GORIBA- PALM TREE
Gabatarwa
Salamu alaikum masoya wannan dandali namu da muke antayo muku labarai da al'adu, da kuma sharhi fina-finai , da al'amuran yau da kullum. Muna muku fatan alheri, naku Sadik Yusuf.
Menene bishiyar Goriba
Bishiyar Goriba, wata bishiyace mai tsayi, wadda tayi kama da bishiyar Dabino, da kuma bishiyar Giginya. Ana sarrafa gayenta ta wasu fannoni daban-daban. Kamar irinsu.
1 Tabarma
2 Rufin daki.
3 Mafici.
5 Fai-fai, da ake rufe abubuwa dashi a gar gajiyance.
Wannan bishiya tafi rayuwa a gurare masu zafi, kamr a arewacin Nigeria, da kuma wasu sassa na kasar Africa.
Ana cin 'ya 'yanta, in an tsunko su Ana kawosu kasuwa buhu-buhu Ana neman kudi da ita. Ana yin garita asa a fakage a rika sayarwa, har shayi anayi daita.
Bishiyar Goriba
● kadan daga abinda akeyi da ita.
* Ana yin kwando, domin zuba kaya ko zuba wasu abubuwa na gargajiya wanda ba'a so sulalace, kamar danbun nama.
* Sai shayi mutane suna anfani da garinta, ko kuma a bareta daga kwallon asa a shayi.
* Ana anfani da itacenta wajen gina gida, kamar abinda ake kira azara, domin tsayin da itacen yake dashi.
* Anayin lemo da ita.
* Anayin rufin daki da ita, musamman a karkara.
* Ana samun mai a cikinta, har Ana girki dashi a wasu guraren. Har girki ana yi.
● Anfanin Goriba - Palm tree
Tana da anfani sosai a jikin lafiyar dan Adam ga kuma zaki idan Ana cin dan itacenta, tana da kamshi mai dadi, ana sarrafa ganyenta, wajen samun sauki daga mura ko zazzabi. A wasu guraren, ya danganta da yadda mutanen wajen suka dauka.
Kuma wani abin mamaki ana anfanida busashen ganyenta wajen korar kwari, da maganinsu.
Haka ana dan kona kwallonta ana sa shi a hanci don rage jiri a jikin mutum. Mutane da dama suna son Goriba musamman mata da yara a yankin mu na arewacin Nigeria.
Yana da kyau mutane surika cin goriba ko saying ta, don kar mu rasa abinda Allah ya kunsa a cikinta.
GA SINA DARAN DAKE CIKINTA
Tana dauke da wasu sinadarai da jikin mutum yake bukata don inganta lafiya, zamu dan hi bayani kadan daga cikinsu.
1 vitamin A, C, E
2 calcium
3 iorn
4 potassium
5 magnesium
6 fiber
7 Fatty acid. Ake sqmu a man Goriba
Wannan suna darai suna temakawa lafiyar Dan Adam sosai arika anfani da ita, da shawarar kwararru sa likitoci, don kaucewa matsala.
1 GA WASU DAGA CIKIN MAGANI DA TAKEYI
● Don samun sauki daga zawo. ( Ana fafa 'ya 'yanta da ruwa in ya huce asha.)
● Don maganin zazzabi da g!jiya. (Ana shan ruwanta in anjika.)
● Ana anfani da ita wajen kara karfin jiki, kamar (energy drink.)
2 GANYEN GORIBA
● Ana tafasa ganyen a tace a sha. Tana maganin kumburi ko ciwon ciki.
● Ciwon sanyi ko mura. Ana shakar turirinta bayan an tafasa.
3 SAIWAR BISHIYAR GORIBA
● Domin matsalar fitsari. Ana an fani da saiwarta in an tafasa a rika sha.
● Don ciwon Koda ko ciwon ciki. Ana anfani da tushendon rage ciwon.
Duk wanman bayani namu ba dolene yazama hakaba, sai dai arlka tambayar likita shi yafi dacewa.
'Ya 'yan Goriba joking bishiyar ta
KWALLON CIKINTA
Dan cikinta shima ba'a barshi a bayaba, domin ana fasawa ayi anfani dashi, swansong kima ayi makamashi dashhi. Ga kadan daga anfaninsa.
1 Ana anfani dashi wajen matsalar daji, da kuma kimbirin daji.
2 Sai matsalar ciwon Hakori, ana taunawa, ko anfani da ruwan, don samun sauki.
Duka wannan bayani namu ba lallene yazama hakaba, domin ya ban-banta daga mutum zuwa mutum, muna bada shawara a karo na biyu. Arika tun-tubar likita, don maganin gargajiya bazai maye na asibitiba.
Zamu tsallaka izuwa bayanin wani dan itace mai zaki.
FASA DABUR
Fasa dabur wani dan itacene mai zakin gaske kai kace zuma, kuma yana da kamshi sosai, dan itacen a dunkule yake, jikinsa kamar kwananniyar Fura.
Mutane suna sansa sosai , amma ba koina ake samun saba, ko kace gashi ana sayarwa a kasuwa, fan cikinta farine da kwallo baki, tana yin 'ya 'ya duk shekara.
Bishiyar Fasa Dabur
Tana da anfani ga lafiyar Dan Adam, saboda sina daran dake jikinta, gasu kamar haka.
1 vitamin C . Yana taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki.
Kuma yana temakawa fata wajen kareta daga saurin tsufa.
2 bitamin B6. Yana temakawa wajen inganta kwakwalwa, tayi aiki mai kyau, da karfafa jijiyoyin jiki.
3 Faibar. Yana hana kumbirin ciki, da saurin narkewar abinci. Yana rage kitse da sukari a jiki.
4 Calcium. Yana karfafa Hakora da Kashi. Suyi kwari.
5 Iorn. Yana samar da jinj mai kyau ga jikin dan Adam.
6 magnesium. Sarrafa zuciya, da hada tsokar jiki.
7 Potassium.yan sa jiki ya dai daita ruwa, da sinadarai.
8 Antioxidant. Suna kare jiki hana saurin tsufa da ciwon daji.
Saboda haka kaga wannan dan itace ba abin yarwa bane, duba da irin abubuwan da yake dauke dasu, na kare jiki daga cuta da kara sinadarai.
Nan muka kawo muku karshen wannan bayani na fasa dabur, da Bayanin Goriba. Don haka mutane mudena kallon irin wannan abubuwa a matsayin kayan yara, domin wani lokacin yafiwa manya anfani.
FASA DABUR
Naku sadik Yusuf domin kari bayani da yimana sharhi, sai a tuntubemu.
08148166212
Sadiku854@gmail.com
Nishadisport.blogspot.com
Mun gode
ReplyDeletedakyua
ReplyDelete