Posts

LABARAN MAKO

Image
  GABATARWA  Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku labarai, da al'amura na yau da kullum, wato nishadisport nine naku Sadik Yusuf har kullum da  fatan kuna lafiya. Kwamishina ya aje mukaminsa  Ga sharhin labaran dallah-dallah. Kwamishinan sufiri na jihar kano Ibrahim Namadi, ya ajiye mukaminsa na kwamishina bisa radin kansa acewarsa.inda yake cewa:  "na aje mikamina na kwamishinan sufiri, saboda na kare kima, da martabar Gwamnatin jiha kar kashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, saboda abin da yafaru dan gane da belin wanda ake tuhuma da aikata lefin safarar miyagun kwayoyi.  "hakan ta farune saboda banyi cikakken bincikeba, na karbe shi saboda haka na ga ya dace da nayi murabus, kuma na bawa al'ummar jihar kano hakuri  da gwammnati, da yan jam"iya bisa abinda yafaru."  "Ina mika godiyata ga gwamna, saboda damar da yabani ta hidimtawa al'ummar jihar kano na gode." Kuma ya kara da cewa "na yi farinciki ...

DUKAN DUHU- NA DAYA

   GABATARWA   Salam yan uwa masu bin wannan shafi namu na blogs, wato nishadisport munamuku maraba da sake saduwa, nine naku Sadik Yusuf,   ga sharhin shirin " Dukan Duhu." Bayanin shirin Wannan labari da akawa lakabi da " Dukan Duhu"  labarine da yake nuna cewa kada mace ta juya baya, bayan angama komai na sha'anin aure. Saboda hakan ya haramta inko aka aikata haka to sai a saurari abinda zaije yazo. Kamar dai yadda aka musalta a wannan labari, kuma labarin ba da wani akeba, madallah. A gidan su Sailuba Suna magana da Babanta da mamanta. Umma tana magana tace:  "Wai, ni, baban Sailuba, mai katanada dangane da bikin wannan yarinya Sailuba."  Baban Sailuba yace: "To,! Amma dai kinfi kowa sanin halin da na tsinci kaina a yanzu ya kike so nayi, sata ko fashi" ta tari numfashinsa. Umma: "To,! duka, kaje kayi mana, ni dai kawai a wuyanka nake neman Gado da Kawaba ehe!" Nan ya yanke jiki ya fadi kasa tum, yasamu shanyewar barin jiki dama...

Gwamna ya samu hadarin Mota ya tsallake rijiya da baya

Image
     GABATARWA   Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku sharhin abinda ke faruwa a sassan Nigeria nine naku Sadik Yusuf.   Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya gamu da hadari. A ranar Lahadine wani lamari da ba'a saba ganiba a Nigeria ya afku wato ace Gwamna mai ci yayi hadari. Wato Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda, yayi hadarin mota a hanyarsa da yataho daga Daura zuwa katsina.inda wani dreban Golf yayi aron hannu. Shi ya haddasa hadarin.  Hakan na faruwa, nan da nan aka garzaya dasu asibiti dake Daura. Aka duba lafiyar su, su uku ne acikin Motar. Inda daga bisani kuma aka garzaya dasu asibitin tarayya na jihar Katsina.                   Umar Dikko Radda  Daraktan yada labarai na Gwamnan Katsina Maiwada Dan Malam yatabbatarwa manaima labarai lamari, inda yake cewa. "bayan abin yafaru. Aka kaisu wani asibiti dake Daura,aka basu taimakon gaggawa, inda daga bis...

SADIK YUSUF

Gabatarwa daga Sadik Yusuf Garba Ni sunana Sadik Yusuf Garba, an haife ni a unguwar Jakara, Tudun Makera, dake cikin birnin Kano, a karamar hukumar Dala, a shekara ta 1974. Na fara karatuna da karatun Alkur’ani mai girma, sannan na ci gaba da karatun Islamiyya. Haka kuma na yi karatun boko daga matakin firamare har zuwa sakandire. Na yi aure ina da shekara 25 a lokacin, yanzu kuma ina zaune a gidana tare da iyalina. Ina da ’ya’ya hudu — uku maza da mace daya. Harkokina na Yanzu Ina zaune a unguwar Goron Dutse kusa da hanyar gidan gyaran hali (prison) dake kusa da hanyar Kansakali. A nan ne nake gudanar da harkokin kasuwanci, musamman: Sayar da bakin mai Sayen duro da yamti Sayar da man mota da sauran mayuka daga kamfanonin cikin gida da na kasashen waje Harkokin Lafiya da Wasanni Na dade ina cikin harkar motsa jiki, musamman wasan kareti, inda na kai matakin bakar damara (black belt). Har ila yau muna gudanar da horaswa da tsalle-tsalle a Goron Dutse Sport Center, dake hanyar Jakara. H...

Antashi da rasuwa a Nigeria

Image
             GABATARWA  Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku labarai da sharhi kan al amuran yau da kullum. A wannan shafi namu na blogs nishadisport.blogspot.com.  Nine naku "Sadik Yusuf" nake gabatar muku da labaran.  * Rasuwar Muhammadu Buhari.   A yaune Lahadi tsohon shugaban kasar NIgeria. Muhammadu Buhari. Ya rasu a kasar ingila inda yake jinya  Kar kashin likitoci,mai magana da yawun tsohon shugaban kasa. Garba Shehu ya fitar da wata sanarwa,in da yace:  "ya rasu ne da misalin karfe 4:30 sakamakon doguwar jinya."  A cewar fadar shugaban kasa, Bola Ahamad Tinubu ya umarci matemakinsa, Kashim Shattima da yaje birnin na London ya rako gawar ta Muhammadu Buhari zuwa gida Nigeria.  A makon jiyane shugaban yaje birnin London domin duba lafiyar sa kamar yadda ya saba amma daga bisani yakamu da wata rashin  lafiya inda ta kaishi da kwanciya, a, Asibitin na London, kuma...

mahaukaci da soyayya

Image
    GABATARWA Salamu alaikum    Masu binmu a wannan shafi muna godiya da bamu hadin kai. A YouTube da kuma a shafin nishadisport.blogspot.com.  Wannan labari na Yar Malam kirkirarren labarine da aka yishi ta hanyar film don fadakarwa ba don waniba. labarin a kwai muhimman jarumai da suka taka rawa acikinsa lallai zaku ce na gayamuku. Mai rubutawa Naku Sadik Yusuf mungode! Sharhin Shirin Yar Malam — MAHAUKACI DA SOYAYYA  Assalamu alaikum, masu bibiyar tashar NishadiSport! Madalla da kasancewa da mu a cikin wannan shiri na Yar Malam.  A yau za mu duba abin da ke faruwa a cikin sabon sashe, inda mahaukaci dan gidan mai gari ya shiga wani hali saboda soyayya.               Mahaukaci ya tinkaro kawa Mahaukacin nan dai ya makale da son kawar Ladidi, yana yawo lungu da saƙo yana nemanta. Kamar wanda akace matar sa ta gudu yake yawon  nemanta. Idan aka tambaye shi, yana cewa, “Ni dai sai na aureta!” Kuma in k...

Rasuwar Aminu Dantata,Kano ta farka da alhini

Image
    GABATARWA  M una ci gaba da kawomuku abinda yake wakana a kasa baki daya a wannan shafi namu mai suna nishadisport ga labaran dallah-dallah. Alhini a Kano: Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata Ya Rasu Kano, 27/06/2025 – An tashi da jimami a jihar Kano da ma duniya baki ɗaya sakamakon rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin dan kasuwa  mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata. Wanda ya rasu yana da shekara 94, a kasar Dubai . Bayan wata gajeruwar jinya. Awani asibiti dake birnin na Dubai.Inda yake karbar jinya a chan. Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana’izarsa ne a Madina , Saudiya, kamar yadda ya bukata a wasiyyarsa.  A nan Kano kuwa, an gudanar da sallar jana’izar ga’ib ,a masallacin Aliyu bn Abi Talib, kar kashin jagoranci shek Ibrahim Khalil. Wadda ta samu halartar manyan baki ciki da wajen jihar, har da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , da sauran jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, da manyan ‘yan kasuwa daga ciki da wajen jihar. Madina ...