Posts

Showing posts with the label sadik Yusuf

DUKAN DUHU KASHI NA 2

DUKAN DUHU KASHI NA BIYU  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, wanda muke kawomuku dadadan labarai masu cike da darasi, waɗanda suke taba zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum. Zamu ci gaba da kawo muku cigaban labarin "DUKAN DUHU KASHI NA BIYU" . Sai ku biyo mu a hankali don jin yadda zata kaya. Ni ne naku Sadik Yusuf , na gode! SAILUBA TAJE WAJEN KAWARTA NEMAN SHAWARA Sailuba tana ba kawarta labarin yadda sukai da Alhaji. Ita dai Halima ta tsaya tana sauraronta, tayi zugum da ido. Halima tace: "Nidai abinda zan gayamiki Sailuba, ki nutsu ki tsaya wajen talakanki, domin shi yafi dacewa da ke. Kar ki jifan gafiyar baidu." Sailuba ta harareta cikin mamaki, tace: "Yau kuma kece mai fadin haka? Ke da nake zato zaki maramin baya, amma sai naji wata banzar magana ta futo daga gareki haka." Halima ta kara cewa: "To ai gaskiya ne. Abinda yasa kika ga ina kin sale, saboda naga ba’a sa muku rana ba, kuma ba’a yi baikon ba. Tu...