DUKAN DUHU- NA DAYA
GABATARWA Salam yan uwa masu bin wannan shafi namu na blogs, wato nishadisport munamuku maraba da sake saduwa, nine naku Sadik Yusuf, ga sharhin shirin " Dukan Duhu." Bayanin shirin Wannan labari da akawa lakabi da " Dukan Duhu" labarine da yake nuna cewa kada mace ta juya baya, bayan angama komai na sha'anin aure. Saboda hakan ya haramta inko aka aikata haka to sai a saurari abinda zaije yazo. Kamar dai yadda aka musalta a wannan labari, kuma labarin ba da wani akeba, madallah. A gidan su Sailuba Suna magana da Babanta da mamanta. Umma tana magana tace: "Wai, ni, baban Sailuba, mai katanada dangane da bikin wannan yarinya Sailuba." Baban Sailuba yace: "To,! Amma dai kinfi kowa sanin halin da na tsinci kaina a yanzu ya kike so nayi, sata ko fashi" ta tari numfashinsa. Umma: "To,! duka, kaje kayi mana, ni dai kawai a wuyanka nake neman Gado da Kawaba ehe!" Nan ya yanke jiki ya fadi kasa tum, yasamu shanyewar barin jiki dama...