Posts

Showing posts with the label labarai

DUKAN DUHU- KASHI NA 3

  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna ( nishadisport). Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!. Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3  SALE DAURE A WANI KANGO  Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit. Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba. Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace: Alhaji:  "Malam Salele mai liki,  yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soya...

Rikicin daba a kano

     GABATARWA Rikicin ‘Yan Daba a Kano, a ga ya za'a kamo bakin zaran.Daga Sadik Yusuf, Kano Nigeria Zami duba da wannan matsala da kuma wasu al'amura na yau da kullum. Dafatan za'a kasance damu. Daga Sadik Yusuf – Kano, Nigeria Tuntuba: sadiku854@gmail.com Shafinmu: nishadisport.blogspot.com Abin Da Ke Faruwa a Kano Ya kamata mu fuskanci abinda ke faruwa mu fadawa kanmu gaskiya, game da matsalar da ke addabar jihar Kano – wato rikicin 'yan daba.  Wannan matsala da take nema ta gagari Kundila  ta shafi unguwanni da dama a jihar ta kano , kamar irinsu  Dorayi, Sheka, Dala, Zage, Kofar Mata  s harada, ja'in da kuma kurnar Asabe  da dai sauran su. A bin yazama kamar annoba.Yara da basu kai shekaru 15 zuwa 18 ba suna haduwa suyi gungu suna fada a da makamai a  tsakaninsu,  suna kai hare-hare a inda suke so.  Suna amfani da makamai masu hadari irin su adda, barandami, fafalo , da kuma kayan maye da suke shaye-shaye. Sau da dama. ...

Gwamna ya samu hadarin Mota ya tsallake rijiya da baya

Image
     GABATARWA   Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku sharhin abinda ke faruwa a sassan Nigeria nine naku Sadik Yusuf.   Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya gamu da hadari. A ranar Lahadine wani lamari da ba'a saba ganiba a Nigeria ya afku wato ace Gwamna mai ci yayi hadari. Wato Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda, yayi hadarin mota a hanyarsa da yataho daga Daura zuwa katsina.inda wani dreban Golf yayi aron hannu. Shi ya haddasa hadarin.  Hakan na faruwa, nan da nan aka garzaya dasu asibiti dake Daura. Aka duba lafiyar su, su uku ne acikin Motar. Inda daga bisani kuma aka garzaya dasu asibitin tarayya na jihar Katsina.                   Umar Dikko Radda  Daraktan yada labarai na Gwamnan Katsina Maiwada Dan Malam yatabbatarwa manaima labarai lamari, inda yake cewa. "bayan abin yafaru. Aka kaisu wani asibiti dake Daura,aka basu taimakon gaggawa, inda daga bis...

Antashi da rasuwa a Nigeria

Image
             GABATARWA  Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku labarai da sharhi kan al amuran yau da kullum. A wannan shafi namu na blogs nishadisport.blogspot.com.  Nine naku "Sadik Yusuf" nake gabatar muku da labaran.  * Rasuwar Muhammadu Buhari.   A yaune Lahadi tsohon shugaban kasar NIgeria. Muhammadu Buhari. Ya rasu a kasar ingila inda yake jinya  Kar kashin likitoci,mai magana da yawun tsohon shugaban kasa. Garba Shehu ya fitar da wata sanarwa,in da yace:  "ya rasu ne da misalin karfe 4:30 sakamakon doguwar jinya."  A cewar fadar shugaban kasa, Bola Ahamad Tinubu ya umarci matemakinsa, Kashim Shattima da yaje birnin na London ya rako gawar ta Muhammadu Buhari zuwa gida Nigeria.  A makon jiyane shugaban yaje birnin London domin duba lafiyar sa kamar yadda ya saba amma daga bisani yakamu da wata rashin  lafiya inda ta kaishi da kwanciya, a, Asibitin na London, kuma...

Rasuwar Aminu Dantata,Kano ta farka da alhini

Image
    GABATARWA  M una ci gaba da kawomuku abinda yake wakana a kasa baki daya a wannan shafi namu mai suna nishadisport ga labaran dallah-dallah. Alhini a Kano: Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata Ya Rasu Kano, 27/06/2025 – An tashi da jimami a jihar Kano da ma duniya baki ɗaya sakamakon rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin dan kasuwa  mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata. Wanda ya rasu yana da shekara 94, a kasar Dubai . Bayan wata gajeruwar jinya. Awani asibiti dake birnin na Dubai.Inda yake karbar jinya a chan. Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana’izarsa ne a Madina , Saudiya, kamar yadda ya bukata a wasiyyarsa.  A nan Kano kuwa, an gudanar da sallar jana’izar ga’ib ,a masallacin Aliyu bn Abi Talib, kar kashin jagoranci shek Ibrahim Khalil. Wadda ta samu halartar manyan baki ciki da wajen jihar, har da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , da sauran jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, da manyan ‘yan kasuwa daga ciki da wajen jihar. Madina ...

Anrage farashin mai

Image
          GABATARWA    Assalamu alaikum masu binmu a wannan shafi namu mai Suna.  nishadisport.blogspot.com barku da sake haduwa damu har kullum ni ne naku "Sadik Yusuf" ga abinda yake wakana a wannan rana ta Talata 1/7/2025,kamar haka.    MATATAR MAI TA DANGOTE TA SANAR DA RAGE FARASHIN MAI  Matatar mai ta dangote,  ta sanar da rage farashin mai daga Naira dari takwas da tamanin, zuwa naira Dari takwas da arba'in, a gidajen mai na yan kasuwa, mu samman ma gidajen dake da alaka da Dan Gote kamar irin su (M R S) da sauransu.  Hakan ya biyo bayan tsayar da yaki tsakanin Isra'ila da Iran, wanda tun a farko yakin ne ya jawo tashin man, kuma yanzu da yakin ya dakata farashin ya sauka, har mutane sun fara cece-kuce  kan karin man.  Har gidajen man sun fara rufewa da jin labarin tashin man fetir din. To abin jira agani dai yanzu raguwar farashin ya fara aiki nan danan, kar yan kasuwar man suyi  abin da suka saba, s...

Nigeria a yau

Image
GABATARWA  Salamu alaikum masoya wannan dandali namu wanada muke kawo muku labarai da al'amura na yau da kullum da zaman takewar al’umma, nine naku Sadik Yusuf nake kawomuku labaran.   YAN WASAN DA SUKA WAKILCI JIHAR KANO SUNA HANYAR DAWOWA DAGA ENUGU,  SUN GAMU HADARIN MOTAR DA YA YI SANADIYAR MUTUWAR MUTANE 22 Yan wasan da suka wakilci jihar Kano, a wani wasan da aka fafata a jihar Enugu, yayin dawowarsu gida sun gamu da hadarin mota. ● Mutum ashirin da biyu sun mutu  Wannan mummunan hadari ya yi sanadin mutuwar mutane 22, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata. Ciki harda masu horaswa,da 'yan wasa, drebobi, da sauransu.  Jama’a da dama da suka jikkata suna karbar magani a asibiti inda ake basu kulawa ta musamman. Wadanda suka rasa rayukansu kuma, an yi jana'izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.  Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini tare da jajantawa iyalan mamatan, da daukacin al’ummar Kano. Haka zalika, ya sha alwashin dau...

Shekara 1 da Tinibu talaka ya koka

📰 Rahoton Musamman: Shekara Daya da Bola Tinubu – Talakawa na Cikin yanayi! Assalamu Alaikum Jama'a, da fatan kun wayi gari lafiya. Kuna tare da ni, Sadik Yusuf , a dandali na NishadiSport. GABATARWA A yau muna dauke da rahoto na musamman, game da halin da Najeriya ke ciki, shekara guda bayan hawan shugaba  Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki. ⚠️ Halin Talauci da Tsadar Rayuwa  Ana bikin cikar gwammnatin A P C hawa karagar mulkin  Nigeria shekar biyu. A cewar jama’a da dama, ba’a gani ba, a kasa sai dai ana ji a jiki – babu wani cigaba da talaka zai iya nunawa, cewa gashi yasamu sauki a wannan gwamnati. Ana cikin ma wuyacin hali a wannan lokaci na mulkin farar Hula, abin ba'a cewa komai sai dai neman sauki a wannan kasa Nigeria. Ga wasu daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye rayuwar yau: 🔌 Rashin wutar lantarki 💧 Rashin ruwan sha 🎓 Ilimi ya tabarbare 🔫 Rashin tsaro – ana kisa kullum, ana ji, ana gani 🍞 Tsadar abinci – hatta biredi ya gagari talak...