YAR MALAM SEASON 1 EPISODE 1 review
GABATARWA
Salamu alaikum barkanmu da saduwa, a wannan dandali namu wato nishadisport wanda muke kawo muku sharhin Shirin film din 'Yar Malam". Daga sadik Yusuf.
๐น️TSOKACI KAN FILM NA 'YAR MALAM ZANGO NA 1
Shirin Yar Malam Kashi na daya, shirine da yake nuna rashin rike amana na wani mutum da dan uwansa ya mutu ya bar masa dukiya.
kamar irin su gonaki, dabbobi, da kuma kudi, da gidaje , kuma mutimin mai suna M Nomau, mutumin kirkine ya temaki dan uwan nasa ,mai suna Malam Idi.
Amma yaci amanarsa ya kasa rike wannan amana da yabashi. Saboda rudin zuciya. Ga kadan daga cikin episode one.
๐น️A GIDAN MALAM NOMAU
Ladidi na zaune a kusa da mahaifiyarta ta tashi don ta kaiwa babanta ruwa sai tasameshi a kwance ya kasa tashi, yana nishi sama-sama.
Sai nan danan ta durkusa gabansa tana Kuka, ta Yar da kofin dake hannunta shiko yakama yimata nasiha cewa:
Malam Nomau:
" Ladidi Kiji tsoron Allah ki kasance mai addu'a a duk inda kike." Tana kuka tana firgecewa ta rasa meke mata dadi.
Malam Nomau:
Sai yace: "takiramasa Dan uwansa" nan ta tashi ta rugo da gudu,babarta tana mata magana amma tayi gaba ta bata tsayaba, garzaya ta kirashi .
Nan da nan mahaifiyar Ladidi ta shiga gun nasa itama ta ganshi ba yadda yake yana ta faman shakuwa.
Mama cikin kaduwa tace:
"Malam ko akawomaka Ruwa ne?." Malam Nomau yana shakuwa da kyar yake magana. Sai yace:
"A'a! Ki barshi wannan shakuwa tawa bata shan ruwabace."
Mama itama sai kuka take tana masa fifita.
๐น️ LADIDI DA IDI SUN KARASO
Malam Idi Yazo da sauri shi da Ladidi, ya durkusa gabansa, nan M Nomau yabashi amanar iyalinsa da Kuma dukiyarsa, gaba daya.
Malam Nomau: Ya rike hannun dan uwansa Malam Idi yace dashi:
"Kaji tsoron Allah ga iyalina da dukiyata, ka kulammin da
su, wasu abubuwa nawa ba sai nafadaba ka sansu. Domin dakai ake komai."
Nomau ya juya gun Ladidi yace: "kar ki manta da abin da nagayamiki." Tana kuka tace: "to Baba" idi yai kasake yana sauraronsu.
Nan take ya mutu. Suka kama kuka shiko Malam Idi yatashi ya futa da alamar murna a fuskarsa, sukuma suna ta faman kuka.
๐น️ IDI YA HANA ZAMAN MAKOKI
Ya hana Zaman makoki ya samu abokin Malam Nomau wato Soja kan batun dawo da kadarori da suke a gunsa, Soja yayi mamakin wannan lamari.
Malam Idi:
Yahadu da soja a hanya bayanda soja yadawo daga wata tafiya sai Malam idi yace:
"Yauwa daman kai nake nema domin ka dawomin da gonaki dake hannunka na dan uwana Nomau."
Soja:
"Yo mai yafaru kake wannan tambaya haka ai gidan na Malam nomau zani."
Idi yace:
"Ai Malam Nomau ya mutu." Soja ya dafa kirji ya zaro ido:
"Yamutu! Allah ya jikansa yai masa rahama yasa yahuta."
Soja Yai mamakin Malam idi,ya kara da cewa :
To!, "zan kawo." ya tafi abinsa. Ashe shima gafiyane tsira dana bakinki.
๐น️ SOJA SHIMA YANASON CINYE GADO
Soja babban yaran Malam Nomau ne, bayan Malam idi, duk wani abu na Nomau, dashi ake guda narwa.
Gonaki dake gurinsa so yake ya cinyesu, shikenan suka shiga takun saka tsakanin Soja da M Idi kowa Yana ganin kowa macuci ne. oh, Allah sarki Ladidi macuta sun kewayeta.tanata fama dasu.
๐น️DOGO DA GA IDI
Ga Kuma dansa Dogo wato da Ga M Idi Shima yabi sahun ubansa wajen muzgunawa Ladidi.
Haka ta rayu har saida uwar itama ta rasu kaka kara kaka ya ya Ladidi zata kasance a chikin wannan hali na kuncin rayuwa.
Haka wani lokaci taje neman taimako har gidan Malam Idi, amma M Idi ya koreta yai mata fata- fata har matarsa tana taremata amma yarufeta da fada, tayi shiru abinta ta zuba ido.
Dansa wato Dogo shi kuma ya biyewa ubansa aka cigaba da wulakanta Ladidi.
Dogo da Magatakarda
Dogo da abokinsa wanda shi kuma yake zuga Dogo don su chimma burinsu shi da Babansa domin ganin an mallake wa Ladidi kudinta da gonaki, shanu, gidaje,da sauransu ko tsoro basa ji.
Ga ukuba da Allah ya tanada saboda Allah yai hani da haka akwai azaba da ya tanada ga mai cin hakkin marayu kuma tun daga Duniya zai fara fuskantar matsala.
Sudai su Dogo da abokinsa, magatakarda da mahaifinsa ko ajikinsu,wai an yakushi kakkausa suka ci gaba da muzgunawa Ladidi duk fa don taji wahala ta sadudu.
Ko kuma ta mutu gabaya a huta bisa zugar Maga takarda abokin sa.
๐น️ MALAM IDI YA HADA KAI DA ME GARI
Shikuma M Idi yayiwa mai gari alkawarin bashi gona daga cikin gonakin Ladidi a zuwan toshiyar baki don ya bashi hadin kai komai yatafi yanda suka tsara.
Haka kuwa mai gari ya bashi hadin kai shima ya samu nasa Rabon.
Kajifa uban kasa dashi aka hada kai a cinyewa marainiya hakkinta, wanda shi ya kamata a kaiwa karar andanne hakki ya kwato wai kuma shine zai cinye kaji shi kuma irin nasa salon na mugunta
๐น️MAHAUKACI 'DA GA MAI GARI
Gefe daya kuma mai Gari yana da wani da shi kuma mahaukacine in yaga galala sai yabika da duka haka ake ta fama da shi acikin garin ,amma idan kace dashi "in anbi Rabbana, sai yace:" ba wahala nawa"
Sai ya kyaleka katafi ba abinda zai maka,shikuma kaji nasa salon na mahaukata. In kuma bakafadi hakaba yo kuwa kashinka ya bushe. Ku kasance damu dai cikin wannan kaya taccen shiri namu na YarMalam.
Sai kuma labarin Sani, wanda shi kuma yake temakon Ladidi tunda yazo wucewa ta unguwarsu yaga dogo ya nema yayi mata wula kanci nan ya samu ya temaketa .
Shi kuma kaji yadda akai ya shigo rayuwar Ladidi, yaba babansa labarin ta ,shi kuma uban yace lallai ya samu ya temaketa domin yasan zai iya.
Sai kuma kawa wadda take shareware Ladidi hawaye lokavin da ta shiga wani yanayi na ukuba da wulakanci.
A kwai munzali Gurgu sahima da ga Soja shikuma Ladidi yake so amma ita bata sons, gefe guda kuma suka kama rigima sa Sani saboda Ladidi.
Munzali Gurgu da Soja
KAMMALAWA
● Nanne karshen wannan sharhi shin Malam idi zai yi nasara a cinye dukiyar maraya?.
● Yaya idi zaiyi da soja? Ko soja zai kaimasa gonakin wajensa.
● Ya ya kuma mahaukaci dan mai gari? Sai a kasance damu don jin shiri na gaba a blog namu.
ko kubiyomu a tashar tamu wato nishadisport, a manhajar youtube. Shin waye zai nasara a wannan lamari mai rikitarwa sai kubiyomu.
In kun shiga shafin youtube kuka rubuta "nishadisport" tasharmu zata bayyana saika kalli duk wanda kake so daga shirye shiryenmu na zamani, suna da kyau ga ilmantarwa, ga Nishadantarwa gami da ban dariya maganin hawan jini.
An kasa wannan shiri gida-gida, a kwai (play last) na kowane season daga (season )1 har zuwa (season ) 2 da (season 3) mun gode!.
By Sadikyusuf:
๐ Http://nishadisport.blogspot.com.
๐A tuntubemu sadiku854@gmail.com
๐Lambar waya 08148166212
Zamu kallah
ReplyDelete