An tarewa Sani hanya
GABATARWA
Salamu alaikum waraha matullahi ta'ala Wabaraka tuhu, masoya wannan Shiri namu wato Yar Malam, aci gaba da kawo muku sharhin wannan shiri naku mai farinjini.
Daga bakin Sadik Yusuf, kobiyomu mun gode!.
Sani yana neman gidan su Ladidi:
An tarewa Sani hanya a kokarinsa na neman gidan su Ladidi, yaran Dogo sukai masa kwantan bauna, suka rutsa shi. A wani lungu dake cikin unguwarsu.
Shikuwa ya zulle ya ruga da gudu suka bishi ya samu ya labe, ya ringa yimusu dauki dai-dai, a hikimance yana labewa yana bugesu wani ya hau bishiya in ya karaso gun ya dauke shi yai sama dashi ya sako,
Su duka guda udu sai da yayi musu duka, ya samu ya gudu sukuma su ka koma da borin kunya.
Suka nufi gun uban gidansu gurgu. Ya gansu suna tafe ba karsashi, sai gurgu ya tambayesu ya akai? Sukace: "Ai mutuminnan karfi ne dashi, yayimana dukan tsiya ya gudu.
Gurgu ya daka musu tsawa yai fada yai tagagi, ya barsu a nan suma sukai gaba.
● Baiga Gidanba:
Sani ya isa gida gun iyayensa suka tambayeshi ko yaga gidansu Ladidi?.
Sani yace:
"Banga gidanba, kuma a hanyata ta zuwa neman gidan su Ladidi, aka zuba Yara marasa kunya suka taremin hanya, wai sai sun nakasani"
Malam yace:
"Kai naji ikon Allah, to ya Kai dasu."
Sani yace:
"Hikima nayi ina binsu ina mammakewa, daya bayan daya na samu na sulale na gudu suka rasa inda nayi."
Malam yace:
"Kayi min daidai haka akeso, gobe ma sa kara"
Innna tace:
"Ah!, Malam karfa anakasa min yaro" Malam yace "a'a ba kina masa addu'a ba, ba abinda zai sameshi."
Sani yace:
"Ai! Innah bakomai ai indai daku, ba wata matsala kamar yadda Baba yafada, tunda kuna yimana addu'a ba abin da zai faru,"
Ita dai kanwar Sani bata ce komaiba, ta zuba wa sarautar Allah. Sai Sani yace da ita ta kawomasa ruwa, nan ta tashi ta dakko masa ruwan ya karba ya sha.
● Kakkarfane:
Sani yanaji da karfi domin su Dogo da yaransa, sun rasa yanda zasuyi dashi domin yafi karfinsu kullum basa samun nasara a kansa.
Amma duk dahaka Basu hakuraba, in sun hadu sai sun kawomasa hari, shi Kuma baya gajiya sai yayimusu duka domin shi yayi atisaye na koyon Chaskale,shi isa yake da karfi haka abin yake.
Ga wanda duk ya dage yakoyi yanda zai kare kansa, daga mahara in dai ba wani tsautsayiba to samun galaba kan mutum yana da wuya, domin anasamun dabaru kala-kala na kariya da yanda zakai duka domin shi kansa dukan in baka iyaba sai kaji ciwo a yayin da ka kaishi, shi isa ake son a koya.
Wannan shawarace ga mutane su daure su koyi yanda zasu kare kansu, domin yanzu al'amuran sun chanza kullu a cikin barazana muke ga barayi da yan daba da yan kwacen waya ,Allah ya kyauta
Shi Malam yayi amanna da Allah cewa indai mutum ya mikamasa komai to ba zai tabeba, bugu da Kari kuma ga addu'ar iyaye itama tana tasiri akan 'ya'ya saboda haka iyaye su dage da yiwa 'ya'yansu addu'a ba zagiba, da bakaken maganganu. Shi ne abinda yafi dacewa.
SU DOGO BA NASARA
Abinduniya ya damu su Dogo, duk inda suka bullo sai suga ba mafita,to shawara Dogo kawai ku hakura da ikon Allah. Domin Allah yafi karfin wasa, itadai Ladidi ta dace da samun Sani, ba ta wata fargaba in zata fita da tayi addu'a sai kaga tasamu .
MAHAUKACI DA KAWA
Rannan suna tare da kawa sai sukayi kcibis da Mahaukaci, nan da nan ya tunkarosu sukai kamar zasu gudu.
Sai suka tsaya sukace dashi: "in anbi rabbana?"
Mahaukaci sai yace:
"Ba wahala tawa" sai ya kece da dariya, su kuma sukai gaba ,haka dai mahaukci ya gamu da wani bawan Allah daman shi duk wanda yagani sai ya kama tambayarsa cewa ina budurwata.
In kabashi amsa ka tsira, in kace bakasani ba yo kashin ka ya bushe, domin kuwa zaka sha sanda don jibgarka zai tayi kamar yasamu Jaki.
Haka kuwa wannan bawan Allah yace bai saniba, aiko yace dawa Allah ya hadani ,yai ta dukansa yana ihu da kyar yasamu ya gudu suka zuba mahaukaci ya bishi suna gudu.
Saiga dodon mahaukaci wato sani yabiyo hanya kamar yadda yasaba sukai arba da mahaukaci, mahaukaci yana ganin Sani, sai ya juya da gudu yabi wata hanya kaji ta inda wannan bawan Allah ya samu ya sulale, shiko sani ba abinda yake sai dariya yatafi abinsa.
● Dogo da Magatakarda suna shawarar yadda zasu tinkari Sani.
Dogo yace:
"Kai wai yazamu bullowa wannan takadirin mutiminne?" Yai zugum yana saurarensa.
Magatakarda yace:
"Ai nima tinanin da nake kenan, abin ya shige min duhu. To amma akwai yadda zamiyi dashi,shi din banza waye shi, kuma meye shi, munefa."
Dogo:
to yazamuyi? Kadubafa irin wannan karti namu da suka zo daga birni, kaduba yanda yai fata-fata dasu." Magatakarda yai dariya yace:
"yanzu muyima wa dannan yaran barazana, su kara kaimi wajen tunkarar sa, su dage sukara azama suyi maganinsa tunda don haka muka kawosu in bahakaba mu aunasu su koma inda suka futo."
Dogo ya jinjina sai yace:
"Hakane kuma muyi musu tayin kudi masu tsoka, ko sa samu karfi a jikinsu." Eh! Hakane inji Magatakarda.
● Ladidi tanajin tsoro.
Ita kuma Ladidi tana fida a cikin jin tsoron, ko yaran Dogo sun yi galaba akan Sani, batasan tuni ya korasuba tana ta yin addu'a akan Allah ya kareshi saboda tana ganin a da lilinta zai shiga matsala, wadda bata shafe Shiba.
Domin su Dogo sun kawo masu basu kariya daga birni. kuma tana ganin suna da karfi. Amma batasan Sani yafisu karfiba.
Allah ya sawaka.
● Ladidi zata debo ruwa:
Wataran Ladidi zata debo ruwa kamar yadda ta saba, ta fito kenan sai taga su Dogo da Magatakarda da yaransu sunyi san -sani a waje, tazo zata wuce, Dogo ya daka mata tsawa yace ina wankin da yasata.
Sai a kunnen wani bawan Allah ya tinkaro wajen nan fa ya tsai dasu dayimata wulakanci yace:
"Lallai baku da mutunci yanzu marainiyar Allah kukewa haka ko tsoron Allah ba kwaji." Suka zuba masa ido ita kuma Ladidi ta rasa ina zata.
Sai Dogo yace;
"kai kuma, a suwa kake mana wannan fada haka."
Bashir yace:
"Ni a wanda Malam Nomau ya temaka a rayuwarsa, shi yaban taimako naje Birnh na samu ilimi."
Magatakarda yazuba masa harara,, dogo yace: "amma a banza. Ke Ladidi zo ki wuce ki debo mana ruwa.
sShi uma ya hana Ladidi fita, yace ta koma cikin gida, Ladidi ta koma.
Yaran dogo suka taso masa, Dogo yace su kyaleshi, suka barshi ya tafi.
Shi kuma Magatakarda yake ihu bayan hari, yake nasa fadan bayan Bashir ya tafi sai yace:
"lallai wannan mutimin ya raina mana hankali, shi kuma waye, bsi sanmu ba kenan, lallai zai gane shayi ruwane, damu yake zancen."
๐ KAMMALAWA
Muna godiya kucigaba da bamu hadin kai, ku masu kallo da karatu muna nan a hade. A cigaba da binmu a blog namu wato nishadisport.
ILMANTARWA
* Hakadai su Magatakarda suke ta neman yanda zasu halaka Ladidi, hakan ba dai-dai bane masu jinmu,dafatan kun fadaka. Halin su dogo ba dadi.
* Mu hadu a YouTube channel dinmu nishadisport.
Daga SADIKYUSUF.
Mun Gode! A tuntubemu a imel
kamar haka. Sadiku854@gmail.com.
http//: nishadisport.blogspot.com
Comments
Post a Comment