Kano – 28/06/2025
Gwamnatin Saudiyya ta amince da a binne marigayi Dr. Aminu Alhasan Dan Tata a gobe Litinin, a birnin Madina, kamar yadda yake cikin burinsa tun kafin rasuwarsa.
Sakataren marigayin, Alhaji Mustafa, ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Facebook, inda ya ce za a dauko gawarsa daga Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) zuwa Saudiyya domin gudanar da jana’iza.
A cewarsa, “Shi dai Dr. Aminu Alhasan Dan Tata ya bayyana cewa bai da buri face a binne shi a Madina. Iyalansa sun yi duk mai yiwuwa don ganin hakan ta tabbata – kuma Allah ya nufa.”
Wannan shine burin Aminu Dan Tata in yarasu a kaishi madina birnin Manzo don a binne shi.
A nan Kano kuwa, an gudanar da sallar jana’izar ga’ib a masallacin Aliyu Bin Abi Talib, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Khalil, inda manyan baki da al’ummar gari suka halarta domin yin sallah da addu’a ga marigayin. Allah ya jikansa da rahama, amin.
"Kullu nafsin za’iqatul mawt" – Hakika kowane rai zai dandana mutuwa.
Amma mutuwar ta girgiza jama’a ciki da wajen Kano, haka iyalansa sunui matukar kaduwa da jin labarin mutuwar.
Gyaran Tituna a Kano: Gwamnati na Ci Gaba da Aiki
A wani labari kuma, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da gudanar da gyaran tituna kimanin goma sha takwas (18) a cikin birni da kewaye.
Wasu daga cikin aiyukan sun yi nisa, wasu kuma an fara. Sai dai jama’a daga wasu yankuna na korafi kan cewa wasu tituna an yi watsi da su, inda suka nuna fargaba ganin yadda damina ke karatowa, kuma akwai hadarin ambaliya a yankunan da ba a kammala gyaran ba.
Mazauna Zungeru na Cikin Fargaba
Mazauna titin Zungeru sun koka da cewa saukar ruwa na lalata musu kaya, musamman idan aka samu ruwan sama mai karfi. A cewar wani mazaunin yankin:
“Ko ruwa kadan aka yi, yana lalata mana kaya. Babu hanyar ruwa. Ko me muka ajiye ruwan, sai ya bata mana da kaya muna tafka asara sosai.” injishi
Sun roki gwamnati da ta gaggauta kammala aiyukan domin ceton rayuka da dukiyoyin al'umma.
Gwamnati Tana Kokari, Amma Tana Bukatar Hadin Kan Jama’a
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun yabawa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan yadda take gudanar da gyare-gyare, musamman wajen yashe magudanan ruwa da aikin shatale talen titin gidan Baban Gwari, da kuma titin Yahaya Gusau wanda ake ci gaba da aikin.
Sai dai sun bukaci gwamnati ta kara kaimi da saurin kammala aikin kafin ambaliya ta kawo cikas.
Gwamnati Ta Gargadi Jama'a Kan Zubar da Shara a Magudanan Ruwa
A bangarenta, gwamnati ta bukaci jama’a da su guji zubar da shara barkatai, musamman a magudanan ruwa, wanda hakan ke haifar da toshewar hanyoyin ruwa da ke janyo ambaliya da asarar dukiya har da rayuka.
Gwamnati ta bukaci jama’a su:
- Rika shara da kyau.
- Sanar da hukuma idan sun gudanar da aikin gayya, don gwamnati ta tura motoci su kwashe shara.
- Su rika sa ido ga gwamnati wajen bayar da rahoton inda ake bukatar gyara.
Wani mai sharhi, Sadik, ya bayyana cewa:
"Muna godewa gwamnati bisa kokarinta, amma muna fatan za ta cika alkawurran da ta dauka ga jama’a."
Shawara ga gwamnati
Wasu mazauna birnin Kano suna kokawa kan yawaitar lalacewar tituna a jahar,wanda kusan duk shekara sai tituna sun lalace saboda kila ba'ayinsu da inganci shi isa suke saurin lalacewa, da zarar damuna tayi nisa ga ba hanya ta ruwa ga shara ko'ina.
wani mazaunin Kano da ya bukaci a sakaye sunansa yake ba gwamnati kano shawara kan.
"ta samo wata aabuwar fasaha ta gina hanyoyi wadda bada kwaltaba ko asamu zaman hanyoyin lafiya su rika dadewa ana anfani dasu."
"Idan akasamu hanya mai inganci wadda zata dade to kaga sai aiuukan gwamnati suyi wani bangaren wanda ba titiba domin shi an gama da shi, sai kaga kudi suna zuwa har asibiti da wasu fannoni daban-daban."
Jirgin kasa a Nigeria
Hukumar kula da jigilar mutane ta jirgin kasa a Nigeria ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa da kaduna zuwa Abuja har zuwa wani lakaxi a nan gaba.
Kayode opaifa shugaban hukumar ta Nrc ne ya bayyana hakan ga manema labarai dalilin da yasa jirgin yaui hadari.
Opaifa yace: "wasu ma'aikatan hukumar da hukumar, da hukumar kula da sufuri da sauran wanda abin ya shafa suna nan suna gudanar da binceke kan faruwar lamarin a inda akasamu hadarin."
Yaui watsi da magan ganun mutane inda wasu suke cewa jiragen na laying dogon basu da inganci Inda yace: "a halin yanzu anfara ma yarwa da fasinjoji kudinsu"
Hukumar tana kira ga jama'a su kwantar da hankalin su komai zai koma kamar da kima asamu ingan tuwar al'amura a harkar ta Jirgin kasa a Nigeria.
Jirgin kasa
Talakawa suna nasu tsokacin
Wasu yan Nigeria suna tofa albarkavin bakinsu kan faruwar hadarin jirgin kasa wanda ada ba'asaba ganin hakaba suna ganin a kwai lauje cikin nadi da yakamata gwamnati tayi binviken kwa-kwaf kan al amarin jirgin kasa a Nigeria don su samu amincewa dasu.
Hukuma ta abayyanawa mutane musabbabin abin fon su samu karfin hawa jirgin.
Jami'a A S U U
wata sabuwa Malam jami'a a Nigeria suna yin zanga-zangar nuna fushin su na rashin cika alkawarin da gwamnati tayi musu tun a shekarar Dubu biyu da sha tara da akayimusu al'kawari har yanzu angaza cikashi.
Zanga-zangar lumanar ta malaman ta haifar da tsaiko a harkokin koyon karatu na daliban.
Malamai kar kashin kungiyar ta asuu sun koka inda suke cewa suna wahala wajen harkar koyar da karatu.
Kuma suna aiki cikin yunwa da rashin kayan gwaje-gwaje da rashin abin more rayuwa injj su
Shugaban na asuu farpesa criistoper yace "in gwamnati bata dauki matakiba za'a iya shiga yajin aiki na sai bab tagani ma'ana na din-din din."
Ansha fama da yajin aikin jami'oi a Nigeria a gwamnatoci daban-daban, amma har yanzu bata chanza zaniba inda a Wannan gwamnatin ma ake kokarin shiga yajin aikin.
Kungiyar na bukatar karin kudade na gudanar da aikin koyo da koyarwa da bayar da izinin yin binceke cikin sauki.
Ana fata gwamnati ta duba wannan lamari don kada a durkusaar da harkar karatu a kasar. Allah ya kyauta amin,ya kawo karshen dambarwar jami'oi a Nigeria.
Tuntube Mu:
Mawallafi: Sadik Yusuf
📧 Imel: sadiku854@gmail.com
📱 WhatsApp: 08148166212
🌐 Shafin Blog: nishadisport.blogspot.com
Comments
Post a Comment