Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku sharhin abinda ke faruwa a sassan Nigeria nine naku Sadik Yusuf.
Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya gamu da hadari.
A ranar Lahadine wani lamari da ba'a saba ganiba a Nigeria ya afku wato ace Gwamna mai ci yayi hadari. Wato Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda, yayi hadarin mota a hanyarsa da yataho daga Daura zuwa katsina.inda wani dreban Golf yayi aron hannu shi ya sa hadarin ya afku.
Hakan na faruwa nan da nan aka garzaya dasu asibit dake Daura Aka duba lafiyar su, su uku ne acikin Motar. Inda daga bisani kuma aka garzaya dasu asibitin tarayya na jihar Katsina.
Umar Dikko Radda
Daraktan yada labarai na Gwamnan Katsina Maiwada Dan Malam yatabbatarwa manaima labarai lqmari inda yake cewa."bayan abin yafaru. Aka kaisu wani asibiti dake Daura,aka basu taimakon gaggawa inda daga bisani kuma aka garzaya dasu asibitin (teaching hospital dake birnin Katsina.
Kwararrun likitoci suka cigaba da dubasu don a tabbatar ba wata matsala a cewarsa".
Gwamnatin Katsina tace anyi gwaje- gwaje an tabbatar ba wata matsala da Gwamnan yake ciki.
Mai Wada Dan Malam yace: "akwai mutum uku da abin yafaru har da su, ciki akwai (chif up staff ) Alhaji Mamman Nasir da kuma hakimin Kuraye da Shamsu Funtua.
To dukkansu ba wani mummunan lamari, sai dai akwai me bukatar dinki kuma anyi masa. Yanzu haka suna cikin Katsina sun bar Daura inji Maiwada Dan Malam."
"Daraktan yada labarai na Gwamnan Katsina yace Gwamnan ya dauki matakin rage motocin jerin gwanonsa saboda yana yawan xuwa Daura saboda rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana yawan shige da fuce a hanyar.
Shine yarage motocin zuwa uku don arage kashe kufin al'ummar jihar,"
Wanan bayani na daraktan ya musanta abinda wasu suke ta yadawa a shafukan sada zumunta inda suke cewa Gwamnan yana cikin mawuyacin hali a dalilin hadarin da ya rutsa dashi a ranar ta Lahadi.
Anga gwamnan a wani faifan bidiyo
Anga gwamnan na Katsina a wani faifan bidiyo inda yake cewa:
"muna godiya da addu’oinku Allah ya jarrabemu da hadarin Mota kuma muna nan a asibiti muna samun sauki mungode sosai Allah ya bar zumunci".
Wani dan social media yana gwabawa gwamnan katsina magana inda yake cewa: "ga inda ya kamata gwamna yayi kuka ana sace yara a makarantu ana kashe na kahewa amma gwamna ba kai kukaba sai da Buhari ya mutu to Allah ya sawaka".
Allah ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Sanata Natasha da majalisar tarayya,
A wani lamarin kuma sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya Natasha Akpoti, ta kudurci aniyarta ta komawa Majalisar Dattawa a Nigeria,"ta gudiri aniyar komawa Majalisar ranar talata. Biyo bayan wani hukunci da kotu ta yanke karkashin mai shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya dake Abuja".
Sukuma yan majalisar suna nan kan da
katarwar da sukaimata sunce hakan ya karya dokar majalisar.
Natasha Akpoti
To Allah ya kyauta fadan manya sai manya yakamata a maida wukar cikin kube don samun zaman lafiya daGa wani hoto na Seneta Natasha Akpoti-Uduaghan a majalisar dattawa, inda ake iya ganin ta a matsayin abun tattaunawa a baya-bayan nan, musamman game da rigimar da ta jawo hankali a Najeriya.
Tarihin Natasha Akpoti
Natasha Hadiza Akpoti-Uduaghan yanzu ta kasance Sanata ta Kogi Central ita ce mace ta farko da aka zaɓa a wannan matsayin a jihar Kogi, kuma tana wakiltar Majalisar Tarayya ta kasa (10th National Assembly) tun daga Nuwamba 2023 ta kasance a ciki.
Rayuwarta:
An haife ta ne a ranar 9 ga Disamba, 1979 a Ilorin, Kwara State Nigeria.
Mahaifinta shi ne Dr. Jimoh Abdul Akpoti, likita daga Kogi, mahaifiyarta kuma 'Yar Ukraine ce, Ludmila Kravchenk .
Ta yi karatun digiri na farko a Dokar LLB a Jami’ar Abuja (2000–2004), sannan ta kammala Nigerian Law School kuma an yi mata kira (called to bar) a shekarar.
Daga baya kuma ta samu LL.M. da MBA (Oil & Gas Management) daga Jami’ar Dundee, Scotland,daga kasar waje.
Aiyukan da tayi:
Ta fara aiki a matsayin lauya a kamfanin Brass LNG daga 2007 zuwa 2010, a Nigeria.
A shekarar 2015, ta kafa tashar Builders Hub Impact Investment Program (BHIIP)—tsarin taimakon jama’a da bayar da tallafi kan ci gaban masana’antu, da al'umma a kasa Nigeria.
Ta shahara kwarai a Najeriya lokacin da ta gabatar da rahoto ga Majalisar Wakilai a 2018, inda ta yi tir da rashin gaskiya da cin hanci da rashawa a Ajaokuta kamfanin karafa na Nigeria, kar kashin gwamnatoci da ban daban-daban.
Siyasarta:
Ta fara neman kujerar Sanata a 2019 ta karkashin jam’iyyar SDP (Social Democratic Party), amma bata yi nasara ba. Amma bata sareba taci gaba da siyasa.
A 2023, ta sake neman kujerar karkashin jam’iyyar PDP (People’s Democratic Party).
Duk da an bayyana cewa ta sha kaye a zaben farko, Kotun Daukaka kara ta soke sakamakon zaben, ta kuma bata kujerar a matsayin Sanata, matsayin da take a halin yanzu.
Ta samu lambohin yabo:
An bata lambar yabo ta "Politician of the Year" daga Leadership Excellence Awards (2023), an kuma kirata "People of the Year" a wannan shekarar. Saboda jajircewarta.
Ta samu kalubale:
A cikin Fabrairu 2025, Natasha ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da nemanta da lalata yayin wani ziyara da takai a gidansa .
Wannan zargi ya jawo cece-ku-ce a kasar, har ma da kasashen waje,amma Hukumar Ladabi ta Majalisar ta dakatar da ita sakamakon wannan zargi da tayi akan Apabio
A ranar 6 ga Maris 2025, an yanke mata hukunci na dakatar da ita daga majalisa na tsawon watanni shida an hana ta shiga ofis, kuma an hana ta albashi da tsaro bisa dalilan rashin bin doka da tozarta majalisa .
A wani martani dalilin haka, wasu kungiyoyin kare hakkin bil dama da mata sun shirya zanga-zangar lumana a jihohi daban-daban, na kasar, suna nuna goyon baya a mayar da ita kan mukaminta a matsayin cewa an zalunce ta a majalisar.
Mutane suna ganin cewa an zalinceta, ya kamata ayi bincike na gaskiya,ko asamu dai-daito a siyasar Nigeria.
Me Natasha Apoti take ciki?”
A takaice, tana cikin wani rikici mai zafi na siyasa da jarunta, inda ta tsaya daga baya kan kiyaye mutuncinta da kawo sauyi.
Duk da matsaloli, ta kasance ginshiki ga 'yancin mata da tsai da gaskiya a Najeriya. Yanzu haka tana ƙarƙashin hukuncin dakatarwa na watanni shida, amma hakan bai rage kwarin guiwa da ganin yaƙin da take bai ƙareba. Madallah.
Daga sadik Yusuf.
Tuntubemu: sadiku854@gmail.com.
Comments
Post a Comment