Rasuwar Aminu Dantata,Kano ta farka da alhini

 Alhini a Kano: Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata Ya Rasu

Kano, 27/06/2025 – An tashi da jimami a jihar Kano da ma duniya baki ɗaya sakamakon rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin dan kasuwa  mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Alhasan Dan Tata.

 wanda ya rasu yana da shekara 94 a kasar Dubai. Bayan wata gajeruwar jinya. A waji asibiti fake birnin na Dubai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana’izarsa ne a Madina, Saudiya, kamar yadda ya bukata a wasiyyarsa.


 A nan Kano kuwa, an gudanar da sallar jana’izar ga’ib,a masallacin Aliyu bn Abi Talib kar kashin jagoranci shek Ibrahim Khalil,wadda ta samu halartar manyan baki ciki fa wajen jihar, har da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da sauran jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, da manyan ‘yan kasuwa daga ciki da wajen jihar.

Ya bar Yara Goma Sha Takwas

Marigayin ya rasu ya bar yara 18, kuma yana da iyalai da dama. Da mata biyu.Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa.


Takaitaccen Tarihinsa

Alhaji Aminu Dan Tata ya fara karatunsa a makarantar firamare ta Koki, unguwar da ya taso a cikinta. Wadda mahaifinsane ya samar da ita.

Ya taba rike mukamin kwamishina, sannan ya kasance fitaccen dan kasuwa hamshakin attajiti mai rike da kamfanoni da kadarori a ciki da wajen Najeriya.

 Yana da gidaje da gilaye da gonaki har ma ace bai san adadinsuba, bugu da kari yana da gida a ingila,da saudiyya,da hadaddiyar daular larabawa wato Dubai da faransa, da sauransu.

Kuma anayimusu lakabi da (Alasawa) sakamakon shura dasukayi wajen kasuwanci da taimakao,kuma dukansu fanginsu suna da kudi ciki kuwa harda attajirin Africa baki daya wayo Dan Gote.

An san shi da taimakon jama’a, gina makarantu, asibitoci, da ma’aikatu, da kuma taimakawa gwamnati da ‘yan kasuwa a lokutan gaggawa kamar gobara, ambaliya, da bala’o’i daban-daban. Hakika anyi rashi babba.

“Ya Gaji da Duniya”

A cewar wani rahoto, an rawaito cewa ya bayyana cewa “ya gaji da duniya” yana fatan komawa ga Allah. 

Sakamakon rashin sa'oinsa domin duk sun koma ga Allah kuma gashi yanzu lokacin ya yi – Allah ya amshi rayuwarsa cikin rahama. Kuma alumma sunyi jimami.

Gidansa – Cibiyar Taimako

A kullum, gidansa cike yake da jama’a masu neman taimako. Ana ciyar da mutane da abinci mai rai da lafiya, har da nama, kowane lokaci.

 Hakika, mutane sun nuna alhini sosai da kuka, suna cewa an yi rashin gwarzo, wanda maye gurbinsa yana da wuya. Kano tayi asarar hamshakin mai taimako.


Gwamnatin Tarayya Da Jam’iyyu Sun Aike Da Sakon Ta’aziyya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta bakin fadar gwamnati, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, al’ummar Kano da kuma Najeriya baki ɗaya.

Abdullahi Umar Ganduje yayi murabus 

Haka zalika, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin jam’iyya, bisa dalilan rashin lafiya, kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar ya tabbatar.

Sai dai ‘yan adawa na ci gaba da bayyana shakku, suna cewa murabus din ba komai bane illa sakamakon matsin lamba da rikicin cikin gida na siyasa, duk da cewa jam’iyyar APC ta musanta hakan.

Fashi kansa Abdullahi Umar Ganduje din "yace ya ajiye bisa rasin kansa domin ya kula da lafiyarsa.


Sabon Lamari Mai Tsoratarwa: Jariri Ya Tsira Daga Kisan Gilla

A wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a Kano, an tsinci jariri sabuwar haihuwa a cikin rami, bayan an binne shi da rai.

Cikin ikon Allah, mutane sun jiyo kukan jaririn, suka kira ’yan sanda, wadanda suka tona ramin a hankali suna tonawa suna fadin inna lillahi wa'innah ilaihi raji'un suma sun girgiza a hankali har suka ceto shi. 

Yaron ya kasance a nade cikin atamfa, an daure shi da igiya kuma an binne shi a raye.


wannan lamari yazama ishara mai ban tsoro daga Allah subhanahu wata 'ala ace anbinne jariri daraj amma bai mutuba har aka jiyo kukansa akazo aka tonoshi. 


Wallahi jama’a muji tsoron Allah mu kaucewa asarar rayuwa ta duniya da kuma lahira.

An Zargi Tsafi Ko Cikin Zina

Mutane na hasashen ko dai cikin zina ne aka yi aka binne, ko kuma wani lamarin tsafi ne. Sai dai, Allah ne mafi sani. Wannan lamarin ya girgiza jama’a da ma jami’an tsaro da suka halarci wurin. Allah ya kyauta ya karemu daga shrrin zuciya amin.


Rufe makarantun kwana a Kano 

A sassan kananan hukomimi na jihar kano an rufe makarantu na kwana a shekara ta dubu biyu da shadaya sakamakon rashin tsaro da arewa ta tsinci kanta aciki, yo amma yanzu abin ya kawo tsaiko wajen cigaban karatun yara musamman na karkara wannan makarantu sun lalace kjma ga rashin dalibai.


Al'ummar yankin sun koka sakamakkn lalacewar da marantun sukayi, akwai wata makaranta a wata karamar hukuma dake kano sun koka acewar wani tsohon dalibin makarantar.

 "da makarantar tana da dalibai kimanin dubu biyu amma yanzu sakamakon rashin yin bodin din ya sanya yara basa zuwa makaranta saboda nisa da kuma lalacewa da tayi inji shi"

Haka wani dalibi me mafarkin ganin yazama likita shima ya baiyyana damuwarsa na rashi kyau na makarantar inda yace:

 "ni nakasance ina so inzama likita amma yanzu abin ya faskara sakamakon rashin malamai masu koyarwa,wanda ada makarantar tana da dalibai kimanin dubu uku amma yanzu bagi mu biyar a ajiba kima makarantar gaba daya bamu fi mu ashirin da biyarba."

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa yace: 

"ada makarantar tana da kyakyawan tsari cike take da dalibai har da namakotan jihar kano ana kawosu wanda da akwai gidajen malamai kusan guda ashirin amma yanzu duk sun lalace ba rufi a kansu wannan ya haifar da koma baya a wannan yanki namu muna fata gwamnati ta wai wayi wannan yanki ta kawo dauki in jishi."

Da aka tambayi kwamishinan ilimi na jihar Kano Mustafa Rabi'u Musa yace.

 "wannan lamari ga darsa mukai kuma muna iya bakin kokari muga mun gyara don samun cigaban ilimi a wannan jiha tamu ta Kano kar kashin Alhaji Abba Kabir Yusuf, kuma muna kan gyaran in Allah yaso."


Kammalawa

Lamarin rasuwar Alhaji Aminu Dan Tata, da kuma abin da ya biyo baya na jariri da aka binne a raye, sun nuna irin halin da al’umma ke ciki da kuma irin jarabawar da muke fuskanta.

Allah ya jikan mamacin, ya shiryar da bayinsa, ya karemu daga sharrin mutane da al’amura marasa kyau.
Amin.


Rahoto daga: Sadik Yusuf
📧 sadiku854@gmail.com
🌐 nishadisport.blogspot.com



Comments

Post a Comment