Shekara 1 da Tinibu talaka ya koka

๐Ÿ“ฐ Rahoton Musamman: Shekara Daya da Bola Tinubu – Talakawa na Cikin yanayi!

Assalamu Alaikum Jama'a, da fatan kun wayi gari lafiya. Kuna tare da ni, Sadik Yusuf, a dandali na NishadiSport.
A yau muna dauke da rahoto na musamman game da halin da Najeriya ke ciki shekara guda bayan hawan shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki.

⚠️ Halin Talauci da Tsadar Rayuwa

 Ana bikin cikar gwammnatin A P C hawa karagar mulkin  Nigeria shekar biyu. A cewar jama’a da dama, ba’a gani ba, a kasa sai dai ana ji a jiki– babu wani cigaba da talaka zai iya nunawa cewa gashi yasamu sauki a wannan gwamnati. Ga wasu daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye rayuwar yau:

  • ๐Ÿ”Œ Rashin wutar lantarki
  • ๐Ÿ’ง Rashin ruwan sha
  • ๐ŸŽ“ Ilimi ya tabarbare
  • ๐Ÿ”ซ Rashin tsaro – ana kisa kullum, ana ji, ana gani
  • ๐Ÿž Tsadar abinci – hatta biredi ya gagari talaka
  • ๐ŸŒพ Wake ana aunawa kwano – Naira 4,000!
  • ๐Ÿฅ Lafiya? Komai sai mutum yayi da kansa
  • ๐Ÿš Shinkafar gida (mudu) – Naira 3,800!

A irin wannan yanayi, jama’a da dama sun shiga halin kaka-nika-yi, inda ake tambayar cewa to ina talaka zai sa kansa? Lamarin rayuwa daga wannan sai wannan, uau kaji ance an cire tallafin mai sai kuma kaji ance an cire na wuta ko kuma na asibiti wanda manufofin shugaba Bola Ahamad Tinubu sun jefa al'ummar Nigeria cikin halin ni 'ya su.

Mutane suna mutuwa saboda basu da kudin magani a asibiti,o abin da zasu sa a bakinsu wasu sai sun roko kana suke samu,wasu kuma su cinye dan jarin da suke dashi sai su dawo su tsuguna.

Ana fatan ganin samun sauki a wannan yanayi na kunci,gwamnati ta san yanda zatai don ganin al'umma sun samu sauki muna fatan haka.

๐Ÿช– Sojoji Sun Fara Taka Tsantsan

A rahotonmu na musamman, sojoji sun bayyana cewa ba za su lamunci kisan da ake yi wa ‘yan uwansu ba.

Domin ana bi har barikinsu akashesu a dauke makamansu sinajj suna gani wannan daliline yasa babban hafsan sokin ya magantu cewa bazasu laminci wannan lamariba na kisan 'yan uwansu, yakamata sojoji su farka su san abinda sukeyi su kula da kansu, wanda sune alhakin kare kasa da 'yankasa ya rataya a wuyansu to suma ana musu kisan mummuke yo ina kuma ga talakawa.

yakamata gwamnati ta samar da yanayi mai kyau na sabunta harkar tsaro a Nigeria, a samar da kayan aiki na zamani hakan zai taimaka wajen kawo karshen wannan lamari.
To abun jira a gani  – shin sojojin za su dauki mataki ko kuma zance ne kawai?

Allah ya kyauta.


๐Ÿ„ Tsadar Sallah Babba – Shanu da Raguna Sun Zama masu tsada ๐Ÿช

Yayin da Sallah Babba ke tafe, tsadar dabbobin layya na kara kamari:

  • Shanu da raguna suna kara tsada kowace rana.
  • Jama’a da dama suna kasa sayen dabba saboda matsin tattalin arziki.
  • Ana ganin hakan ya samo asaline saboda shugaban kasar Niger Muhammadu chani ya hana futa da dabbobi daga kassr tasa domin shima 'yan kasarsa su samu sauki.

  •  Sukuma 'yan Nigeria suna ganin wannan matakine ya haifar da wannan mummunan tsadar dabbar saboda kusan duk Shanun daga kasar ta Niger ne ake shigowa dasu.

Mungana da wani mazaunin birnin Kano (wanda ya bukaci a boye sunansa), ya bayyana cewa:

"Ai tsadar abinci ta fi komai a yanzu. Babu maganar sayen dabba, kawai dai idan anyi hadin gwiwa ana samun nama."

Wasu mutane suna hada kudi – mutum 7 ko fiye – domin sayen dabba guda, domin yin layya cikin hadin kai, yayin da wasu kuma kawai suke sayen nama domin su dandana daga cikin albarkar Sallah. 

kuma iyali suma suce sunyi siya mutane sukance a maida mugun yawu ko kuma kar yara su shiga makwafta suga ana suya sukuma ba'ayi a gidansu wasu kuma sukance kafi zuru. Allah ya kawo sauki.

Tsokaci Sallah ta wuce ta bar wawa da bashi.๐Ÿ

Hauswa su kance! Sallah tawuce ta bar wawa da bashi. Hakan yasamo saline saboda musulunci bai ce lallai sai mutum yayi layyaba. 

Layya Sunace ba farillah ba amma dai sunnah ce mai karfi gamasu hali suyi duk shekara ta babbar Sallah wanda bashi da hali ba'a ce lallai sai yayiba don haka ba'a ce mutum yaci bashiba domin yin layya.

Manzon tsaira annabin rahama, ya yi layya fa manyan Raguna guda biyu, yace daya nawa daya kuma na al'umma ta ga wanda bai yiba. Yo kaga kar ka takurawa kanka wajen. Cewa lallai sai ka yi musulinci yana sauki da afuwa Allah ya hore mana abin yin layya amin.

Halin mutane na boye nama

Wani lamari kuma na halayyar mutane wanda suka samu sukayi layya shine, rowa da kima boye nama.

Allah subhanahu wata' ala ya umarci mutane cewa in sunyi layya to su kasa naman guda uku, daya suci daya kuma su bayar daya su aje.

 To amma sai kaga ba'a yin hakan dan kadan ake ba mutane wani lokacin kuma abaka mara kyau wanda ba'a so, kk hanji ko kitse, mutane sukan aje nama har tsawon shekara guda wata Sallah ta tarar da wata kuma naman har rubewa yake amma bazasu ciba baza su bayarba ko mai zasuyi dashi? Oho!.

yakamata mutane su rika bayar da nama fi sabilillahi domin abin da ka bayar shi zaka tarar wanda kwci kuwa kashi zai zama wanima ya zamema cuta don haka mu kiyaye. Allah ya hore. 


๐Ÿงพ Kammalawa

Halin da ake ciki a Najeriya yanzu na bukatar addu'a, hakuri, da kokari daga kowa da kowa.
Gwamnati na da alhakin saukaka rayuwar talaka, amma har yanzu jama’a na fama da matsaloli kala-kala.kama da rashin mahalli,rashin abinci,ga kuma lafiya. Wa yannan kullum zaka ga mutane sunabi kwararo kwararo suna neman a temakamusu.


Muna rokon Allah Ya kawo sauki, ya ba mu zaman lafiya da saukin rayuwa. Amin.


Mawallafi: Sadik Yusuf
๐ŸŒ nishadisport.blogspot.com
๐Ÿ“ง sadiku854@



Comments