Anrage farashin mai
GABATARWA
Assalamu alaikum masu binmu a wannan shafi namu mai Suna. nishadisport.blogspot.com barku da sake haduwa damu har kullum ni ne naku "Sadik Yusuf" ga abinda yake wakana a wannan rana ta Talata 1/7/2025,kamar haka.
MATATAR MAI TA DANGOTE TA SANAR DA RAGE FARASHIN MAI
Matatar mai ta dangote, ta sanar da rage farashin mai daga Naira dari takwas da tamanin, zuwa naira Dari takwas da arba'in, a gidajen mai na yan kasuwa, mu samman ma gidajen dake da alaka da Dan Gote kamar irin su (M R S) da sauransu.
Hakan ya biyo bayan tsayar da yaki tsakanin Isra'ila da Iran, wanda tun a farko yakin ne ya jawo tashin man, kuma yanzu da yakin ya dakata farashin ya sauka, har mutane sun fara cece-kuce kan karin man.
Har gidajen man sun fara rufewa da jin labarin tashin man fetir din.
To abin jira agani dai yanzu raguwar farashin ya fara aiki nan danan, kar yan kasuwar man suyi abin da suka saba, suce basu sayar da na bayaba, amma inkari yazo kawai ba jiran kawo sabon mai, sai su kara kudi, Allah ya kyauta.
Ya kamata dillalan man fetir su rika yin abin da ya dace na saukakawa jama'a masu sayen man, ko mutane saji saukin radadin rayuwa.
ZA'A, MAYAR DA GWAMNAN JIHAR RIVERS
A wani labarin kuma, shugaban kasa Bola Ahamad Tinibu, yana shirin mayar da gwamnan jihar rivers, Simalye fubgbara, kan matsayin sa na gwamnan jihar bayan samun sulhu da uban gidansa na siyasa tsohon gwamnan jihar, ministan babban birnin tarayya Abuja.
Wato Iwelson Wike, shugaban kasa ya shiga tsakani yayimusu sulhu, wanda manya na jihar suka halarci taron ciki harda kakin majalisar jihar.
Rudanin siyasa ya barke ne a tsakanin gwamna kubarah da Wike, sakamakon rashin jituwa a tsakaninsu har abin ya kusa rusa tattalin arzikin jihar. Da kuma rarrabuwar kai a tsakanin manya yan siyasar jihar, Suna nunawa Juna yatsa.
Yanzu dai ana fatan komai ya zo karshe, sakamakon sanya dokar ta baci a jihar. Da Bola Ahamad Tinubu yayi.
A NASA RAN BINNE DANTATA
A yau talatane kuma ake sa ran binne Alhaji Alhasan Dan Tata marigayi ,sakamakon tsaiko da aka samu wanda tun da farko an shirya binne shi a ranar litinin da tagabata.
Hakan yasamo asaline saboda cike-ciken takardu da akeyi, tsakanin ofishin jakadanci na Nigeria da na saudiyya, da kuma iyalan mamacin,wanda tuni birnin na madina ya karbi manyan baki daga Kano, da ma Nigeria baki daya da gwamnonin arewa.
kuma yanzu janaizar tasa ta koma zuwa magariba sabanin yanda akashirya yi tun a baya. zuwa la'asar tunda farko.
A tabakin mataimakinsa na musamman, Muhammadu Mustafa Junaid, shi ya bayyana hakan, "yace tuni gawar tasa ta isa Birnin na Madina, za'a shirya gawar kafin daga bisani akaishi masallacin shugaban halitta baki daya, a gudanar da sallah, kana a binne shi.
Haka gwamnan Jigawa Namadi Sambo, da kuma gwamnan kano, Abba Kabir Yusuf suka kaiwa iyalan mamacin ta'azyya a birnin na madina.
Allah hu Akabar. Allah ya jkansa ya gafartamasa, ya kyauta makwanci amin.
Aminu Alhasan Dan Tata, ya samu gagarimin martabawa sakamakon da hukumar saudiyya ta bayar na a bari a shiga kasarta a binne shi, hakan yasamo asaline na da ga, daddiyar alaka dake tsakaninsu tun shekarun baya sanda yake da rai, abokinsu ne na kud da kud.
Ba kowane yake samun hakaba, ya mutu a wata kasa kana a kaishi birnin na madina a binne sai, dai-dai. Allah yasa mudace amin.
MATSALAR YARA MASU GOGE GILAS A KAN TITUNA
Wani lamari da yakunno kai cikin wannan jiha tamu ta Kano, wato shine zakaga yara kana yan mata da basu wuce shekara bakwai zuwa takwas ba, suna bi bakin danja suna goge gilas din Mota, kamar yadda maza keyi wani lokacin kuma suna bi suna bara.
To matsalar anan itace, makomar yaran nan gaba, ya zata kasance, yara ba makaranta sun zama uwa ba kwaba zakaga sunata fada akan abinda ake basu.
Suyita gunduma ashar akan titina na birnin Kano. Muna kira ga hukuma ta kalli wannan lamari tun kafin yayi Girman da magance shi zaiyi wahala, domin su Allah ya dorawa kula da hakkin mutane.
Gwamnati tayi duk me yiwuwa wajen ganin ta magance wannan lamari domin a samu yara nagari a nan gaba, asamu a sasu a makaranta don gobensu tayi kyau.
Don a haifi da mai ido nan gaba, saboda barin yaran a haka yana da mummunan hadari a gaba, suke zama matsala ga kasa, su zama yandaba ko barayi 'yan shaye-shaye, Allah ya shiryi bayinsa yabasu abunyi amin.
ZAMBA DA DAMFARA.
Haka kuma wani sabon lamari da ya kunno kai cikin al’umma, wato shine za'a sanyawa yaro takarda dauke da adreshin wani guri a jikinsa, sai yaron ya futo kan hanya yana kuka.
To idan akasamu wani ya tausayamasa, ya ga wannan takarda a gaban Aljihun yaron, ya tausaya sai ya dauki yaron da zummar ya kaishi ga wannan adreshi da yagani.
To dazar yaje wannan guri, sai wannan mutane suyimasa fashi,kudi ko waya ko kuma abin hawan nasa dugurum, wannan lamari an bayyanashine a tagwayen Gidan rediyo na Kano.
Ta bakin Malam Nuhu Gudaji inda akewa Malam Ibrahim Khalil tambaya kan mai zaice game da wannan al'amari.
Malamin yace "to kamata yayi duk wanda aka gani da irin wannan takarda a jikinsa, koma babu to mutum ya kaiwa 'yansanda wannan yaro domin sune suke da iko a hannunsu na kama duk wani mai laifi. Domin su suka san doka.
"Yakara da cewa ko mai unguwa kada a kaiwa, domin shima yana iya cewa zaije ya kai yaron kuma a illatashi, don haka muna kira da mutane sukula sosaia. karshe yayi addu'ar Allah ya kawo karshen wannan lamari baki daya mutane su hau kan layi sudena mugun abu."
SADAKI DA ZAKKA A KANO
Hukumar zakka ta Kano tayi kira da malamai su zauna a fidda matsaya dangane da abinda ya shafi harkar sadaki da zakka.
Inda akeso sadaki mafi kankanta yazama naira dubu Ashirin, haka itakuma zakka ta zama daga Naira Miliyan daya shine nisabi.
Malamai sun yarda da wannan lamari, inda akayi duba da darajar Azurfa tunda ana aunawa da zinare, kuma ana aunawa sa Azurfa.
Ya danganta da yanayin da ake ciki, to Allah yasa mu dace amin.
๐ KAMMALAWA
Ni ne naku Sadik Yusuf. Nakawo muku wannan labarai da fatan an fadaka, Allah ya kara bamu sauki na farashin kayayyaki amin.
A cigaba da bibiyarmu a NishadiSport.
Nagode! za'a iya tun tubarmu ta hanyar imel namu .
Sadiku854@gmail.com. ko lambar waya 07082643256
Gwamnati ki farka
ReplyDeleteAllah ya kawo sauki
ReplyDeleteAllah ya kawo sauki
ReplyDelete