Nigeria a yau

   Yan wasan da suka wakilci jihar Kano a wsanin da aka fafata a enugu a hanyarsu ta dawowa Kano suka gamu da hadarin  mota  inda mutum 22 suka. Mutu , inda wasu kuma suka jikkata ,suna karbar magani a asibiti suna samun, kulawa ta musamman wanda suka  mutu kuma akayi janaizarsu kamar yadda addini ya tanadar  ,tuni gwamnan kano Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa jama'ar Kano inda ya mika gaisuwarsa ga jama ar jihar kano da kuma iyalan wanda suka mutu yakuma ci alwashin daukar nauyin maganin wanda suka jikkata Allah ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba, itama fadar shugaban kasa ta mika gaisuwar ta ga gwamnati da alummar Kano da kasa baki daya. 
 Allah ya kyauta ya kiyaye afkuwar haka nan gaba. 

   Anata hada hadar kwaso dabbobi daga guri zuwa guri, amma akwai wani abu da na lura dashi masu kai dabbobin suna gwada musu rashin imani suna labtarsu baji ba gani abin tambaya anan shine wai babu hukuma mai kula da hakkin dabbobine ? Inakwai to yakamata su farka su sauke nauyin da ya rataya akansu, wani abu da nagani mutum ya dakko dabba a kan babur a baya sun daure mata kafa kuma sun hau kanta sun zauna suna tafiya babu tausayi ko kadan ba tsoran Allah  Allah ya ganar da mutane su rika kula da hakkin dabba.

 Amma fa sai gwammnati ta tashi tsaye ta kula da hakkin dabbobi wajen kar kade dokar da ta ke kare hakkin dabbobi 
Inkuma babu to ya kamata a samar da ita domin suma dabbobi suna da hakkin a kula dasu , kamar yadda kasashen duniya suke kula da dabbobi in ka wulakanta dabba a wasu kashe na yamma to ko zaka gaya wa aya zaki
wanda haka shine abin da yadace. 

 Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suna cewa yakamata gwamnati ta farka ta rika lura da masu cin zarafin dabbobi ana hukuntasu, don ko musulinci bai yadda da cin zarafin dabba ba koda kuwa yankata za: ai ,yakara da cewa in zaka yanka dabba ka wasa wukarka sosai tukun domin ka hutar da abinda xaka yanka,kuma ka daure shi ka juyar da fuskarsa kasa kada a rika nunamasa cewa yankashi za'ai.  Amma sai kaga yara sun daurowa sa igiya wajen guda hudu suna ta dukansa alhali kuma yana tafiya ba baya tafiya kaga hancinsa yana ta jini amma su ko jikin
su baruwansu wani lokaci ma hakan yasa, dabbar, yarasa ransa, ko kaga an dakkosu a mota tun daga wata kasa kamar irinsu jamhuriyar Niger da sauransu ko kuma wata  jiha a cikin kasa Nigeria don haka nake kira da kakkausar murya da mutane su kula da hakkin dabbobi ko suma Allah ya tausayamusu domin hakan yazama zalinci kowa kuma yasan Allah baya son zalinci don haka mu gyara.

 Kowa yayi da kyau zaiga da kyau wannan shine nasihar ta yau saboda ance duk abin da ka shuka shi zaka girba don haka mutum ya kiyaye da hakkin mutane dana dabbobi  don shma yasamu yanda yake so, mungode da bibiyarmu da kuke ayima subscribe, a mana shere,  kuma abimu a shafukanmu da ban da ban mungode 
 Naku,  Sadik yusuf 

 Sadiku854@gmail.com. 

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review

Burinsa ya cika