LABARAN MAKO
GABATARWA
Salamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu mai kawo muku labarai, da al'amura na yau da kullum, wato nishadisport nine naku Sadik Yusuf har kullum da fatan kuna lafiya.
Kwamishina ya aje mukaminsa
Ga sharhin labaran dallah-dallah. Kwamishinan sufiri na jihar kano Ibrahim Namadi, ya ajiye mukaminsa na kwamishina bisa radin kansa acewarsa.inda yake cewa:
"na aje mikamina na kwamishinan sufiri, saboda na kare kima, da martabar Gwamnatin jiha kar kashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, saboda abin da yafaru dan gane da belin wanda ake tuhuma da aikata lefin safarar miyagun kwayoyi.
"hakan ta farune saboda banyi cikakken bincikeba, na karbe shi saboda haka na ga ya dace da nayi murabus, kuma na bawa al'ummar jihar kano hakuri da gwammnati, da yan jam"iya bisa abinda yafaru."
"Ina mika godiyata ga gwamna, saboda damar da yabani ta hidimtawa al'ummar jihar kano na gode."
Kuma ya kara da cewa "na yi farinciki da binciken da akayi, ya nuna ban karbi wasu kudi a hannun wanda ake tuhumaba, kuma bani da wata dadaddiyar alaka dashiba. "Kuma ina tare da gwammnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf zan cigaba da goya mata baya a kowane mataki."
● Gwamna ya amince
A nasa bangaren gwammna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da yin murabus din nasa nan take, in da yayi kira da kakkausar murya, kan mukarrabansa da sukula da amanar da aka dora musu.
"duka wanda ba zai iyaba, ya sauka domin hakan shi yafi dacewa, muna kira ga huku momi da su sauke nauyin da yake kansu."
Haka kuma ya yabawa kwamishinan Ibrahim Namadi kan gudummawar da ya bayar, a hukumar sufiri ta jiha ya nai masa fatan alheri.
Anyiwa 'yan uwan wanda suka rasu goma ta arziki
A wani labarin kuma, Gwammnatin Kano kar kashin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bawa yan wasan da suka rasa ransu su 22, wanda suka wakilci jihar Kano, a kakar wasa ta 2025 wanda aka gudanar a jihar Ogon dake kudancin kasar.
wanda a hanyarsu ta dawowa gida daga gasar, sukayi hadari, yanwasa da masu horaswa da mataimakansu,
Injiniyoyi, drabobi, sun kusa isa birnin Kano sukayi hadari, suka rasa ranu.
A yanzu gwamnati ta bawa iyalansu kyautar tsabar kudi har #5,000,000 kowannasu da kuma filaye, a sakamusu da gudunmawar da suka bayar. Haka iyalan sunyi godiya da wannan karramawa da akayimusu.
Yan siyasa basu da tarbiyya.
Sarkin kano Malam Muhammadu Sunusi Na II, ya zargi yan siyasar Nigeria da rashin iya Shugabanci, da kuma cinhanci da rasahawa,da rashin tarbiyya tun daga tasowarsu lokacin kuruciya.
Sunusi Lamido Sunusi na II
Da aka tambayeshi a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na channel, Sarkin yace: "da yawansu ba'a koya musu tarbiya tun daga tushe mafi yawa suna shiga harkar gwamnati bisa dalilai marasa kyau injishi."
"Ina ganin an rusa mafi yawan dabi'un kasar nan masu kyau, suna shiga ofisoshi ne bisa dalilai na kashin kansu. ba su da wani abin alfahari da suka ajiye"
"Da yawa suna sone su tara dukiya, da ya wan gidaje da jiragen sama, basa ganin mutane nayimusu kallon barayi,don haka sukula da hakkin mutane."
"Ba matsalar mutum guda bace, shugaban kasa ko gwamna hatta malaman addini, da sarakuna sun fada cikin wannan rudani."
Muna kira ga wayanda abin ya shafa da sukula da nauyin da ya rataya a kansu ko asamu cigaba.
Zaben cike gurbi a Nigeria.
A Nigeria za'a gudanar da zabe na cike gurbi, na wasu mazabu na yan majalisa inda 'yan siyasa suke kartar kasa wajen ganin sun lashe zabukan daban-daban.
Ita kuma hukuma anata bangaren, tazage damtse wajen ganin an gudanar da zaban lafiya, kamar yadda doka ta tanada. Inda aka baza jami'an tsaro wajen da abin yashafa suna ta rali, gamaiyyar jami'an tsaro irin su ' ●yansanda
● Civil defence
● sojoji
● custom.
Da sauransu.
A Kano anyi zaben a Tsanyawa, da kura, da garin Malam. inda 'yansanda suka kama kusan mutum dari uku, da muggan makamai, da bindiga mai sarrafa kanta, da kuma bindiga kirar gida guda shida, da irinsu Barandami, Fafalo, da Takubba, Adduna, ta bakin mai magana da yawun 'yansandan Nigeria reshen Kano Abdullahi Haruna Kiyawa.
Inda yace: "anyi ga garumar nasarar chafke wannan miyagun mutane, da abubuwa daban-daban, ciki harda ka yayyakin zabe da makamai, ana gudanar da bincike in an kammala za'a gurfanar dasu gaban kotu, kowa yagirbi abinda ya shuka." Injishi.
To Allah ya kyauta yakamata hukuma ta farka saboda lamarin yan bangar siyasa yana kazanta gashi yanzu harda bindiga a gunsu aka kamasu in abin yaci gaba to ba'a san abinda zai kasance nan gababa.
< wani jigo a wata jam"iya
Wani jigo a jam"iyar N N P P Buba Galadima, ya bayyana cewa bawata magana da akayi tsakanin Dr Rabi'u Musa Kwamkwaso da shugaban kasa Bola Ahamad Tinibu, ta cewa Kwamkwason zai yimasa aiki a zabe na gaba, yace:
"Tunda gwamnatin tarayya ta daurewa tsohon sarki Aminu Ado gindi, to bawata alaka tsakanin mu da Bola Ahamad Tinubu, tunda Abba Kabir Yusuf shine gwamna a halin yanzu kuma ya tube Aminu amma gwamnatin ta rayya tayi katsalandan kan lamarin."
Yayi wannan magana ne a cikin shirin siyasa na wani gidan talabijin inda ya chashewa gwamnatin tarayya.
Jihar rivers
A fagen siyasa dai, gwamnan jihar rivers Simalye fubgbara saura wata daya ya koma kan karagar mulki, inda jama'ar jihar suke fatan ganin ya koma kan kujerarsa yaci gaba da aiyukan da ya soma na cigaban jiha.
A watan bayane shugaba Bola Ahamad Tinubu, sanar da kafa dokar tabaci a jihar, sakamakon rikici tsakaninsa da wanda ya gada kuma uban gidansa na siyasa wato inwilson wike,
Sun dade suna takun saka tsakanin su, a Kan lamarin siyasa.
Allah ya kawo karshen wannan kulla- kulla a wannan jiha ta rivers, ko asamu cigaba da dai-daito a cigaba da aiyukan alheri, Amin. bbchausa
● Tsokaci
Amma akwai bukatar ayi karatun ta nutsu a harkar siyasa a Nigeria, saboda sau dayawa sai kaga ana rigaima a jiha daya tsakanin saban gwamna da tsoho.
Yawanci kuma sai kaga tsohon gwamnan ne ya dora sabo. Amma saboda wasu dalilai, ba jimaws sai afara rigima. Ko yan baranda na kowane bangare, su hada gitinar. Allah ya kawo karshen irin wannan lamura amin.
KAMMALAWA
Muna godiya ga dukkan masoya masu bin wannan shafi namu, mai rubutawa Naku, Sadik Yusuf.
Sai mu hadu a labarai na gaba da comment.
Tuntuba ta imel, sadiku854@gmail.com
Waya 08148166212
Na gode!
Sunusi kayi dai 'dai
ReplyDelete