ZOGALE- MORINGA
GABATARWA
Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa daku masu bibiyar wannan shafi namu na blogs, munai muku fatan alheri. Nine naku Sadik Yusuf nake gabatar muku da wannan bayani.
A yau zamu tattauna don gane da bishiyar zogale wadda take an fani ga lafiyar Dan Adam wato "Tree life"
Anfanin zogale ga lafiyar Dan Adam
Zogale wata bishiyace mai daraja, kuma bata da girman itace, wanda ke bawa mutum gudummawa ga lafiyarsa. Haka kuma ana neman kudi dashi, a sassa daban-daban na duniya.
Ana yin miya da ganyen zogale, kamar miyar tuwo, miyar shinkafa, miyar kuka, da sauransu. Har abin sha anayi dashi, kamar yin shayi.
Hatta sassakensa ba'a barshi a bayaba, da saiwarsa. Duka ana anfani da su fomin yin magani.
Ruwan zogale yana taimakawa fata tayi laushi da kuma tsaftace jiki daga ciki.
Ana wanke gashi da shi don yayi laushi da tsawo.
Ruwan zogale yana temakawa mata masu shayarwa. Saboda iorn dake dauke dashi.
Shansa da safe kafin karin kumallo, yana temakawa jiki,wajen dai-daita suga yana kara insulin a jiki.
Kada mutum yasha ruwan zogale fiye da kofi daya a wuni, da kuma mace mai ciki, karta sha shi da yawa.
Bishiyar zogale
GA YADDA AKE HADA RUWAN ZOGALE
1 Ana samun ganyensa a gyara shi, a wanke.
2 A tafashi minti 5 zuwa minti 10
3 Abarshi ya huce sai arika sha kar ya wuce kofi 1 zuwa 2 a rana
4 Ana iya sa Zuma aciki, in ana bukata.
Sinadaran dake cikinsa
● Iorn - yana temakawa jiki samar da jini
● magnesium - yana bada lafiya ga kwakwalwa
● potassium - dai daita bugun zuciya da ruwan jiki
● zinc- don garkuawr jiki
● phosphorus- yana temakawa jiki gina kwayoyin halitta.
● vitamin A- Don inganci gani da fata
● vitamin B1 B2 B3 B6- suna taimkon jiki wajen sauri narkar da abinci, da sa kuzari.
● vitamin E- yana kare kwayoyin jiki daga lalacewa
● vitamin C - yana karfafa gar kuwar jiki
● calcium- don karfafa jiki da hakori
● protein- yana temakawa jiki wajen ginashi
● fat- haka zogale akwai mai a cikinsa
● carbohydrates- yana sa jikin mutum ya samu kuzari
Enzymes da amino acid
Zogale- moringa yana da sinadarin amino acid har guda goma sha takwas 18, suna temakawa wajen gina jiki da kuma lafiyar kwakwalwa, in fai mutum yana anfani dashi zai samu lafaiya sosai ta inda baya zato.
SARRAFAWA
● Ruwan zogale
Ruwan zogale ana shansa bayan andafashi, ruwan da ya rage bayan tsame ganyan sai a rika sha shima yana da anfani ga lafiya.
Yana rage kiba yana dawo da kuzari bayan mutum yayi aiki mai nauyi ko gajya bayan mutum ya tashi daga jinya.
Yana rage kumbirin ciki da rage ciwon ulcer, da hanji, ruwan zogale yana saurin narkar da abinci
Ana dafashi aci ganyensa haka aci ko kuma asa kuli aci musamman karkara, harma yana rage yunwa.
MAGANIN DA ZOGALE YAKEYEYI
1 rashin jini- iorn din dake cikinsa yana da yawa don haka yana karama jiki jini, sosai in mutum yana cin ganyensa ko shan ruwansa.
2 Yana rage hawan jini-(high blood pressure). potassium dake cikinsa, yana yin kamuwa da hawan jini, in mutum yana anfani dashi.
3 ciwon suga (diabetes) , zogale yana rage kamuwa da ciwon suga, in ana anfani da shi yana rage suga a jiki yana dai-daita insulin
4 Yana rage radadin ciwon kashi da kuma yawan gajiya, domin yana da calcium da yawa dakuma magnesium don karfafa kashi da sa kuzari.
5 ganyen zogale ko ruwansa, yana maganin chushewar ciki don yana saurin narkar da abinci. Kuma yana maganin ulcer.
6 Zogale yana sa fatar mutum tayi kyau tana sheki. Kuma yana sa gashi ya fito sosai.saboda yana da vitamin A da E. Kuma ana anfani da mansa wajen shafawa.
7 mata masu shayarwa.yana inganta lafiyarsu, da kuma kara ruwan Nono, da samar da lafiyar yara.
8 Rage kiba yana temakawa wajen rage kiba da kitse a jiki. Da fitar da guba.
GA WATA FA'IDA
Yadda ake anfani da garin zogale
1 Ana shanya ganyen zogale. Shanya ta zama ta inuwa, domin rana tana kashe wasu sinadaran dake jikinsa.
Ayi gari dashi don jikawa a ruwa, ko a tuwo, ko a sa zuma. Yana temakawa jiki, yaki da Mura. Yana kara kwayoyin jini da sauransu.
Yadda ake domin ruwan zogale
1 Asamu ganyen zogale a wanke shi sosai, a sa a wani abu a mutsuka, a matse a ruwan, ko a tafasashi, in ya huce sai a rika sha. Kada a sha fiye da kofi 2 a rana.
2 maganin mura da tari.
3 Maganin kumburin ciki da ciwon kai
4 Rage kiba
Ana sarrafa kwayoyinsa (seed)
1 Ana samun 'yayan zogale ana cin guda 1 ko 2. Ko kuma atafasa su a sha ruwan.
2 Yana taimakawa wajen tsaftace jini da hanji
3 yana rage kitse a jiki wayo (cholesterol)
4 Kara karfin garkuwar jiki.
MATSALAR DA ZOGALE YAKE DAUKE DA
Komai da kasani yana da anfani kuma akwai rashin anfaninsa, wato (side effect), don haka zamu dan kawo wasu daga cikin matsalar anfani da zogale fiye da kima.
● Idan mutum yana da karancin jini a jikinsa, kada yayi anfani da zogale sosai, hakan zai iya sa ma mutum ciwon kai, da zazzabi.
● in aka sha garin zogale ko ruwan sa da yawa yana iya haifar da zubewar ciki, ko kuma ciwon ciki.
● Mace mai sabon ciki, kada tayi anfani dashi sosai, sai da shawar warin likita, domin kaucewa matsala.
● yana sawa wasu nauyin jiki ko kasala in mutum yana jin haka in ya sha to ya rage anfani dashi.
● Kuma mutum ya guji hada zogale da wani magani idan yana sha yin hakan yana da matsala. Ya kamata duk a binda mutum zaiyi ya nemi shawar kwararru, a fannin, don samun zaman lafiya.
Kammalawa
A karshe muna bada shawara ga mai son anfani da zo, to ya tuntubi likita, Allah ya yiwa wannan bishiya albarka, don haka ayi anfani dashi ta hanyar da ta dace.
Tuntubemu 08148166212
Imel sadiku854@gmail.com
Nishadisport.blogspot.com
Usui kyau
ReplyDelete