DUKAN DUHU- NA DAYA

 Salam yan uwa masu bin wannan shafi namu na blogs, wato nishadisport munamuku maraba da sake saduwa, nine naku Sadik Yusuf,  ga sharhin shirin "Dukan Duhu."

A gidan su Sailuba Suna magana da Babanta da manta.

Umma tana magana tace:

 "Wai, ni, baban Sailuba, mai katanada dangane da bikin wannan yarinya Sailuba."

 Baban Sailuba yace:

"To,! Amma dai kinfi kowa sanin halin da na stinci kaina a yanzu ya kike so nayi, sata ko fashi" ta tari numfashinsa.

Umma:

"To,! duka, kaje kayi mana, ni dai kawai a wuyanka nake neman Gado da Kawaba ehe!" Nan ya yanke jiki ya fadi kasa tum, yasamu shanyewar barin jiki daman yana da hawan jini, ta kwalla kara! "Malam mai zan gani, inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.

 Sailuba tsaye da kawarta Halima 

Halima tace da Sailuba:

"Waike sailuba me kika gani ajikin wannan bakin matalaucin kika manne masa wai ke inba Shiba sai rijiya" ta tari numfashinta tace.

Sailuba:

"Ah!!, dakata✋️ bana san wulakanci saurayin danake mutuwar so zaki visa mutunci kamar batare muka taso dakeba." 

Halima:

 "Kai maida wukar🔪 daman ni ina miki kwadayin wanda zaki samu kihuta domin naga ke kalar manyace" Sailuba ta tashi ta  tafi ta barta agun.🚶‍♂️‍➡️

 Sailuba ta fadawa ummanta yanda sukai da kawarta

Umma tace:

 "Wato haka Halima zata rikayimiki ko?"

Sailuba:

 "Kyaieta umma kawai tana min bakin cikine da hassada gami da mugunta."

Umma:

 "Ai kawai gani tayi bata da mashin shini, shi'isa take miki haka amma ki barni da i'ta" shi dai Baban Sailuba yana zaune yana kallon su, ana haka sai sukajj yaro yayi sallama, "salamu alaikum" suka amsa.  "Wai ana salama da Sailuba" 

Sailuba:

"Wake salama"

Yaro:

 "Wai sale ne" sai suka ce: "kace tana zuwa." Yaro ya fita.
Ita kuma Sailuba ta tashi ta fita ta sameshi. Ta gaishe shi ya amsa.

Sale:

"Ai zuwa nayi na sanar dake cewa angama aiki komai yayi dai-dai, kawai abin da ya rage yanzu shine Fenty.

Sailuba tace:

 "Kai nayi murna kwarai da gaske da jin wannan labari kaga yanzu daman saura baifi sati biyuba a daura aure" tana ta murna da farinciki 👵. Suna ta hira cikin farinciki.
A wasu yan daudu sun ga Sailuba suka ga wannan yarinya bata dace da kowaba sai da wani Alhaji mutiminsu, suka ko garzaya domin bashi labari.

Yan Daudu sun je gun Alhaji domin bashi labari.

 Yan daudu:

"Ai alhaji yau muna da wani labari mai dadi da zai farantama, amma zaka bamu tikwici mai karfi."

Alhaji yace:

"Wane labarine wannan?🥸 har da sai na saya.  Yo ina jinku."

Yan daudu:

 Ai Alhaji wata zabgegiyar budurwa muka gani son kowa kin wanda ya rasa muka ga ba wanda ta dace dashi in ba kaiba,don haka bamuyi kasa agwiwaba muka zo mu sanarma." Alhaji ya gyara zama ya zaro ido👀, yace:

"Kai! Mutanena anan wannan ya rinyar ta ke ku kuwa?, nakagu dajin a' ina  take."

Yan daudu:

"Ai alhaji, ina mutuminnan wanda ya talauce, kuma yanzu ya kamu da rashin lafiya" "eh!, inji Alhaji" to ai 'yar sa ce, kuma ana sa ran ankusa aurenta" Alhaji ya zaro ido👀.

 Yace:

"To yanzu ga tikwici kuje ku shana kafin mu hadu" yabasu kudi har dubu ashirin, suka karba suna murna.

Saurayin Sailuba yana zaune suna zance kofar gidan su Ladidi, sai alhaji yazo ganewa idonsa labarin da aka bashi
ya tsaya daga nesa yana kallan yarinyar su basu san halin da ake cikaba, Alhaji ya karemata kallo, ya juya ya tafi abinsa.
 
Washe gari yazo kofar gidan, ya aika ayi sallama da ita tun daga cikin gida. ma haifiyar Sailuba taji wani kanshin turare ya daki hancinta.

Sailuba tace:

"Ni umma ba inda zani" umman dai kanshin nan ya firgita ta tayi shiru ta girgiza kai.

Umman tace:

Ke sailuba bakiji abin da najiba ne.? Sailuba ta kalleta "Umma ni banji komaiba" "to tashi kije kiga ko wanene"

Sailuba:

"To Umma,! nifa kinsan sai Sale" umma ta gyada kai "ke tashi kije" ta tashi ta fita, itama tana fita taji wannan kanshi ya daki hancinta, nan da nan sai jikinta ya mutu ta karasa a sanyaye tayi sallama, ya amsa.

Alhaji yace:

"Ah! Sailuba barka da fitowa dafatan kin futo lafiya." Ta kalleshi ta zuba masa ido.

Sailuba:

"To Malam, me ke tafe dakai." Tana sunkwi da kai. "Haba ki shigo cikin Mota muyi magana mana."

Sailuba:

"To ni inada wanda zan aura, saboda haka ni kaga tafiyata"
yabita kallo, yaga wani yaro ya kirashi ya bashi kudi ya kaimusu cikin gidan.  Yayi tafiyarsa.

Kudi zube gaban mahaifiyar Sailuba, tana ba Sailuba shawara kan ta amince da wannan mutimin da ya kawo mata wannan kudi duk da ankusa biki amma ba ruwanta.

Umma tace:

"Sailuba ahinda zan gayamiki ki bude kunnan basira kiji." Sailuba ta kalleta, tace: "inajinki Ummata." Umman tacigaba da cewa:. 

"Kinga ki manta da wannan matsiyacin saurayin naki ki auri wannan Alhajin kingafa mai kudine jibi kudin da yabaki." Ta nuna kudin da hannu. "Saboda kinsamu gurin hutu ki huta muma mu samu mu huta."

Sailuba:

"Haba umma yanzu haka za'a yiwa Sale, Umma kar ki manta idonki yarufe domin mutunci yafi kudi Umma." 

Umman tace: 

"to zauna kallon ruwa kwado yayimiki kafa ans gabas kina yamma me zakici da wannan mai likin tayar me nasama yaci balle yaba na kasa kullum kina gani yana tafiya da kyar da wani tsohon Keke riga duk ta kode yana zabga uban wari."

Sailuba ta shiga tinani tana zato ido gami fa mamaki ta tashi ta shiga daki ta zauna a gefen Gado tana tinani🧕.

Sale kofar gidan su Sailuba:

Yasa wayarsa mai kyuro ya kira Sailuba, amma bata futo dawuriba kamar yadda ta saba yana tsaye da dan kekensa 
yana ta gumi gami da hamma. 

Chan saigatan tana yauki tana tafiya a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta tahe ya zuba mata ido har fai ta karaso ta tsaya kerere ko gaisuwa babu, yana kallon ikon Allah yau yaga abinda bai taba ganiba a gunta.

Sale:

"A masoyiya yau lafiya kike kuwa."?

Sailuba:

"Lafiya kalau nake babu abinda yake damuna." Tayi shiru bata sake cewa komaiba. Shima yayi shiru yana kallon ikon Allah.

Sailuba Tace: 

"To in baka da abin fada ni zankoma gida domin ina da abin yi Ummata ta sani aiki.

 Shidai yana kallon ikon Allah yakasa cewa komai domin yaga gagarimin chanji. Takada kai ta tafi. Shima ya dau kekensa yayi gaba gwiwa a san yaye.



 Nan muka kawomuku karshen kashi na 1 sai abiyomu zuwa kashi na 2 naku Sadik Yusuf. 

A tuntubemu ta imel, sadiku854@gmail.com 
Na gode!.








Comments

Post a Comment