DUKAN DUHU- KASHI NA 3

  GABATARWA

Salamu alaikum masoya wannan dandali namu, na nishadisport. Wanda muke kawo muku dadadan labarai, na kasa, da kuma labarin fina-finai wanda muke juyasu izuwa bidiyo, a manhajar youtube mai suna (nishadisport).

Daga Sadik Yusuf, wanda shine yake kokarin yi muku, wannan ✍️ rubutu da fatan kuna gamsuwa, na gode!.

Ga cigaban labarin Dukan Duhu na 3 

SALE DAURE A WANI KANGO 

Bayan yaran alhaji sun kamo Sale, sun daure shi a cikin wani gini wanda ba'a karasaba, yana daure bai san inda kansa yakeba. Kawai sai suka zuba masa ruwa, ya farka firgigit.

Sai yaga alhaji tsaye da yaransa sun hada rai kamar saci babu, sai alhaji ya kece da dariya irin ta mugunta, ya kalli Sale yai shiru bai ce komaiba.

Sale ya kallesu daya bayan daya ya sunkuyar da kansa kasa, Alhaji ya zuba masa na mujiya, sai ya kada baki yace:

Alhaji: 

"Malam Salele mai liki,  yanzu gaka a hannuna, naima tayin kudi, kaki karba. Kace ko za'a tsireka jininka ya dige kasa, bazaka sayarmana da soyayyar kaba." Shi dai Sale yana kallon sa kawai, yana alamun jin zafin dukan da'aka yimasa da kyar yake magana, sai yace:

Sale:

"Hakane har yanzu ina kan bakana, wannan magana da nai haka take. Yanzu gani a daure gaban ka ba wanda yake ganinmu a mutane sai Allah. Zan sake mai-mai ta maganata, alhaji kozaka tsireni har jinina ya dige kasa, bazan sayar da soyayya taba, idan kun kasheni to ga duniyar nan ku zauna aciki."

Alhaji ya kalleshi ransa a bace, ya kalli yaransa yace:

"Kai! bana san surutun banza ku aikashi lahira kawai." Suka danne shi gami da shakewa, har ya mutu, sai da sukaga ya dena motsi, sai suka haka rami a kangon suka binneshi.

Suka duba basuga kowaba sai suka fice suka bar gun. Kaji yadda aka gama da Sale.

● Alhaji yaje gun Sailuba suna murna

Alhaji da sailuba, suna farinciki sun kashe Sale, suna ta annashuwa abinsu, sai sailuba tace:

"Ai indai akace baka da rabo shi kenan, amma mutum a bashi kudi, yaki karba, wai shi ga sarkin soyayya yo ga irinta nan yanzu ya sheka." Alhaji yayi murmushi shima yana magana yace:

Alhaji:

"To bashi kenanba yanzu ya rasa komai, ba kudi,  ba rai ba Sailuba, ya huta yaje chan yaci soyayya." Suna magan suna dariya.

Allah ya kiyashemu da rudin zuciya, irin ta su alhaji da sailuba, amin.

● Sale ya zama fatalwa

Bayan kwana 2 da kisan Sale, sai yazama fatalwa,  da sigar 👹 kan mutum, ba'a ganin jikinsa sai dai kai.  Kai👹 kawai ake gani.

Rannan Alhaji yaje zance kamar yadda ya saba. Suna hira sai yaga giftawar wani abu shuu! haka kamar inuwa, ya duba baiga komaiba, sai yace:

Alhaji:

"Wai bakiga komaiba kuwa? naga wani abu yana yawo a gunnanfa." Rufe bakinsa ke da wuya, bata kai da bashi amsaba, sai itama taga alamar mutum shu ya huce ta gabanta, sai ta firgita ta na neman guduwa.

Sailuba:

A gigice tace: "wayyo wallahi na ganshi,  meye kuma wannan?.  Kamarfa Sale nake nagani." Alhaji ya zaro ldo 👀 yana kyarma. Suka kaea ganin wannan inuwa tana gift asuu, sai kuma sukaji dariya, ta ko'ina.

Alhaji:

A gigice " To! Bari kigani guduwa zanyi, bazan iya da wannan lamariba." Sailuba na tsye tarasa ina zata, shi kuma alhaji ya nufi Motarsa zai hau, ya bude kofa murfin kofa ya koma ya rufe kansa.

Ya dawo da baya yana jin tsoro, yai karfin hali ya sake bude kofar amma taki buduwa, sai da kyar, ya samu ya bude sannan ya shiga ya ja, ya gudu ya bar Sailuba ta rasa hanya. 

Itama tana kokarin shiga gida ta rasa kofa, da kyar ta samu ta shiga, tana faman haki. Kaji yadda suka fara ganin abinda suka shuka.


● yan Daudu sun gamu da fatalwa 👹

Yan daudu sun  nufi gun da Sale yake liki, da nufin su yimasa tsiya, sai suka ga guri wayam ba kowa. Su basu san tuji alhaji ya shekeshiba.

Suna tafiya suna karai-raya wai su basu yadaba matane, guda daga cikinsu ya fara magana, wai shi Murja.

Mutja yace:

"Wai, ni yasu, ina wannan banzan mara rabo ya shigane?. "Yana magana yana tafa hannu, yana kama kugu.

Atine yace:

"Ai wallahi in akace mutum bashi da rabo ko a Tandun man sahanu aka sashi, ko kanshin man ba zai eboba haka zai futo."  Suna magana suna shewa suna tafawa. Harda rangada guda.

Ana haka sai kawai suka rika jin saukar mari, kota ina suka rika ihu suna gudu suna faduwa, sai kawai suka ga Kan 👹 Sale ya bayyana, yana ta kyalkyala musu dariya.

Suka tsaya, sun kasa gudu sun cukume juna, sai Sale yace:

Kan Sale: 👹

"Kune kanwa uwar gami ko? Kuka rabani da masoyiyata, kuka kaiwa Alhaji tallanta, to yau kashinku ya bushe, zaku gane kuranku." Sukai tsuru-tsuru, suna muzurai suka rasa abin fada.

Suna ihu dan Allah kayi hakuri, mun tuba mun bika kai mana rai, "wai gun bakowane? Jama’a ku kawo temako." Inji Atine. Sale yana ta kyalkayala musu dariya, aka cigaba da zabga musu mari tas, tas suka ranta ana kare wannan Kan  👹 mai suffer Sale ya bisu.

Kajj yadda suka kwashe da fatalwar Sale, maganin masu kai tsurku kenan.

● Sailuba na ba kawarta labari

Sailuba taje wajen kawarta Halima tana bata labarin yadda sukai da KAI 👹 mai suffar Sale. Sai Halima tace da ita:

Halima:

"To ni yanzu ya zan yimiki. Lokacin da nake fada miki gaskiya, ai kinki ji, kika  ce bakin ciki nake nuna miki, yo ni yanzu ya zanyimiki." Sailuba tana zaro ido tana jin tsoro.

Sailuba tace:

"To ya zaki dani ai kece kawata , dole ke zaki ban shawara, saboda in gayamiki ki ji, badamar na kwanta barci, sai kawai naji ana marina tas-tas. 

Aiko sai taji mari kas!, nan da nan ta fara ihu,ta buya a bayan Halima, tana cewa da Halima:  "gashinan abinda nake fada miki, sai takara jin mari fas!.

Halima tace:

"A ni ba abin da nagani, kinga ki futo ki tafi kawai kada nima ki jazamin." Sailuba tana ihu. "Dan Allah ki taimakamin ki boyeni wallahi mari nakeji kota ina." Ita dai Halima bata ga komaiba sai ta futo da Sailuba daga bayanta. 

Nan danan Sailuba ta futa aguje, tana gudu tana faduwa, ana ta zabga mata mari.

● Yaran Alhaji sun gamu da gamonsu

Yaran Alhaji, yana kwance a shagonsa,  daya daga cikinsu, sai yaga kofa ta bude, labule yana kadawar iska, sai ya tashi ya tura kofa. Kofa taki rufuwa, sai ya dan ji tsoro, sai kuma yaji ana ta kyal-kyala dariya 👹.

Sai fa hankalinsa ya tashi, sai kuma yaji an zabga masa mari, sai yasa ihu, sai kuma aka dokashi izuwa kan gadonsa ya fada dam!.

Tofa nan fa yarasa ya zeyi, sai mari ta ko'ina, ya ringa runtuma ihu, yayi-yayi ya futa ya kasa, sai ga wani kai 👹 ya bayyana  nan yaron Boss yaga siffar Sale a jikin wannan kai, yana ta masa dariya, da karfi, ko ina yana amsawa.

Da kyar yasamu ya futa ya ringa gudu, yana faduwa yana yana tashi. Yana cikin gudu sai yaci karo da dan uwansa, shima anbiyo shi, suka hadu sukai karo dam, suka fadi kasa.

Kai 👹yana biye dasu yana ta yi musu dariya, sunata jin ana marinsu, suka rasa ya zasuyi, suka kama bashi hakuri. 

"Dan Allah kayi hakuri kayimana rai muntuba bazamu sakeba."

Kai👹 mai kama da Sale:

"Lallai kun makara, da kunsan da Allah, kuka aikata abinda kuka aikata, bakin Alkalami ya bushe." Yana ta dariya ya muzurai, sukuma sunata ihun neman taimako, ba wanda yake jinsu.

Sai wannan Kan👹 ya bace, sai sukai hamdala suka tashi suna ta nishi, sukai murna, kawai sai yasake bayyana ai ko suka zuba da gudu Kai👹 ya bisu yanta dariya suna ta Shan mari ko ta ina. 

Kaji yadda suka kwashe da fatalwar Sale maganin masu zalinci kenan.


ALHAJI A GUN SAILUBA 

Alhaji a gigice yazo gun Sailuba don ganin ita ya take ya kuma bata labarin mutuwar  yaransa, domin shima yarasa yadda zaiyi, duk inda yake sai yaji ana marinsa, yazo gurinta don neman mafita.

Sailuba tace:

"Alhaji ka cuceni karabani da masoyina, har ankusa biki amma kazo kai min roman baki gashinan yanzu mun shiga halin yanzamuyi."

Alhaji:

"Banza sha-sha, ke baki da hankali. Ko dole nayimiki, ai da hankalinki, ke kika bi son zuciyarki, kika bi kudi." Suna ta musu a tsakaninsu, suma gayawa juna bakar magana, sai ga kan 👹Sale ya bayyana yana ta dariya, sai suka firgita sukai tsuru-tsuru, sukai tsit.

Fatalwar kan 👹Sale ta kama magana: "ai mune maganin mugaye,masu son zuciya, yau zaku girbi abinda kuka shuka." Sai dariya ha ha ha! Suna jinta kota ina, sai kuma aka kama marinsu tas-tas, suna ta ihu sunkasa guduwa ko ina.

Da kyar Alhaji ya samu ya gudu, ya bar Sailuba tana shan mari.Tai cikin gida da gudu Kai 👹 ya bita yanata dariya mai karfi.

Ta buya a bayan mamanta, Babarta ta firgita, ta gigice, sai ta tambayi Sailuba: "ke lafiya mai ya faru kike gudu haka?" Sailuba ta kasa magana tana buya a bayanta, sai umman tata ta fara jin mari tas-tas, kota ina marinta ake amma bataga kowaba.

Sai tace da Sailuba:

"Wai ke Sailuba baki da kunyane kike ta faman marina?." Sailuba tana boyewa tana kuka tace: "ai umma bani bace nake marinki nima marina ake tayi, sai ko taji mari a fuskarta har ta fadi kasa fam.

Suka ruku, juna suna ihun nai man temako, ba wanda yaji su bare yazo gurin. Sai ga kan 👹 Sale ya bayyana yana ta sheka dariya mai karfi, suka ganshi kiri-kiri, yana nufo inda suke.

Kan Sale ya ke magana:

"Yau kashinku ya bushe, marasa mutunci, ke Sailuba, kece kika kawo shawara a kasheni, to na mutu ke kuma keda jin dadi har abada." yana ta dariya sunata kuka gami da tsoro.

Sailuba:

"Dan Allah kayi hakuri ,kai min rai na tuba." Ana ta maka mata mari, ga dariya kota ina sunajinta, nanfa sailuba numfashinta ya dauke, sai uwar tata itama ta bazama, tana ta kyalkyala dariya ta kwance.

Duk abinda ake Baban Sailuba yana zaune yana ganin ikon Allah,yaki cewa komai. Domin tun a baya sun ki jin maganarsa, Kaji yadda su Sailuba suka kwashe.

● Alhaji zai gudu

Ya hau mota ya kama gudu, kan Titi wai shi zai tserawa wannan kan da yake binsu, yana tuki yana zabga gumi, sai kawai yaga wannan kan👹 a gaban motarsa yana ta dariya.

Alhaji ya hada birki kuuuu!, ya doka ribas, amma ina kai dai yana biye dashi, yayi-yayi yai gaba da Mota, amma Mota taki tai gaba an riketa.

Alhaji zai bude kofa ya futa, kofa taki budewa, sai dai dariya kawai ake masa, nanfa ya soma jin mari tas-tas, da kyar ya bude kofa ya soma gudu. Yana gudu yana faduwa shi kadai, kai 👹 dai yanata binsa.

Har yakasa gudu ya fadi yanta nishi, saiga kai👹 ya bayyana, ya tunkaro shi, Alhaji ya zaro Ido👀 yana nishi da kyar.👹 Kai ya tunkaro yana muzurai yace:

"Ka gama gudun, to ina zaka, ba inda zaka a duniyar nan ka gujemin, da, ma ka tsaya da yafi sauki."

Alhaji:

"Dan Allah kai min rai, na tuba nabi Allah, kada ka kasheni." Kai 👹yanata dariya, aka shake Alhajin nan kamar yadda yasa aka shake Sale, yayi ta murkususu har ya dena numfashi.

Kaic👹 yai tafiyarsa yana ta dariya, ya tashi sama fiiii!. Latsa nan  Don ganin wasu labaranmu

Kammalawa

Nan muka kawomuku karshen wannan labari. In mutum yaji wani abu da yai kama da halinsa, to badashi akeba, labarine kawai.

Darasi

< Darasin dake cikin wannan shiri mutane sudena hada baki domin yin kisa.

< 'Yammata su dena yaudara.

< iyaye subi gaskiya sudena bin ra'ayin 'ya'yan su.

< Allah ya ganar damu amin.


Tuntuba. 08148166212

Imel.  sadiku854@gmail.com  

Blogs.   nishadisport.blogspot.com 









Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

A chuci Mata-kashi na 1

DUKAN DUHU KASHI NA 2

An tarewa Sani hanya