Posts

Showing posts with the label dukan duhu

DUKAN DUHU- KASHI NA 3

  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna ( nishadisport). Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!. Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3  SALE DAURE A WANI KANGO  Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit. Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba. Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace: Alhaji:  "Malam Salele mai liki,  yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soya...

DUKAN DUHU KASHI NA 2

DUKAN DUHU KASHI NA BIYU  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, wanda muke kawomuku dadadan labarai masu cike da darasi, waɗanda suke taba zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum. Zamu ci gaba da kawo muku cigaban labarin "DUKAN DUHU KASHI NA BIYU" . Sai ku biyo mu a hankali don jin yadda zata kaya. Ni ne naku Sadik Yusuf , na gode! SAILUBA TAJE WAJEN KAWARTA NEMAN SHAWARA Sailuba tana ba kawarta labarin yadda sukai da Alhaji. Ita dai Halima ta tsaya tana sauraronta, tayi zugum da ido. Halima tace: "Nidai abinda zan gayamiki Sailuba, ki nutsu ki tsaya wajen talakanki, domin shi yafi dacewa da ke. Kar ki jifan gafiyar baidu." Sailuba ta harareta cikin mamaki, tace: "Yau kuma kece mai fadin haka? Ke da nake zato zaki maramin baya, amma sai naji wata banzar magana ta futo daga gareki haka." Halima ta kara cewa: "To ai gaskiya ne. Abinda yasa kika ga ina kin sale, saboda naga ba’a sa muku rana ba, kuma ba’a yi baikon ba. Tu...