Maman Ladidi ta mutu
Yar Malam – Cigaba da Shirin NishadiSport Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu Masoya da mabiyan shafinmu mai farin jini wato NishadiSport , barkanmu da sake saduwa a cikin sabon cigaba na shirin Yar Malam . A yau, zamu kalli abubuwan da suka faru a tsakanin Ladidi , Mama , da kuma Dogo da abokan sa . Ku biyo mu. Mama Ta Kamu da Zazzabi – Ta Yi Nasiha Kafin Ta Rasu Mama tana fama da rashin lafiya sosai. Jikinta yayi zafi, tana kyarma, sai ta kama yi wa Ladidi nasiha da kuka, tana cewa: “Ladidi ki ji tsoron Allah, ki rike addininki, ki guji bin shaidan da rudin zamani kuma ki kula da addininki, ki rike bawan Allahan nan fa yatemakeki.” ita fai Ladidi tana kallon ikon Allah nan da nan sai hawaye ya cika mata ido. Ladidi ta katse ta, tace: “Mama ki daina irin wannan maganar. Domin kina fitgitani. Haka Baba ma yana yimin irin wannan nasiha sai kawai na ga ya mutu. Don Allah Mama ki daina!” Mama ta kalli Ladidi, ta ce: “Ba komai. Bawani abu ba...