Assalamu alaikum masu binmu a wannan shafi namu mai Suna.
nishadisport.blogspot.com, barku da sake haduwa damu har kullum ni ne naku "Sadik Yusuf" ga abinda yake wakana a wannan rana ta Talata 1/7/2025,kamar haka.
Matatar Dangote ta rage farashin mai.
Matatar mai ta dangote ta sanar da rage farashin mai daga Naira dari takwas da tamanin zuwa naira Dari takwas da arba'in a gidajen mai na yan kasuwa, mu samman ma gidajen dake da alaka da Dan Gote kamar irin su (M R S) da sauransu.
Hakan ya biyo bayan tsayar da yaki tsakanin Isra'ila da Iran wanda tun afarko yakin ne ya jawo tashin man, kuma yanzu da yakin ya dakata farashin ya sauka, har mutane sun fara cece kuce kan karin man.
Har gidajen man sun fara rufewa da jin labarin tashin man fetir din, to abin jira agani dai yanzu raguwar farashin ya fara aiki nan danan kar yan kasuwar man suyi abin da suka saba suce basu sayar da na bayaba, amma inkari yazo kawai ba jiran kawo sabon mai, sai su kara kudi ,Allah ya kyauta.
Ya kamata dillalan man fetir su rika yin abin da ya dace na saukakawa jama'a masu sayen man ko mutane saji saukin radadin rayuwa,
Za'a mayar da gwamnan rivers
A wani labarin kuma shugaban kasa Bola Ahamad Tinibu, yana shirin mayar da gwamnan jihar rivers, Simalye fubgbara kan matsayin sa na gwamnan jihar bayan samun sulhu da uban gidansa na siyasa tsohon gwamnan jihar ministen babban birnin tarayya Abuja.
Wato Iwelson Wike shugaban kasa ya shiga tsakani yayimusu sulhu wanda manya na jihar suka halarci taron ciki harda kakin majalisar jihar, rudanin siyasa ya barke ne a tsakanin gwamna kubarah da Wike sakamakon rashin jituwa a tsakaninsu har abin ya kusa rusa tattalin arzikin jihar Da kuma rarrabuwar kai a tsakanin manya yan siyasar jihar,Suna nunawa Juna yatsa.
Yanzu dai ana fatan komai ya zo karshe sakamakon sanya
dokar ta baci a jihar. Da Bola Ahamad Tinubu yayi.
Anasan ran binne Dantata.
A yau talatane kuma ake sa ran binne Alhaji Alhasan Dan Tata marigayi ,sakamakon tsaiko da aka samu wanda tun da farko an shirya binne shi a ranar litinin da tagabata hakan yasamo asaline saboda cike ciken takardu da akeyi tsakanin ofishin jakadanci na Nigeria da na saudiyya,da kuma iyalan mamacin,wanda tuni birnin na madina ya karbi manyan baki daga Kano da ma Nigeria baki daya da gwamnonin arewa.
kuma yanzu janaizar tasa ta koma zuwa magariba sabanin yanda akashirya yi zuwa la'asar tunda farko.
Atabakin mataimakinsa na musamman Muhammadu Mustafa Junaid shi ya bayyana hakan, "yace tuni gawar tasa ta isa Birnin na Madina za'a shirya gawar kafin daga bisaji akaishi masallacin shugaban halitta baki daya, a gudanar da sallah kana a binne shi.
Haka gwamnan Jigawa Namadi Sambo da kuma gwamnan kano Abba Kabir Yusuf suka kaiwa iyalan mamacin ta'azyya a birnin na madina.
Allah hu Akabar Allah ya jkansa da gafara ya kyauta makwanci amin.
Aminu Alhasan Dan Tata ya samu gagarimin martabawa sakamakon da hukumar saudiyya ta bayar na a bari a shiga kasarta a binne shi, hakan yasamo asaline na da daddiyar alaka dake tsakaninsu tun shekarun baya sanda yake da rai, abokinsu ne na kud da kud.
Bakowane yake samun hakaba ya mutu a wata kasa kana a kaishi birnin na madina a binne sai dai-dai. Allah yasa mudace amin.
Tsokaci
Wani lamari da yakunnokai cikin wannan jiha tamu ta Kano, wato shine zakaga yara kana yan mata da basu wuce shekara bakwai zuwa takwas ba suna bi bakin danja suna goge gilas din Mota kamar yadda maza keyi wani lokacin kuma suna bi suna bara.
To matsalar anan itace makomar yaran nan gaba ya zata kasance, yara ba makaranta sun zama uwa ba kwaba zakaga sunata fada akan abinda ake basu.
Suyita gunduma ashar akan titina na birnin Kano,muna kira ga hukuma ta kalli wannan lamari tun kafin yayi Girman da magance shi zaiyi wahala domin su Allah ya dorawa kula da hakkin mutane gwamnati tayi duk me yiwuwa wajen ganin ta magance wannan lamari domin a samu yara nagari a nan gaba asamu a sasu a makaranta.
Don a haifi da mai ido nan gaba saboda barin yaran a haka yana da mummunan hadari a gaba suke zama matsala ga kasa su zama yandaba ko barayi 'yan shaye-shaye, Allah ya shiryi bayinsa yabasu abunyi amin.
Yara masu roko kan Titi
Zamba da damfara.
Haka kuma wani sabon lamari da ya kunno kai cikin al’umma wato shine za'a sanyawa yaro takarda dauke da adreshin wani guri a jiki,sai yaron ya futo kan hanya yana kuka.
To idan akasamu wani ya tausayamasa ya ga wannan takarda a gaban Aljihun yaron ya tausaya sai ya dauki yaron da zummar ya kaishi ga wannan adreshi da yagani, to dazarbyaje wannan guri sai wannan mutane suyimasa fashi,kudi ko waya ko kuma abin hawan nasa dugurum, wannan lamari an bayyanashine a tagwayen Gidan rediyo na Kano.
Ta bakin Malam Nuhu Gudaji inda akewa Malam Ibrahim Khalil tambaya kan mai zaice game da wannan al'amari.
Malamin yace "to kamata yay duk wanda aka gani da irin wannan takarda a jikinsa koma babu to mutum ya kaiwa 'yansanda wannan yaro domin sune suke da iko a hannunsu na kama duk wani mai laifi.
Yakara da cewa ko mai unguwa kada a kaiwa domin shima yana iya cewa zaije ya kai yaron kuma a illatashi, don haka muna kira da mutane sukula sosaia karshe yayi addu'ar Allah ya kawo karshen wannan lamari baki daya mutane su hau kan laying sudena mugun abu."
Ni ne naku Sadik Yusuf.
Nagode! za'a iya tun tubarmu ta hanyar imel namu .
Sadiku854@gmail.com. ko lambar waya 07082643256
Gwamnati ki farka
ReplyDeleteAllah ya kawo sauki
ReplyDeleteAllah ya kawo sauki
ReplyDelete