Salamu alaikum masoya wannan dandali namu wato nishadisport.
Muke muku barka da wannan lokaci zamu cigaba da kawomuku labarin "A chuchi Mata" kashi na biyu
Hoton faster Achuci mata
ku biyomu kuga yanda zata kaya.
Fatima ta isa gida ta shaidawa babarta abinda ya gudana
tsakanin ta da Boss me badda kama ,tace:
"wannan mutumin da yazo wai cewa yayi zai aureni".sai
Umman tata:tace
" haka yace".?
Fatima tace:
"eh! Haka yace"
Umman tata tace:
"to in da gaske auren zaiyi me zai hana ki amince? tunda naga yana da kudi. Daman mu wanda zakije gidansa kihuta ai shi muke nema,ga shi kuma Allah ya kawo don haka me ake jira"
Fati tayi ajiyar zuciya ta girgiza kai:
"hakane Umma nima naga ya hadu to yazamiyi da Habu?"
Umma tace:
"ke rabu dashi kudinsa zamu mayar masa da yan komatsan da ya kawo bashi kenan ba wani abune"
Fati tace:
"to Umma naji zan dan yi tunani, don shimafa ina sonsa.
Gashi abin tausayi kuma har yagama gininsa biki ake jira."
Fatima, Taje wajen kawarta neman shawara ta gayamata abinda ake viki:
Fati tace:
"wani lamarine yake tafe dani."
sadiya, tace:
"meke tafe dake? ina jinki."
Fati tace:
"wani babban mai kudine yazo guna wai zai aureni. kuma kinsan saura sati daya a daura aurena da Habu shi isa nazo gareki."
sai kawar tata tayi dariya. Kana tace:
"to meye, wani abune? bakanki farauba ba kuma ba akanki za'a denaba, kawai kimanta da wannan Habu din ki kama mai kudin tunda yace da gaske yake." Fati ta kalleta.
Fati tace:
"To bakomai domin Umma ma haka ta zaba."
Sadiya tace:
"to kingani. Haka ai shi yafi, ki manta dashi yaje yakarata ya nemi wata wadda ta dace dashi."
HABU YAZO GUN FATIMA
Habu yazo da zummar aje aga gida, kamar yadda ya nema.
Yasa waya yakirata. Amma shiru bata futoba sai da tagama batamasa lokaci tukuna sannan tazo tana sanda alamar akwai wani abu atare da i'ta.
ya zuba mata ido domin ba haka yasaba ganintaba lallai yau da matsala.
Habu ya tambayeta, tun kafin su gaisa,yau lafiya kuwa? naganki kamar wadda kwai yafashewa aciki,
Fati tai masa wani kallo she-keke:
"Lafiyar kenan ni kalau nake ba abinda yake damuna tana magana ta yamutsa fuska." Yace:
"To nazone muje in nuna muku gidan domin, kusan abinda zakuyi na aune-aune."
"Me zamuyi injita. Kaga ni bazan zauna a wannan akurkin gidan nakaba. Kaga zancen gaskiya.
Ninyanzu nafi karfinka, domin baka zuwa Dubai, bare Chana."
" Me nake ji kamar a mafarki? wai kece kuwa? ko dai."
Ta tari ninfashinsa, "nice dai wadda kasani Fati." Yana mata kallon mamaki.
Sai ga Boss ya iso a wata arniyar mota. Tana numfashi, ai ko tana ganinsa sai ta bar wajen Habu ta isa gun Boss, ta Bude kofa ta shiga ta barhi nan yana zabga uban gumi.
yarasa me kemasa dadi haka ya daure dai yabar gun kafa funsa ba nauyi.
Sukuma suka cigaba da hirarsu suna shewa.
Anbiyo Habu da gudu yana gudu anabinsa.
Ashe wannan mugun Boss din! nanne ya sa aka biyoshi yana gudu har suka cimmasa ya fadi kasa suka rufar masa da duka.
Sai ga wan Fati nan ya hango ana bugun wani mutun.Nan da nan ya karaso gurin sai yaga ashe saurayin kanwarsane ake duka nan ya shiga ya temakamasa suka samu suka kama daya daga cikin wanda suke dukan. suka tambaye shi.
"Waye ya turosu."
Yana nishi Yace:
" Boss ne ya turomu."
Sukace:
"Boss. inji wan Fati."
Yaro yace:
"Kwarai kuwa."
Sukace"
"To muje muji dalili."
Isar su ke da wuya, sai ga saurayin karya na Fatima.
Yayan yace:
"To wannan shine Boss?.
Yaro yace. Eh! Boss ya zaro ido a firgice:
Sai Boss yayi farat. "Yace kai me ke faruwane ni ban ganeba?."
Yaro yace:
"Ah, ba kaine ka turamuba? kace mu kakkarya wannan."
Ya nuna Sale:
Boss yace:
"Kai bana son rashin mutunci. Ni yaushe nazo garin da zaka ce ka sanni har kuma na turaka ka karya wani? mutimin banza kubani shi nakaishi ga ja mi'an 'Yan Sanda"
Suka bashi shi ya samu yayi yan dabaru ya sulale .
Boss yace:
"To kai ai saika to nan asiri. shi isa na fututtuke,amma kayi hakuri da abinda nayi"
Yaro yace:
"Haba oga. Ai bakomai na fahimta."
Ya yan Fati yana fada a cikin gida.yace
"Ga irin abinda ake gudu.kunga wannan mutumin da kuka tsunto.Gashi har yasa ayiwa Sale rauni.
Duka wai don yana san Fati. Al hali shi yatarar don samun gari."
Ana haka sai suka ji sallama a waje sai shi ya yanta ya leka sai yaga mai sa Labulene tsaye da guduma a hannu:
Sale yace:
"Mai yafaru kaida muke tsammanin kana gun sa labule"
Me sa Labule yace:
"Ai naje domin yin aiki, kuma sai naga ana loda kayan amarya awata mota. Kuma an kulle gidan"
Sale yazaro ido. To mai yafaru ,ya koma cikin gida da gudu, suna ganinsa da gudu hankalinsu ya tashi:
"yaya meke faruwa,inji uwar tasu. "
Dale yace:
"Wato wai mai sa labulene yaje domin aiki sai yaga ana loda kayan Fati a mota. kuma gidan an kulleshi."
Uwar tace:
"Mai kake jira maza garzaya kaga abinda ke faruwa."
nan da nan yafita dagudu isarsa ke da wuya sai yaga an chakume Boss ana kokawa sai ya biya kudin kayan da ya haya,nan yakara sauri kan ya iso Boss ya samu yabige wanchan mutimin ya hau mota ya tsere.
Nan fa yayan Fati yabishi da kyar ya kamashi yayi masa duka sai gun 'Yan Sanda.
Lallai wannan shine "Achuci Mata"!
Haka kawai tana zaune da masoyinta lafiya, an kusa biki amma tabi rudin shedan.saboda batan basira da toshewar basira wai ita taga Mota da babbar Riga.
Haka abin yake faruwa ga duk wanda bai tsaaya a kan gaskiyaba, to kuwa zai kare a nadama, domin ita Fati tayi biyu babu ba tsohon saurayi ba sabo.
Don shi tuni yayi wani gun yayi aurensa yana cikin jjn dadi da kwanciyar hankali.
Nan muka kawo karshen wannan labari mungode sai anjima.
Naku Sadik Yusuf
Don tambaya da karin bayani sai a tuntubemu ta imel: sadiku854@gmail.com
Na Gode!
Comments
Post a Comment