A chuci Mata

   Salamu alaikum masoya wannan dandali namu naku mai farinjini wanda kuke son ji da gani da karatu ku biyomu a

NishadiSport – A Chuci Mata (Kashi Na Daya)

Rubutawa: Sadik Yusuf

Assalamu alaikum masu bibiyar tashar NishadiSport, ni ne naku Sadik Yusuf. Muna kawo muku dadadan labarai, da fatan kuna jin dadin shirye-shiryenmu.


A wani gari, akwai wasu abokai suna rigima akan wani bashi da Isah yake bin abokinsa mai suna Boss. Isah ya rike wuyan Boss suna kokawa yana cewa sai an biyashi kudinsa da ya kai shekara guda.


 Boss ya samu sa’a ya daga Isah ya bugashi da kasa har ya ji masa rauni, sannan ya gudu ya barshi nan yana murkususu. Da kyar Isah ya mike, ya tafi gida yana dafe kai.

Boss ya fada wa abokinsa Musa abin da ya faru, sai Musa yace:

“Ahh Boss, baka kyauta ba. Yaya za’a yi mutum yana  binka bashi har shekara guda ka ki biyansa, kuma ka ji masa rauni. Wannan rashin imani ne.”

Boss ya ce:

“Kai tsiyata daman kai haka kake . Kullum sai ka ce za ka fada wa mutum gaskiya wai kai ga na na Allah.”

Musa ya amsa:

“Ni ba abinda zai hanani fadar gaskiya, komai dacin ta. Idan baka so gaskiya  ka daina zuwa gurina, sai dai ka daina — amma gaskiya sai na  fada.”

Boss ya ce:

“To shikenan, ka yi kar ka fasa. Ni kuma ba zan canza ba sai naga yadda zakayi.”

Sai ya tashi ya tafi ya bar Musa yana ban-bami.


A gida kuwa, Isah yana shigowa yana dafe kai sai kanwarsa Fati ta fito tana shirin zuwa kanti. Ta gan shi yana dingishi, ta tambaye shi abin da ya faru.

Isah yace:

“Wallahi Boss ne ya min wannan wulakancin akan bashi da nake binsa bashin kuma har na tsawon shekara guda.” tana kallon sa tana jimami. Sai,

Fati tace:

“Wannan mutumin fa mugune kainema kake zuwa gunsa yakamata ka chanza guri domin ba tsararka bane shi mutumin banzane.” yana fafe kai yana nishi.


Washe gari Boss da Musa suna zaune, sai Boss ya hango wata yarinya tana tafiya.

Boss ya ce:

“Kai Musa, haka wannan yarinyar ta zama!”

Musa ya ce:

“Wace yarinyar? Ai ba ka ganeta ba? Kanwar Isah ce!”

Boss ya ce:

“Wallahi ina sonta.”

Musa ya ce:

“To ka manta da komai da kayi musu kenan? Duk azabtarwar da kayi wa 'yan gidansu sata kwace”

Boss ya ce:

“Kai kawai ka goya min baya don na cimma burina.”

Musa ya ce:

“Ni gaskiya zan fada, wannan yarinya tafi karfinka don kai ba mutumin kirkine ba ko da kana so ko ba ka so sai na fada.” Boss yana kallonsa yayi kwafa, yatashi ya barshi.


A wani lokaci, wani yaro na kan hanya an turo shi da kudi, sai Boss ya tare shi ya kwace kudin. Yaron ya koma gida yana kuka, Fati ta tareshi shi. Ta tambayeshi waye?

Yaron yace:

“Wannan mugun mutumin nanne Boss na gurinchan shine ya kwace min kudi.”

Fati tace:

Wannan Boss din mara mutumci shine ya kwace mana kudin?.

Suka tafi wajen domin fati ta karbo kudin a wajen Boss din, amma Boss yana hango su dai yatashi ya bar gun ya  gudu ya ɓuya. Suka duba basu ganshiba suka koma.


Saurayin Fati ya zo wajen ta, suna hira. Ya shaida mata cewa ya gama gina gidansa kuma ya shirya da gaske don aure.

Fati tace:

“Insha Allah zan tsaya akan alkawari. Ba zan yaudare ka ba kar kaji komai nayi murna da jin wannan labari.”

Sai suka ci gaba da tattaunawa cikin farin ciki, sannan saurayin nata ya tafi.


Boss ya je ya aro kaya, ya gyara jikinsa, ya aro mota, ya je kofar gidan su Fati. Ya sha kamshi, yana takama da alamar alhaji.

Fati ta fito, bata ganeshi ba.

Boss yace:

“Ni baƙone daga Dubai, nagan kine ke kin kama zuciyata... Naga ina sonki."

fati tace: "to a ina kasanni? ina ka taba ganina?

Boss:

"ah! Bakece kika zo wucewa ta kusa da kantin chanba? Dake wani yaro ai anan na ganki." Ita dai tana kallon sa alamar kamar ta ganeshi shi kuma yana boyewa.

Fati tace:

“Ni ina da wanda zan aura cikin sati guda, don haka kayi hakuri kaga tafiyata.”

Ta barshi a wurin yana girgiza kai.


Ta shiga gida sai taba maman ta labarin yadda sukayi da wannan Boss din wai yana sonta sai maman tace:

"Waye kuma wannan a ina yake." Tana kallon Fati.

Fati:

"Wai cewa yayi bakone shi jiya yazo daga dubai domin kawo wasu kaya a kwantena." Maman tata tana jinjina lamarin. Sai ta tashi ta tafi ta cigaba da aikinta.

Boss yana ba abokinsa labari yanda sukai

Boss:

ai inatinanin yarinyar zata amince dani, ga yadda naga tana dan satar kallona ta gefen ido."shi dai abokin nasa yana jin labarin banza.

Abokin yace:

"kai ka faye rigima yanzu ya zakai randa akace ta ganeka?"

Boss yace:

"yo ba karamar kwakwalwa ce dasuba haka zan jasu basu ganeba." Ai zamuyi kallo nan gaba zamu ga yadda za ai" inji shi.


Nan ne muka kawo muku karshen kashi na daya na shirin A Chuci Mata. Ku kasance tare da mu don kashi na biyu.

Wanda ya rubuta: Sadik Yusuf
📧 Imel: sadiku854@gmail.com
📱 WhatsApp: 08148166212



 

Comments

Post a Comment