Rikicin daba a kano
GABATARWA Rikicin ‘Yan Daba a Kano, a ga ya za'a kamo bakin zaran.Daga Sadik Yusuf, Kano Nigeria Zami duba da wannan matsala da kuma wasu al'amura na yau da kullum. Dafatan za'a kasance damu. Daga Sadik Yusuf – Kano, Nigeria Tuntuba: sadiku854@gmail.com Shafinmu: nishadisport.blogspot.com Abin Da Ke Faruwa a Kano Ya kamata mu fuskanci abinda ke faruwa mu fadawa kanmu gaskiya, game da matsalar da ke addabar jihar Kano – wato rikicin 'yan daba. Wannan matsala da take nema ta gagari Kundila ta shafi unguwanni da dama a jihar ta kano , kamar irinsu Dorayi, Sheka, Dala, Zage, Kofar Mata s harada, ja'in da kuma kurnar Asabe da dai sauran su. A bin yazama kamar annoba.Yara da basu kai shekaru 15 zuwa 18 ba suna haduwa suyi gungu suna fada a da makamai a tsakaninsu, suna kai hare-hare a inda suke so. Suna amfani da makamai masu hadari irin su adda, barandami, fafalo , da kuma kayan maye da suke shaye-shaye. Sau da dama. ...