Yar Malam – Cigaban Labarin Ladidi da Rikicin Gida
Ladidi a cikin shirin Yar Malam – tashar NishadiSport Yar Malam – Cigaban Labari (Sharhi daga Sadik Yusuf) Assalamu alaikum masu sauraronmu, Muna ci gaba da kawo muku sharhi kan shirin Yar Malam , wanda yake fitowa a tashar NishadiSport a YouTube. Ni ne naku, Sadik Yusuf daga Goron Dutse, Kano State . Ladidi cikin Hawaye da Juyayi Ladidi na zaune cikin kuka da damuwa kan rasuwar mahaifiyarta. Kwatsam sai ga Inna – mahaifiyar Dogo – ta shigo, ta yi sallama. Ladidi na ganin Inna sai ta taso daga kan kujera fuska cike da hawaye.Tana ganin Ladidi na kuka, sai ta rungumeta tana bata hakuri. Ladidi tace: "Inna, sun kashe ta sun huta." Inna tayi turus ta dago Ladidi daga kafadarta. Inna ta ce: "Wa ya gaya miki haka? Ai babu tabbaci. Ki dena fadin haka tun da baki ganiba Kuma kuma zargi bashi da dadi." Ladidi cikin kuka tace: t" nan fa suke kokarin bata guba ta sha bata dhaba Allah ya kareta to gashi yanzu ta mutu." Inna fai tana bata hakur...