DUKAN DUHU KASHI NA 2

DUKAN DUHU KASHI NA BIYU 

GABATARWA

Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, wanda muke kawomuku dadadan labarai masu cike da darasi, waɗanda suke taba zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum.

Zamu ci gaba da kawo muku cigaban labarin "DUKAN DUHU KASHI NA BIYU". Sai ku biyo mu a hankali don jin yadda zata kaya. Ni ne naku Sadik Yusuf, na gode!


SAILUBA TAJE WAJEN KAWARTA NEMAN SHAWARA

Sailuba tana ba kawarta labarin yadda sukai da Alhaji. Ita dai Halima ta tsaya tana sauraronta, tayi zugum da ido.

Halima tace:

"Nidai abinda zan gayamiki Sailuba, ki nutsu ki tsaya wajen talakanki, domin shi yafi dacewa da ke. Kar ki jifan gafiyar baidu."

Sailuba ta harareta cikin mamaki, tace:

"Yau kuma kece mai fadin haka? Ke da nake zato zaki maramin baya, amma sai naji wata banzar magana ta futo daga gareki haka."

Halima ta kara cewa:

"To ai gaskiya ne. Abinda yasa kika ga ina kin sale, saboda naga ba’a sa muku rana ba, kuma ba’a yi baikon ba. Tun da farko.To yanzu an saka rana, lokaci kawai ake jira. Karki ƙara ƙiraga, wannan shine dalilina."

Sailuba ta ce cikin haushi:

"Shikenan. Idan bazaki goyi bayana ba, to ki kyale ni. Domin yanzu nayi canji. Duk bakin cikinki, yar rainin hankali, ba ke bace kike cewa narabu da Sale ba, kuma yanzu nazo miki da maganar sabon saurayi, sai kice ba haka ba."


ALHAJI YAJE SAYEN SOYAYYA

Alhaji cikin wata arniyar mota 🚘 ya je wajen Sale inda yake likin taya ya sameshi chickin aiki. Sai Sale ya hango mota tsaye kusa dashi sai yai wajen.

Sale yace:

"Alhaji barka da zuwa, karin iska ko liki?"

Alhaji ya zuge gilashin motarsa yana masa wani irin kallo sama da kasa yace:

"A’a, ba don wannan na zo ba. Nazo ne domin muyi wani ciniki da kai." Sale yana mamaki me za'a saya a gunsa shida ko kaza bai daureba. Sai Sale yace:

"Ban fahimta me kakeso zaka saya a guna? ni da bana sai da komai, sai likin taya, itace sana'ata." Alhaji ya gyara Hula yayi murmushi.

Alhaji yace:   "Ba wani abu bane, soyayyar ka nake so ka sayarmin, domin naga wata yarinya Sailuba, tace kai saurayintane, don haka nazo mu sasanta."   Sale yadaga kai ya kalleshi yaji maganar wata iri.

Sale yace:

"Wai kana nufin na sayarma da soyayya ta wadda nake wa Sailuba?, a ina kataba jin haka run da kake?." Alhaji ya sake gyarawa yace:

"Kada ka cuci kanka kayi asara baki daya, shi isa nake maka wannan tayi kada kayi asara gaba daya."  Sale yayi fushi yana huci shi kadai.

Sale yace:     "To bari kaji abinda zangayama, in zaka ratayeni, ka tsireni kamar tsire, bazan taba sayar ma da Sailuba ba, domin ita rayuwatace." Alhaji ya kece da dariya. Sai yace:

"Shi kenan tunda haka kazaba ka rasa. Kuma kasani cewa ita Sailuba tunj ta sayar da tata soyayyar don kaji nagayama."  Sale yai dam!, yaji wata irin magana kamar a'lmara, ya zurawa Alhaji ido.

Shikuma Alhaji yakada kai ya shiga Motarsa ya tafi. Yabar Sale tsaye yan tinani. Nan da nan ya hada kayan likinsa ya tashi.



SALE YA KIRA SAILUBA 📞

Sale ya ciro wayarsa mai like da kyauro ya  kira Sailuba, waya ta shiga tana kara amma ta ƙi ɗaga waya. Halima ta yi mata nasiha amma ta ƙi sauraro. A lokacin suna tare da Halima

Halima tace: 

"wayarki tana kara bakiji bane?, Sailuba ita kara kallon waya tace:    "Wannan banzanne Sale yake damuna da waya shi baisan nachanjashiba, yake ta faman waya."

Halima ta numtasa tace:  To wulakanci ba dadi kiji tsoron Allah ba kyau wulakanta mutun, bare kuma wanda kikai wa alkawarin aure."  Sailuba ta daka mata harara.

"to na wulakantashi din sai me?, zaki soma min lalatar taki ko?, wallahi ki fita faga idona kar namiki rashin mutunci."  Sailuba ta tashi ta bar Halima a gun, Halima ta bita da kallo tai shiru abinta.

Shi kuma Sale yai mamakin kin daga waya daga masoyiyarsa Sailuba  yace cikin zuciyarsa:

"To bazan yanke hukunci ba, bari naje na ganewa idona, kar in yi abu cikin fushi."


SALE YAJE GUN SAILUBA, YA TARAR DA ALHAJI

Sale ya isa gidan Sailuba 🚲 sai ya tarar da ita da Alhaji suna hira cikin nishadi.

Sale yai turus, ya tsaya yana kallonsu, su basu ganshiba, yai fushi ya rasa meke masa dadi, sai ya yar da keken dake hannunsa, sai suka ji karar keke ya dau hankalinsu suka juya suka ga ashe Sale.

Da suka ganshi sai suka yi dariya suna nuna shi da yatsa 👉. Sale ya juya cikin bakin ciki ya tafi.

Sailuba tace da Alhaji:  "tunda haka wannan mutumin ya zaba, cewa a tsireshi to ni aganina ya kawo shawarar yadda za'ai dashi saboda haka kai Alhaji ya rage naka."

Alhaji ya gigiza kai yace:    yace hakane kuwa zai gani.



AN BIYO SALE ZA’A HALAKA

Wasu mutane biyu suka biyo Sale suna son halaka shi. Suka yi ta neman sa har  suka hadu, yana ganin su ya ranta a na kare suka bishi, ya samu ya guje musu, suka duba basu ganshiba. 

Da yaji shiru sai ya futo daga inda ya buya, ya lallaba ya futo yaga wata bishiya ya hau, yana hawa ,sai yagansu a kan bishiyar, nan da nan ya durgo kasa, suka biyoshi.

suka rutsashi suka kaimasa bara ya goce yana jan kugu a kasa, da kyar suka kamashi a chafke shi, suka daure shi sai gaban Alhaji.


SAILUBA A GIDA DA MAMANTA

Sailuba tana ba mamanta labarin yadda suka kitsa kashe Sale, ba tare da ta nuna damuwa ba.

Umma tace:

"To, yanzu ya kukayi da shi?" Sailuba tana dariyar mugunta.

Sailuba tace:

"Tunda an masa tayin kudi, yace bazai karbaba sai dai a tsireshi, to don haka muka zabi tsirewar, har jininsa ya dige." Tana dariya.

Umma ta amince da maganar ’yarta ko tsoro babu.Don karanta dukan duhu na daya latsa nan


KAMMALAWA

Nan muka kawo ƙarshen wannan kashi na Dukan Duhu Kashi na 2. Sai ku biyomu a kashi na 3, don jin yadda zata kaya tsakanin Sale da Alhaji, bayan sun kamashi sun daure shi.

  • Shin Sale zai kubuta a gunsu?
  • Ko Alhaji zai auri Sailuba?

👉 Ku biyo mu a gaba a blog ɗinmu: nishadisport.blogspot.com


DARASI

  • Iyayen su daina goyuwa da bayan ’ya’yansu wajen cin amana.
  • Zalinci ba shi da daɗi, domin Alhaji ya haɗa kai da mugaye.
  • Zamuga yadda zasu kare.

TUNTUBA

📧 SADIKU854@GMAIL.COM


📞 08148166212


Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

A chuci Mata-kashi na 1

An tarewa Sani hanya