SADIK YUSUF

Gabatarwa daga Sadik Yusuf Garba

Ni sunana Sadik Yusuf Garba, an haife ni a unguwar Jakara, Tudun Makera, dake cikin birnin Kano, a karamar hukumar Dala, a shekara ta 1974. Na fara karatuna da karatun Alkur’ani mai girma, sannan na ci gaba da karatun Islamiyya. Haka kuma na yi karatun boko daga matakin firamare har zuwa sakandire.

Na yi aure ina da shekara 25 a lokacin, yanzu kuma ina zaune a gidana tare da iyalina. Ina da ’ya’ya hudu — uku maza da mace daya.

Harkokina na Yanzu

Ina zaune a unguwar Goron Dutse kusa da hanyar gidan gyaran hali (prison) dake kusa da hanyar Kansakali. A nan ne nake gudanar da harkokin kasuwanci, musamman:

Sayar da bakin mai

Sayen duro da yamti

Sayar da man mota da sauran mayuka daga kamfanonin cikin gida da na kasashen waje


Harkokin Lafiya da Wasanni

Na dade ina cikin harkar motsa jiki, musamman wasan kareti, inda na kai matakin bakar damara (black belt). Har ila yau muna gudanar da horaswa da tsalle-tsalle a Goron Dutse Sport Center, dake hanyar Jakara.

Harkar Fina-finai da YouTube

Mun fara shiga harkar fina-finan Hausa fiye da shekara 25 da suka wuce. A wannan lokacin muna:

Shirya fina-finai

Kaiwa kasuwa

Taka rawa a bangaren motsa jiki a fim


A yanzu kuma muna da shiri mai dogon zango da muke gudanarwa a tashar YouTube mai suna NishadiSport, kuma sunan shirin shine "Yar Malam".

Har ila yau muna halartar sauran fina-finai inda ake gayyatar mu don taka rawa ta motsa jiki da atisaye.


Tuntuba

🖥️ Blog: http://nishadisport.blogspot.com
📧 Imel: sadiku854@gmail.com







Comments