mahaukaci da soyayya
GABATARWA
Salamu alaikum Masu binmu a wannan shafi muna godiya da bamu hadin kai. A YouTube da kuma a shafin nishadisport.blogspot.com.
Wannan labari na Yar Malam kirkirarren labarine da aka yishi ta hanyar film don fadakarwa ba don waniba. labarin a kwai muhimman jarumai da suka taka rawa acikinsa lallai zaku ce na gayamuku. Mai rubutawa Naku Sadik Yusuf mungode!
Sharhin Shirin Yar Malam — MAHAUKACI DA SOYAYYA
Assalamu alaikum, masu bibiyar tashar NishadiSport!
Madalla da kasancewa da mu a cikin wannan shiri na Yar Malam.
A yau za mu duba abin da ke faruwa a cikin sabon sashe, inda mahaukaci dan gidan mai gari ya shiga wani hali saboda soyayya.
Mahaukaci ya tinkaro kawa
Mahaukacin nan dai ya makale da son kawar Ladidi, yana yawo lungu da saƙo yana nemanta. Kamar wanda akace matar sa ta gudu yake yawon nemanta. Idan aka tambaye shi, yana cewa, “Ni dai sai na aureta!”
Kuma in kana gaban sa ka ƙi gaya masa inda take, toh, ko dai ya buge ka, ko ka yi gudun tsira da ranka.
* Kawa ta shaida wa Ladidi halin da take ciki.
Ladidi tace:
> "Lallai wannan ba ƙaramin lamari bane abin a dubane. Wannan mugun mahaukacin da nasani me bugun mutane shine zai ce wai yanasanki." Kawa cikin damuwa.
Kawa ta tambaye ta?:
> "To, me za mu yi? Shawara nake nema awajenki. Ya zanyi da wannan al'amari." Ladidi ta numfasa alamar tana nazarin me zatace.
* Ladidi ta ba ta shawara:
> "Toh! Abinda zangayamiki ki nemi taimakon Allah, addu’a ita ce mafita. Nima addu'a, ita na rike na koma ga Allah shine nasamu sauki a gun mugayen mutanen nan, Dogo da Babansa,don haka kema ki rike addu'a."
Kawa ta tsaya tana nazarin maganar Ladidi, tayi shiru Ladidi tana sauraronta Suna cikin tattaunawa. Kafin su gama magana, sai ga mahaukaci ya bayyana, Suka kama tsorata da ganinsa.
Kawai sai kawa ta ce:
> "Hasbunallahu wa ni’imal wakeel!" Suna kallon juna. Sai
Mahaukaci ya durƙusa yana gaida su, ya zuba musu ido.
Mahaukaci:
"Ina wuni ina gajiya,kuna lafiya?"
Nan suka kalli juna suka yi mamaki, nan da nan suka amsa masa: "lafiya lau."
Suna muzurai na jin tsoro suna ja da baya, shi kuma yana matsosu, suka samu suka fice.
Mahaukacin kuwa ya tafi yana dariya, yana waige.
Sai ya tafi yin tunani wai sun yi aure kuma matar tasa ta samu ciki. Yana tunanin zai kai ta asibiti, akan doki!. Dokin kuma na kara, yana ta cewa ta hau, ita kuma tana ta runtuma ihu yanacewa:
"kizo ki hau inkaiki gun idi likita" ya nata washe baki itako tana rike kugu gami da ihu.
Sai yadawo daga wannan tinani Amma sai yaga mutimin da yake firgita shi,wato Sani – dodonsa!.
Aiko ya shige da gudu kamar wanda ya ga mala'ikan mutuwa. Yana gudu yana faduwa yana tashi. Har ya kule.
* Ya kuma haduwada Sani.
Sani da kawa suna nan suna hira, akan matsalar Ladidi suna dariya,shi kuma mahaukaci ya tunkaro wajen,sai ya tsaya, a chan nesa yana hango su yana cizon yatsa saboda haushin ganin su tare.
Shi kuma Sani yana tambayar kawa inda Ladidi take. suka manta da mahaukaci.
Kawa ta ce:
> "Baban ta ya hana ta fita, kuma ya hana kowa zuwa wajenta. Yanzu tana tunanin guduwa daga gida."
Sani ya ce:
> "Ai guduwa daga gida ba mafita bane. Ki ci gaba da lallashinta. Allah yana tare da masu haƙuri."
Kawa ta ce:
> "Zanyi iyakacin ƙoƙarina inga na hanata guduwa, tunda tana jin shawarata, duk garin bata da abokiyar shawara kamar ni."
A gefe guda kuwa, mahaukacin yana nan yana kallonsu daga nesa. Tsoron Sani ya hana shi kusantarsu.
Shi mahaukaci, shine wanda da an ganshi ake gudu amma kuma shima yashiga tsoron wani , yanzu shi ne ke buya.
LADIDI ANA TUHUMARTA
Itako Ladidi tana chan gida,Malam idi yana tuhumarta a kan cewa ta dauke masa kudi, kuma ba ita ta dau kudinba, kawai sharrine irin na karan tsana, ladidi tana, kuka tace:
"Wallahi Baba bani na dauki wannan kudin ba,ban shiga dakin kaba." Ya daka mata tsawa ke!.
Malam Idi:
"To in ba keba waye ya dauka sai kigayamin, shin mu nawane a gidan." Inna tana ko karin magana amma yana katseta ya hana ta magana. Tayi Ta maza dai tace:
Inna:
"Malam ba ita ta daukaba" yai farat yace: "To ke kika dauka da zakice ba ita bace." Tace: "a a bani bace."
Ya hana ta magana, ita kuma inna sai ta tuna taga Dogo ya fito daga dakin, amma bataga meye a hannunsaba, tana tsoron magana tayi shiru da bakinta ta zurawa sarautar Allah ido.
Malam Idi yace da Ladidi, ta fita duk inda kudi yake ta samo ta kawo in bahakaba sai na lahira ya fita jin dadi. Ladidi ta tashi ta fita ta bar gidan cikin kuka da dimuwa.
* Ladidi ta hadu da Soja
Tana kuka ta hadu da soja, yake tambayarta ko lafiya?
Ladidi tace:
"Wallahi babane ya kalamin sata, wai ya aje kudi na dauke, ni kuma bani bace." Shi dai soja ya tsaya yana kallonta.
Soja:
"Kai aiko baki kyautaba" ta daga kai ta kalleshi, "anan banga laifin Malam Idi ba, ai Babankine don haka kiyimasa biyayya kuma sata bata da dadi, don haka ki chanza hali."
Tayi mamakin yadda soja ya goyi da bayan Malam idi, al hali ya san halinsa, kuma shi ne take zaton zai sama mata lafiya,amma ya buge da nuna cewa ita, ta dauki kudin, kaka tsara kaka, gaba kura baya siyaki.
* Ta hadu da Munzali Gurgu
Tayi gaba tana kuka sai kuma ta hadu da Munzali gurgu, shi kuma yana ta tambayarta ko mai ya faru take kuka. Taki tsayawa ta bashi amsa, domin bai isheta kalloba.
Gurgu:
"Dan Allah ki tsaya, meke faruwane waye yataba ki a garin'nan? ki fadan ko waye zan miki maganinsa." Ita dai tana kuka bata tsayaba, taci gaba da tafiya. Munzali Gurgu yace:
"wato inaji saboda banzan mutuminnan, shiyasa take kin kulani amma lallai zanyi maganinsa mara mutunci.
wannan fa shine batan basira ga wani yana nemanka kai kuma kaki ka bashi hadin kai, sai dai wanda bai damu da kaiba shi kake hari, haka duniya take.
● Karshen Wannan Kashin kenan, shin mahaukaci zai iya cimma burinsa na soyayya?
● Shin Sani da Ladidi za su samu soyayya lafiya?
Shin baban Ladidi zai sauya matsayinsa?
KAMMALAWA
Karshen wannan sharhi kenan inda kuka ji yadda Mahaukaci ya ke bibiyar wata Budurwa da sunan so ko ya haka zata yiyu, kubimu a shiri na gaba. Mun gode!
ILMANTARWA
Akwai nishadi aciki, kana kuma da wa'azantuwa, inda inna take kokarin ganin ta taimaki Ladidi daga matsin da su Dogo suka sata, wannan hali nata abin koyine.
Ku kasance damu don ganin yadda shirin zai cigaba. (Ku shiga cikin shafin don duba abubuwa na baya)nishadisport
Ku biyo mu a tashar YouTube ɗinmu 👉 NishadiSport
Kuyi Subscribe, ku bamu like, da sharhi. Muna godiya da kasancewarku tare da mu!
rubutawa: Sadik Yusuf
📍 nishadisport.blogspot.com
Tuntuba, sadiku854@gmail.com
Mahaukaci kana da siki
ReplyDeleteMuna godiya
ReplyDelete