Nigeria a yau
GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu wanada muke kawo muku labarai da al'amura na yau da kullum da zaman takewar al’umma, nine naku Sadik Yusuf nake kawomuku labaran. YAN WASAN DA SUKA WAKILCI JIHAR KANO SUNA HANYAR DAWOWA DAGA ENUGU, SUN GAMU HADARIN MOTAR DA YA YI SANADIYAR MUTUWAR MUTANE 22 Yan wasan da suka wakilci jihar Kano, a wani wasan da aka fafata a jihar Enugu, yayin dawowarsu gida sun gamu da hadarin mota. ● Mutum ashirin da biyu sun mutu Wannan mummunan hadari ya yi sanadin mutuwar mutane 22, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata. Ciki harda masu horaswa,da 'yan wasa, drebobi, da sauransu. Jama’a da dama da suka jikkata suna karbar magani a asibiti inda ake basu kulawa ta musamman. Wadanda suka rasa rayukansu kuma, an yi jana'izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini tare da jajantawa iyalan mamatan, da daukacin al’ummar Kano. Haka zalika, ya sha alwashin dau...