π₯ Fada Ya Kaure Tsakanin Soja da Malam Idi! | Yar Malam
Assalamu alaikum jama'a! Muna maraba da ku zuwa wani sabon bangare na shirin Yar Malam, wanda ke cigaba da kayatar da masu kallo a tashar NishadiSport,dake youtube.
⚔️ Rikici Tsakanin Soja da Malam Idi
Wani tashin hankali ya barke tsakanin Soja da Malam Idi. Sojan na tafiya a hanyarsa sai yaji kamar ana binsa a baya. A firgice, ya ruga da gudu. Yana gudu yana yar da wayarsa ta hannu Da ya juya baiga kowa sai ya tsaya.
sai yacigaba da tagiya a hanya kuma sai kawai ya ci karo da Malam Idi. A cikin fushi da zargi, Soja yai charaf ya shake Malam Idi yana masa kashedin cewa meyasa yake binsa a zaton shine ke bibiyarsa!
Malam Idi cikin kuka da kokari yace:
"To me na maka da zaka shake ni,kana nema ka kasheni kashe ni"
Soja yace:
"Wato kai ne kake kokarin kashe ni ko? Bari ni na fara kaika kafin kai Ka kaini!"
Da kyar dai ya sakeshi, ya bashi kashedi mai zafi. Malam Idi na murza wuya da kyar ya tashi, ya dauki sandarsa, ya fice daga wajen cikin kunci da takaici.
Anan ne rikicin dake tsakaninsu ya sake yin zafi — rikici ne akan dukiyar marayu, kowa na kokarin danne dan uwansa.
Tsakanin Soja da Malam Idi haka suka ci gaba da zargin juna suna neman kashe kansu a aikin banza akan abin da bana suba.
Soja da Malam Idi
π¨π¦ Soja Ya Bayyana Gaskiya Ga Dansa Gurgu (Munzali)
Soja ya kira dansa Munzali (wanda ake kira Gurgu), ya sanar masa da abinda ya faru.idi yana turomasa yara don su hallakashi. Munzali cikin fushi ya tafi gonar da su Dogo suke aiki domin yayi musu kashedi.
Su Dogo suka ce:
"Kai Gurgu wallahi bazata sabuba domin ya kusa kashe min ma haifi,Uba bai fi uba ba! Idan ubanka yayi laifi, ba zai hana mu kare kanmu ba."
Munzali yace:
"Yo kuyi duk abinda zakuyi ,ku kiyayi kanku wallahi na isheku Shegu! Ku zuba mu gani. Banda butulci irin naku ace ni zaku juyawa baya kun manta da duk taimakon da na baku to muje zuwa ni zanyi maganinku."
Ya tafi abinsa cikin fushi.
Dogo ya kara da cewa:
"Soja ya kusa kashe mahaifina akan zargi mara tushe — wai saboda yaji kamar ana binsa."
Munzali ya gargadi kowa ya kama gabansa, ya ce zai tona asirin zaluncinsu da yadda suke cutar Ladidi. Shi kuwa Magatakarda yana ta basu hakuri amma babu wanda yasaurarae shi.
π Rikicin Soyayya da Yaki Akan Dukiya
Lamarin dai ya nuna cewa:
- Gurgu na son Ladidi,
- Su Dogo kuma suna so su allaka Sani,
- Amma baban Gurgu da baban Dogo suna rigima — su ne suka janyo rikicin cikin gida.
Duniya kenan! Watarana ana dariya, watarana ana hawaye. Tsoffin abokai sun koma abokan gaba saboda son zuciya da zalunci. A haka rikicin ya kaure, kowa na kokarin ganin ya fi dan uwansa.
Ita kuma Ladidi tana fama da rashin kwanciyar hankali a gidan Malam Idi domin kuwa ya hana ta sakat bata da wata walwala sai inta gita gun kawarta anan ne take dan samun nutsuwa.
ladidi tana sallahπ€²
Ku cigaba da kallon wannan kayataccen shiri Yar Malam a tashar NishadiSport. Akwai nishadi, akwai dariya, akwai wa’azi — shiri ne na musamman!
π️ Kada ku manta ku:
- Subscribe
- Danna kararrawa
- Yin like da sharing
- Barin sharhi ko bada shawara
Wanda ya rubuta: Sadikyusuf
π http://nishadisport.blogspot.com
π§ Sadiku854@gmail.com
Nagode
ReplyDelete