Posts

Showing posts from September, 2025

DUKAN DUHU- KASHI NA 3

  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna ( nishadisport). Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!. Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3  SALE DAURE A WANI KANGO  Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit. Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba. Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace: Alhaji:  "Malam Salele mai liki,  yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soya...

DUKAN DUHU KASHI NA 2

DUKAN DUHU KASHI NA BIYU  GABATARWA Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, wanda muke kawomuku dadadan labarai masu cike da darasi, waɗanda suke taba zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum. Zamu ci gaba da kawo muku cigaban labarin "DUKAN DUHU KASHI NA BIYU" . Sai ku biyo mu a hankali don jin yadda zata kaya. Ni ne naku Sadik Yusuf , na gode! SAILUBA TAJE WAJEN KAWARTA NEMAN SHAWARA Sailuba tana ba kawarta labarin yadda sukai da Alhaji. Ita dai Halima ta tsaya tana sauraronta, tayi zugum da ido. Halima tace: "Nidai abinda zan gayamiki Sailuba, ki nutsu ki tsaya wajen talakanki, domin shi yafi dacewa da ke. Kar ki jifan gafiyar baidu." Sailuba ta harareta cikin mamaki, tace: "Yau kuma kece mai fadin haka? Ke da nake zato zaki maramin baya, amma sai naji wata banzar magana ta futo daga gareki haka." Halima ta kara cewa: "To ai gaskiya ne. Abinda yasa kika ga ina kin sale, saboda naga ba’a sa muku rana ba, kuma ba’a yi baikon ba. Tu...

A CHUCI MATA kashi na biyu

Image
    GABATARWA  Salamu alaikum masoya wannan dandali namu wato nishadisport. Muke muku barka da wannan lokaci zamu cigaba da kawomuku labarin "A chuchi Mata" kashi na biyu, wanda yake kirkirarren labarine ba da kowa akeba. Da fatan za ku biyomu kuga yanda zata kaya.                               Hoton faster Achuci mata  FATIMA NA BA UMMAN TA LABARI TSAKANINTA DA SAURAYINTA  Fatima ta isa gida ta shaidawa babarta abinda ya gudana tsakanin ta da saurayin da ta yiwa tsiya, tqi watsi da shi.  umman tata tace: "Ai haka yafi, yaje ya karata matsiyaci kawai." Suka tafa da maman tata suna shewa.   Boss yazo gun Fatima Boss me badda kama, yazo ya tabbatar wa da Fati cewa auranta  zaiyi, ta amince dashi, sukai sallama ya tafi, itama ta shiga gida ta gayawa ummanta yanda sukai. Fati tace: "wannan mutumin da yazo wai cewa yayi zai aureni".sai  Umman tata:tace " haka yace?....

A chuci Mata-kashi na 1

Image
    Salamu alaikum masoya wannan dandali namu naku mai farinjini wanda kuke son ji da gani da karatu ku biyomu a NishadiSport – A Chuci Mata (Kashi Na Daya) Rubutawa: Sadik Yusuf         Gabatarwa  Assalamu alaikum masu bibiyar tashar NishadiSport, ni ne naku Sadik Yusuf. Muna kawo muku dadadan labarai, da fatan kuna jin dadin shirye-shiryenmu. wannan labari na "Achuci Mata" kirkirarren labarine anyishi ne badan waniba ko kuma wata , kawai dai labarine,kada wani yaga wani abu da yai kama da halinsa ya zaci dashi muke mun gode!.🙏 * RIGIMA BOSS DA ISAH A wani gari, akwai wasu abokai suna rigima akan wani bashi da Isah yake bin abokinsa mai suna Boss. Isah ya rike wuyan Boss suna kokawa yana cewa sai an biyashi kudinsa da ya kai shekara guda ba'a biyaba.  Suka cukume suna kokawa a tsakaninsu titi-titi   Boss ya samu sa’a ya daga Isah ya bugashi da kasa har ya ji masa rauni, sannan ya gudu ya barshi a nan yana murkususu. Da kyar Isah y...