DUKAN DUHU- KASHI NA 3
GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna ( nishadisport). Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!. Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3 SALE DAURE A WANI KANGO Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit. Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba. Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace: Alhaji: "Malam Salele mai liki, yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soya...