuma sai dai a yanka anan. Don haka jama'a sai mu gyara domin itama dabba tana da nata hakki akanmu.
Tambayar anan ita ce: Ina hukuma mai kare hakkin dabbobi take? Idan kuwa akwai, lokaci ya yi da za ta tashi tsaye wajen ganin an sauke nauyin da ya rataya a kanta.
Akwai bukatar gwamnati ta kafa dokar da ke kare hakkin dabbobi, ko ta farfado da ita idan tana nan. Dabbobi, koda ba mutane ba ne, suna da hakkin kulawa da tausayi kamar yadda addinin Musulunci da sauran kasashen duniya ke koyarwa.
A wasu kasashen waje, cin zarafin dabba yana iya kai mutum gidan yari. Amma a nan gida Nigeria, za ka ga yara ko manya na dukar dabba da igiya, har dabbar ta jikkata ko ta mutu.Ba mai cewa kamai wannan zalunci ne kuma Allah ba ya son zalunci.
Musulunci ya koyar da cewa in za ka yanka dabba, sai ka wasa wukarka sosai domin kar dabbar ta sha wahala. Ka kuma juya dabbar da fuskarta kasa, kada a nuna mata cewa za a yanka ta. Wannan koyarwa tana nuna muhimmancin jin kai ga halittu.viki harda tsintsaye.
Don haka ina kira da kakkausar murya ga jama'a da su kiyaye hakkin dabbobi. Mu dinga nuna tausayi da jin kai, domin rayuwa da albarka tana biyo bayan aikata adalci. Allah yana son masu adalci, kuma duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.
MU SAUKAKAWA KANMU
Wato na lura da cewa ansamu saukin abubuwa na kayayyaki sun sauka, musamman ma kayan abinci,irinsu Wake,Dawa,Sahinkafa, Masara,Waken suya,da sauransu wannan abubuwa da na lissafa duk sunyi sauki a kasuwa.
Amma abin takaici, sai kaga masu saida abincin sayarwa basu kara hannuba sunci gaba da sayarwa yanda suka saba. Don haka yakamata mutane muma muzama masu jinkai in abu yasauko mu aauke in ya tashi mukara, wannan shine adalci,don kowa yasan cewa muma muna son juna.
Amma in shugabanni sukayi ba dai-dai ba sai muyi cha akansu zagi da suka,kuma muma bama wa kanmu adalci don Allah mu gyara,gyara kayanka bai zama sauke muraba. Inkai sauki nima nayi sauki wanchanma yaui sauki sai kaga kowa yasamu.🙏
KARSHEN NASIHA
Kowa ya kyautata — domin kowa zai ga alherin da ya aikata. Kowa yayi da kyau zaiga da kyau, Wannan shi ne sakona na yau. Kada ku manta ku dinga binmu a dandalinmu na NishadiSport, ku yi Subscribe, ku rika Sharing da Commenting. Muna godiya da kasancewa tare da mu.
Naku cikin girmamawa,
Sadik Yusuf
📧 Sadiku854@gmail.com
Yayi mungode da wanan sharhi
ReplyDeleteGood
ReplyDelete