Ankorota cikin dare

    A cigaba da kawo muku sharhin Shirin film din "YAR MALAM" daga Sadik Yusuf gashinan zan dora. Ku kasance damu a wannan shafi namu na blogs. Muna godiya.


   Wani abin mamaki ko kuma abin takaici wai Dogo chikin dare ya koro Ladidi daga gidan ubanta saboda wai sun sayar da wannan gidan da take ciki, wai tunda taki konawa gidan su Dogo, inda uban Dogo wato Idi yace takoma.  Dogo yace to sai takoma wani tsohon gidansu, kuma tsohon gidan ba kowa a ciki kuma Babu komai wai a haka zataje ta zauna. 

Bayan yatafi Ladidi tana kuka ta rasa me ke Mata dadi, saiga kawarta ta iso Dan ta kawomata abinci sai ta ganta zaune tana kuka bakin kofa.  Kawa ta tambayeta lafiya , Ladidi tace: 

"Wai Dogo ne ya korota wai yasayar da wannan gidan da take ciki."  kawa tai salati tace:

Kawa:
 "yanzu a wannan tsohon Daren yakoreki to  shi ya haukacene naga gidan ai nakine da  zasu koroki kai wannan mutane suji tsoron gamuwarsu da Allah yana nan a madakata baya bacci kuma baya zalunci sukiyayi haduwarsu.

  "Allah ya sawake yanzu tashi muje gidanmu ki kwana in yaso gobe kin koma." Ladidi tana hawaye tace:

Ladidi:
 "ah ba'ayi hakaba ki barni dasu kawai in kwana a nan in yaso inga me zasu karu dashi tunda haka sukeso."

Kawa:
"kawa a'a ba'ayi hakaba tashi muje kiyi hakuri bakomai kar ki damu."  kawa ta lallasheta haka dai Ladidi ta hakura ta tashi suka tafi.

 Sani kuma ya hango mutane haka daga nesa cikin duhu, sai yai batan basira kuma yaki karasa wa gun yana magana shi kadai. yace:

Sani:
 "oh ko su waye wa 'yan chan haka aduhu,kai bari na koma. tunda ido na ganin idoma an kasa ganin Ladidi  bare kuma a wannan  duhu bari dai sai da safe.   yanzu bari zuwa da safe na cigaba, bari in tafi gida." Ashe yayi batan baka tantan abin da yadade yana nema ne amma  yaki karasawa, kuma gata amma batan basira yaki karasawagun ,yajuya abinsa ya tafi.

             
Sani ga Ladidi a tsaye
   Sani da Ladidi 


    Bayan kwana biyu,  Sani dai yataho  neman gidan su Ladidi kamar yadda ya saba.  Ya isa wani gida ya duba wani gida da aka yimasa kwatance ya buga kofa yayi sallama sai  iske wani mutum ya yafito daga gidan.

 yace: masa 
"nan ba wata Ladidi Shi haya yake agidan saboda haka ya ware yabar gun",

 da yatafi sai ya biyoshi da Tabarya suka fafata Sani yayi galaba a kansa, ashe Dogon ne yasashi a gidan da nufin duk wanda   yazo neman Ladidi ya farmasa. to sun gamu da me karfi ,su hakura ko kuma suyi ta Shan mazga.

 Bayan ya doke wannan dan haya na karya sai aka bugo waya kir tai kara aiko sai Sani ya dauka yayi magana ashe dogone ya bugo da yaji ko ansamu nasara sai yaji ba maganar dan hayabace yasaki baki yana mamaki.

 Magatakarda yace:

 "ya akai ne ko yagama dashi."


Dogo yace"

 "inah ai Sanin nan karfi ne dashi ai ya make dan hayarnan abin ba sa'a."

 Gaskiya Sani yayi kokari wajen son taimakawa Ladidi bisa nasihar mahaifinsa shi Isa yake fadi tashin ganin ya lalubo Ladidi don yasan inda take ya cigaba da taimakawa Ladidi to amma hakan ya ci tura saboda tsoron su Dogo da'ake a garin shi isa ake cewa dashi ba'a santaba amma dai haka yadage sai yaga abinda ya turewa buzu nadi bazai gajiba muna fata  allah ya Bashi sa'a amin summa amin.

Muna.ita kuma kanwar Sani  tana yimasa tsiya cewa wai  son Ladidi yake shi kuma yanacewa da ita ba soyayyace a tsakaninsuba, 

Sani:
"kawai dai tai makone bisa kuma da biyayya ga Baba shi isa nake ta fadi tashin ganin na temakamata  ke kuma kina ganin wai santa  ni kuma ina nuna moki ba hakaba."


 kanwarsa tace:
 "to naji shi kenan muje a haka tunda kaki yarda.Allah ya temaka yabada sa'a ya shige gabah." 

 Sani yace: "haka yakamta kiyi ba ki, ta tuhumata da abinda bashikenanba." Itadai sai dariya take masa tana ganin fai kawai maganace yake, lallai akwai wani abu a tsakani.

 Ladidi tayi rashin ma haifiyar ta bayan ta rasa mahaifinta 
tashiga wani irin yanayi na gaba kura baya siyaki, tarasa wandanzai rungumeta hannu biyu ya share mata hawaye. 
Innace kadai take kokarin kula da ita to amma ita inna Malam Idi ya hanata saboda masifarsa kuma gashi suna gida guda.

Godiya ta musamman ga masoya wannan tasha tamu mai farinjini wato nishadisport mungode naku Sadik Yusuf.

     Daga SADIKYUSUF. 

  Za'a iya tun tubarmu ta imel namu kamar haka  sadiku854@gmail.com. 
 http//: nishadisport.blogspot.com

Comments

Post a Comment