Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku labarai da sharhi kan al amuran yau da kullum. A wannan shafi namu na blogs nishadisport.blogspot.com.
Nine naku "Sadik Yusuf" nake gabatar muku da labaran.
A yaune Lahadi tsohon shugaban kasar NIgeria. Muhammadu Buhari. Ya rasu a kasar ingila inda yake jinya Kar kashin likitoci,mai magana da yawun tsohon shugaban kasa. Garba Shehu ya fitar da wata sanarwa,in da yace:
"ya rasu ne da misalin karfe 4:30 sakamakon doguwar jinya."
A cewar fadar shugaban kasa, Bola Ahamad Tinubu ya umarci matemakinsa, Kashim Shattima da yaje birnin na London ya rako gawar ta Muhammadu Buhari zuwa gida Nigeria.
A makon jiyane shugaban yaje birnin London domin duba lafiyar sa kamar yadda ya saba amma daga bisani yakamu da wata rashin lafiya inda ta kaishi da kwanciya, a, Asibitin na London, kuma har rai yayi halinsa.
Kadan daga tarihin sa
Muhammadu Buhari ya rasu yana dan shekara 83 dan asalin jihar Katsina state, karamar hukumar Daura inda yayiwa shugaba Shagari na mulkin farar hula juyin mulki a dalin rashin iya shu gabanci injishi.
Shi kuma bai dadeba "Ibrahim Badamasi Babangida" yayi masa juyin milki. Shima yayi zargin cewa a kwai gazawa a gwammnatin ta Buhari.
Ha kuma Buhari ya tsaya takara a kar kashin farar
Hula har sau uku amma baiyi nasara ba.Inda yace daga wannan zabe bazai sake takaraba,sai akaro na hudu ne
Inda gungun yan adawa suka hadu suka maramasa baya har ya samu yakai labari a kar kashin jam"iyar A P C.
Ya tsaya takara yana kan mulki Ya kuma cin zabe a karo na biyu, ya kawo sauye sauye a fannin tattalin arziki wanda hakan ya jefa mutane cikin halin ha ula'i har yanzu ana fama da matsalolin da gwammnatin sa ta haifar.
An sauke wani basarake
A wani labarin kuma gwamnan Katsina "Umar Dikko Radda" ya sauke wani basarake da wasu jami'an gwamnati a saboda wani korafi da fulani suka shigar a kansu.
Gwamnan ya dauki wannan matakine don tabbatar da samun zaman lafiya, gwamnan ya bukaci a gudanar da binceke duk wanda aka samu da laifi a yimasa hukunci kamar yadda doka ta tanadar, abin jira agani dai ayi bin ciken kuma ayi adalci kamar yadda gwamnan yafadi.
A wani cigaban Kuma kamfanin man petir na kasa yayi kira ga masu zuba jari na kasashen waje da suzo su zuba jari a kamfanin saboda an yi wasu gyare gyare a fannin inda ya dace ga masu zuba jari na duniya.
Ya baiyyana hakane mataimakin shugaban kamfanin "Udy Ntia", a wani taro da akayi da masu zuba jari a "hostun Texas" na kasar Amurka.
Da yake jawabi domin janyo masu zuba jari a fannin na mai da iskar gas. Yake fada cewa:
"yanzu Nigeria ta kai matsayin da masu zuba jari ke bukata domin al'ummar kasar suna dada fadada, masana'antu suna da cigaban da ake bukata, saboda tashe tashen hankula da ake fama da shi na bangarorin yankin da siyasa ta Amurka, agaremu a Nigeria duk da rashin tabbas na makamashi a duniya ciki har da turai.
Muna ganin dama mai Mahimmanci in jishi,mun tsara dabarunmu don yin amfani farashi mai karfi na yanzu yanda zai dace da ko ina muna ganin zamu samu zuba jari mai yawa nan da she karu biyu masu zuwa."
Fadakarwa
Yanzu anshiga damina, mutane suna da wata al'ada ta zuba shara a magudanen ruwa, ko yin gada wadda bata daceba, akoi'ina cikin birnin Kano da kewaye.
kuma hakan shi yake haifar da ambaliyar ruwa amma kuma sai mutane suki taruwa su yashe kamar yadda akeyi a baya wanda ake kira da (aikin gayya),
Anata bangaren gwammnatin jiha tana iya kokarinta wanjan fadakarwa da mutane suguji zuba shara a magudanan ruwa, amma sai mutane suyi kunnen uwar shegu suki bin umarnin gwamnati.
To amma ya kamata gwammnati ta sanya doka duk wanda aka samu yana zuba shara a magudanen ruwa akamashi don magance hakan.
kuma in ambaliya ta faru mutane suyi ta kuka suna neman taimako yakamata mutane su kiyaye su guji zuba shara a kwata da gina gadoji da basu daceba.
Nema
Hukuma tai makon gaggawa wayo (nema) itama anata bangaren tana iya kokarin ta na fadakar da mutane su guji zama a inda yake da barazanar ambaliya musamman inda yake a kwai Kogi a gurin.
Sukan fitar da sanarwa, cewa ga guraren da zasu iya fuskantar ambaliya don haka mutane sukiyaye.
Fadakarwa
Wani lamari mai tayar da hankali da yake faruwa a wannan kasa tamu Nigeria, a bangarori daban-daban na kasar shine yadda ake samun yawaitar kifewar kwale- kwale musamman lokacin damuna.
Abinda ke faruwa mutane suna da laifi wajen hawa jirgin sa lodin da ya wuce kima, ana daukar su, su da kayansu a cikin girgin kaga anzuba mutane, shanu,da awaki, babura,da dai sauransu.
Hakan shine yake haddasa kifewar jirgin sai abu yafaru kuma ayita cece-kuce ana surutai, ayita kokarin ganin an ceto wanda suka nutse wasu asamu gawarsu, wasu kuma arasa su, basu ba gawarsu.
Mutane surika kin hawa jirgin indai sunga lodi yayi yawa don kare dukiyarsu da rayukansu.
Gwamnati:
Ita kuma anata bangaren tasa ido wajen lura da masu tuka jirgin waje ganin sun kai'dar an fani dashi, asa doka duk wanda ya karya a hukuntashi ko asamu raguwar hakan.
Basai abu yafaruba ace za'a kawo dauki wanda abinda ya faru ya faru, kuma surutu mai zaiyi.
Alhakin kare rayuka da dukiyar al'umma yana wuyan gwamnati ita Allah zai tambaya ya ta tafi da rayuwar mutane, wani gurin gada suke bukata,in anyi gadar shikenan an magance wannan matsala Allah yasa mutane su fadaka ,gwamnati ta gyara amin.
Daga sadik Yusuf muna sauraron ku a comment section.
ko a tuntubemu ta hanyar imel
sadiku854@gmail.com
Na gode!
Comments
Post a Comment