Yar Malam – Cigaban Labarin Ladidi da Rikicin Gida

    
Ladidi a cikin shirin Yar Malam – tashar NishadiSport

Yar Malam – Cigaban Labari (Sharhi daga Sadik Yusuf)

Assalamu alaikum masu sauraronmu,
Muna ci gaba da kawo muku sharhi kan shirin Yar Malam, wanda yake fitowa a tashar NishadiSport a YouTube. Ni ne naku, Sadik Yusuf daga Goron Dutse, Kano State.


Ladidi cikin Hawaye da Juyayi

Ladidi na zaune cikin kuka da damuwa kan rasuwar mahaifiyarta. Kwatsam sai ga Inna – mahaifiyar Dogo – ta shigo, ta yi sallama. Ladidi na ganin Inna sai ta taso daga kan kujera fuska cike da hawaye.Tana ganin Ladidi na kuka, sai ta rungumeta tana bata hakuri.

Ladidi tace:

"Inna, sun kashe ta sun huta." Inna tayi turus ta dago Ladidi daga kafadarta.

Inna ta ce:

"Wa ya gaya miki haka? Ai babu tabbaci. Ki dena fadin haka tun da baki ganiba Kuma kuma zargi bashi da dadi."

Ladidi cikin kuka tace:

t" nan fa suke kokarin bata guba ta sha bata dhaba Allah ya kareta to gashi yanzu ta mutu." Inna fai tana bata hakuri. 

Inna tace: "to amma babu tabbacin cewa sune ko? to Allah ne yaui kwananta ya kare kuma don Allah kukan ya isa haka." 

Daga nan sai Inna ta sanar da ita cewa Malam Idi ya ce ta koma gidansa da zama. Ladidi da jin haka tayi shiru tsit sai ta sake barkewa da kuka. Ladidi ta ce:

"Inna, ta yaya zan koma gidan Malam Idi? Nan ma da nake ya na cika balle na koma gidansa da zama waiyo na shiga uku na lalace!" Taci gaba da kuka Inna tana lalashinta.

Inna ta tausaya mata, ta ce:

"Ba komai ni ina tare dake zan rike ki tamkar 'yar da na haifa a cikina, kar kiji komai tunda Kin rike Allah, komai zai wuce in Allah ya yarda." Ita dai Ladidi tana kuka. Inna tacigaba da cewa: 

"Ki tattara kayanki in Allah ya kaimu gobe zan zo mutafi kinji Ladidi dena kukan haka ya isa." Ta lallasheta ta yi shiru kana inna ta tafi, Ladidi ta koma kan kujera shirim ta zauna.


Rayuwar Ladidi Cike da Kalubale

Ladidi ta ji kamar an yi mata hukuncin mutuwa ne – ace ta koma rayuwa da Malam Idi bayan duk wahalhalun da ta sha? Ga Dogo, duk da cewa Inna ta ce zai kula da ita, amma ta san Malam Idi ba zai taɓa yin  sauƙi ba.

Haka tana wani wajen ana mata barazana bare ta koma kusa dasu.

Yanzu dole ne Ladidi ta fuskanci wannan ƙalubale, domin Dogo zai bi umarnin mahaifinsa. Yaya za ta kare kanta? Daga masifarsu. Sai mu saurari cigaban shirin mu na Yar Malam

Kawa tazo gun Ladidi 

Kawa tazo gurin Ladidi tasa meta tana tagumi a kan tabarma tayi sallama,Ladidi ta amsa, dai kawa tace:

"Ladidi me ke faruwa na ganki haka kamar kina kuka."

Ladidi:

"Wallahi kinga ina nan abin duniya ya isheni shi isa kj ka ganni haka." "To kamar mefa?" Inji kawa: Ladidi tace: 

"wai gidan Malam Idi zan koma da zama." Kawa ta jinjina lamarin ta tausaya mata sai ta girgiza kai, tace:

"Ai bakomai tunda haka aukace, kuma a yanzu sune iyayenki ba yanda zaki dasu don haka kiyi hakuri kawai" kawa ta rungumeta tana lallashinta.


Ladidi Ta Fuskanci Wulakanci

Kafin Ladidi ta koma gidan Malam Idi, sai Dogo ya zo ya koreta dagagwain. Ya ce, wai ya kawo mai haya – ta fice kawai ta bar gidan duk inda zata ta tagi tunda ance ta koma gidan Malam Idi taki.

Ladidi ta sha mamakin irin wannan cin mutunci. Gidan da ubanta ya bari ne, amma sun mayar da ita tamkar ba komai ba. 

wannan cin mutunci dame yai kama ace marainiya da gidanta amma a koreta saboda son zuciya kawai.Wane mugun hali! ne wannan haka A haka ne har suke so ta koma chan gunsu da zama.


Sani Na Neman Gidansu Ladidi

A gefe guda kuma, Sani yana can yana neman gidansu Ladidi. Ya haɗu da kawarta kuma ya na  tambayrta?

Smi:

"ah! Ba ke bace ba rannan muka hadu kika kama ?" Wai yo hudun me kikeyi?ç

Kawarta tace:

"Eh ni ce, saboda na dauke ka kamar yaran Dogo shi isa nake gudu ."

Sani yace:

"A'a, ni fa ba tare nake dasuba. Nazo ne domin taimakon Ladidi bisa umarnin mahaifina shine nake neman gidansu."

Kawar tace:

"Haka ne. Amma ka sani, mahaifin Ladidi ba zai kyaleka ba – musamman idan ya san kana da niyyar taimaka mata." Sani yayi ajiyar zuciya 

Duk da haka, Sani ya nace:

"Ba matsala. Zo ki nuna min gidan nasu." Kawa ta jinjina lamarin saboda itama tsoronsu take ji fon sun sata aiki takiyi, haka dai ta daure suka danna.

Yayin da suka tafi, sai suka ci karo da Dogo da Magatakarda da sauran yaransu. Kawar ta tsere, Sani kuma ya tsaya.

Dogo ya ce:

"Kai Malam, ka bar maganar Ladidi, ko kuma mu hallaka ka. Duk yaran nan nawa ne – abin da na ce su yi, shi suke yi." Sani yayi murmushi. Ya tsaya

Sani ya kara yin dariya ya ce:

"To mu zuba mugani shege kafasa yanzu gani! Sai kuyi abinda zakuyi"
Ya juya ya tafi, ya bar su suna dukan iska.


Malam Idi Ya Fusata

Dogo ya koma gida ya sanar da mahaifinsa, Malam Idi. A nan ne Malam Idi ya fusata sosai, ya shiga yana zagin Ladidi.

"Kar inji, kar in gani! Kin kawo mana wani bako? Wallahi sai na hana ki fita daga gidan nan!"

Ladidi dai kuka kawai take, bata da inda zata je. Ta tafi wurin Inna, wadda ta rarrashe ta da cewa:

"Komai yai zafi, maganinsa Allah ne kiyi hakuri yanzu ki tashi ga abinci chan ki dauka ki ci kinji 'yata." Ta tashi ta dakko abincin ta zauna tana ci a hankali tana kuka.


Karshen Sharhi

Haka dai ake cigaba da fafatawa a cikin wannan shiri namu mai ban sha'awa, Yar Malam, wanda ke fitowa a tashar mu ta YouTube – NishadiSport.


Ku Ci Gaba da Kallo!

Ni ne naku, Sadik Yusuf.
Zaku iya tuntuɓata ta imel: sadiku854@gmail.com
Ko ku ziyarci shafinmu: nishadisport.blogspot.com


Comments