Posts

GORIBA- PALM TREE

Image
    Gabatarwa   Salamu alaikum masoya wannan dandali namu da muke antayo muku labarai da al'adu, da kuma sharhi fina-finai , da al'amuran yau da kullum. Muna muku fatan alheri, naku Sadik Yusuf. Menene bishiyar Goriba Bishiyar Goriba, wata bishiyace mai tsayi, wadda tayi kama da bishiyar Dabino, da kuma bishiyar Giginya. Ana sarrafa gayenta ta wasu fannoni daban-daban. Kamar irinsu. 1 Tabarma 2 Rufin daki. 3 Mafici. 5 Fai-fai, da ake rufe abubuwa dashi a gar gajiyance. Wannan bishiya tafi rayuwa a gurare masu zafi, kamr a arewacin Nigeria, da kuma wasu sassa na kasar Africa. Ana cin 'ya 'yanta, in an tsunko su Ana kawosu kasuwa buhu-buhu Ana neman kudi da ita. Ana yin garita asa a fakage a rika sayarwa, har shayi anayi daita.             Bishiyar Goriba  ● kadan daga abinda akeyi da ita.  * Ana yin kwando, domin zuba kaya ko zuba wasu abubuwa na gargajiya wanda ba'a so sulalace, kamar danbun nama. * Sai shayi mutane suna...

ZOGALE- MORINGA

Image
GABATARWA Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa daku masu bibiyar wannan shafi namu na blogs, munai muku fatan alheri. Nine naku Sadik Yusuf nake gabatar muku da wannan bayani. A yau zamu tattauna don gane da bishiyar zogale wadda take an fani ga lafiyar Dan Adam wato  " Tree life " Anfanin zogale ga lafiyar Dan Adam Zogale wata bishiyace  mai daraja, kuma bata da girman itace, wanda ke bawa mutum gudummawa ga lafiyarsa. Haka kuma ana neman kudi dashi, a sassa daban-daban na duniya. Ana yin miya da ganyen zogale, kamar miyar tuwo , miyar shinkafa , miyar kuka , da sauransu. Har abin sha anayi dashi, kamar yin shayi. Hatta sassakensa ba'a barshi a bayaba, da saiwarsa . Duka ana anfani da su fomin yin magani. Ruwan zogale yana taimakawa fata tayi laushi da kuma tsaftace jiki daga ciki. Ana wanke gashi da shi don yayi laushi da tsawo. Ruwan zogale yana temakawa mata masu shayarwa. Saboda iorn dake dauke dashi. Shansa da safe kafin karin kumallo, yana temakawa jiki,wajen...

DUKAN DUHU- KASHI NA 3

  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna ( nishadisport). Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!. Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3  SALE DAURE A WANI KANGO  Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit. Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba. Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace: Alhaji:  "Malam Salele mai liki,  yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soya...

DUKAN DUHU KASHI NA 2

DUKAN DUHU KASHI NA BIYU  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, wanda muke kawomuku dadadan labarai masu cike da darasi, waɗanda suke taba zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum. Zamu ci gaba da kawo muku cigaban labarin "DUKAN DUHU KASHI NA BIYU" . Sai ku biyo mu a hankali don jin yadda zata kaya. Ni ne naku Sadik Yusuf , na gode! SAILUBA TAJE WAJEN KAWARTA NEMAN SHAWARA Sailuba tana ba kawarta labarin yadda sukai da Alhaji. Ita dai Halima ta tsaya tana sauraronta, tayi zugum da ido. Halima tace: "Nidai abinda zan gayamiki Sailuba, ki nutsu ki tsaya wajen talakanki, domin shi yafi dacewa da ke. Kar ki jifan gafiyar baidu." Sailuba ta harareta cikin mamaki, tace: "Yau kuma kece mai fadin haka? Ke da nake zato zaki maramin baya, amma sai naji wata banzar magana ta futo daga gareki haka." Halima ta kara cewa: "To ai gaskiya ne. Abinda yasa kika ga ina kin sale, saboda naga ba’a sa muku rana ba, kuma ba’a yi baikon ba. Tu...

A CHUCI MATA kashi na biyu

Image
    GABATARWA  Salamu alaikum masoya wannan dandali namu wato nishadisport. Muke muku barka da wannan lokaci zamu cigaba da kawomuku labarin "A chuchi Mata" kashi na biyu, wanda yake kirkirarren labarine ba da kowa akeba. Da fatan za ku biyomu kuga yanda zata kaya.                               Hoton faster Achuci mata  FATIMA NA BA UMMAN TA LABARI TSAKANINTA DA SAURAYINTA  Fatima ta isa gida ta shaidawa babarta abinda ya gudana tsakanin ta da saurayin da ta yiwa tsiya, tqi watsi da shi.  umman tata tace: "Ai haka yafi, yaje ya karata matsiyaci kawai." Suka tafa da maman tata suna shewa.   Boss yazo gun Fatima Boss me badda kama, yazo ya tabbatar wa da Fati cewa auranta  zaiyi, ta amince dashi, sukai sallama ya tafi, itama ta shiga gida ta gayawa ummanta yanda sukai. Fati tace: "wannan mutumin da yazo wai cewa yayi zai aureni".sai  Umman tata:tace " haka yace?....

A chuci Mata-kashi na 1

Image
    Salamu alaikum masoya wannan dandali namu naku mai farinjini wanda kuke son ji da gani da karatu ku biyomu a NishadiSport – A Chuci Mata (Kashi Na Daya) Rubutawa: Sadik Yusuf         Gabatarwa  Assalamu alaikum masu bibiyar tashar NishadiSport, ni ne naku Sadik Yusuf. Muna kawo muku dadadan labarai, da fatan kuna jin dadin shirye-shiryenmu. wannan labari na "Achuci Mata" kirkirarren labarine anyishi ne badan waniba ko kuma wata , kawai dai labarine,kada wani yaga wani abu da yai kama da halinsa ya zaci dashi muke mun gode!.🙏 * RIGIMA BOSS DA ISAH A wani gari, akwai wasu abokai suna rigima akan wani bashi da Isah yake bin abokinsa mai suna Boss. Isah ya rike wuyan Boss suna kokawa yana cewa sai an biyashi kudinsa da ya kai shekara guda ba'a biyaba.  Suka cukume suna kokawa a tsakaninsu titi-titi   Boss ya samu sa’a ya daga Isah ya bugashi da kasa har ya ji masa rauni, sannan ya gudu ya barshi a nan yana murkususu. Da kyar Isah y...

Rikicin daba a kano

     GABATARWA Rikicin ‘Yan Daba a Kano, a ga ya za'a kamo bakin zaran.Daga Sadik Yusuf, Kano Nigeria Zami duba da wannan matsala da kuma wasu al'amura na yau da kullum. Dafatan za'a kasance damu. Daga Sadik Yusuf – Kano, Nigeria Tuntuba: sadiku854@gmail.com Shafinmu: nishadisport.blogspot.com Abin Da Ke Faruwa a Kano Ya kamata mu fuskanci abinda ke faruwa mu fadawa kanmu gaskiya, game da matsalar da ke addabar jihar Kano – wato rikicin 'yan daba.  Wannan matsala da take nema ta gagari Kundila  ta shafi unguwanni da dama a jihar ta kano , kamar irinsu  Dorayi, Sheka, Dala, Zage, Kofar Mata  s harada, ja'in da kuma kurnar Asabe  da dai sauran su. A bin yazama kamar annoba.Yara da basu kai shekaru 15 zuwa 18 ba suna haduwa suyi gungu suna fada a da makamai a  tsakaninsu,  suna kai hare-hare a inda suke so.  Suna amfani da makamai masu hadari irin su adda, barandami, fafalo , da kuma kayan maye da suke shaye-shaye. Sau da dama. ...