’Yan uwa masu sauraro da masu bibiyar shirye-shiryenmu, muna yi muku fatan alheri.da samun nutsuwa.
Ni ne naku Sadik Yusuf, kuma ga labarai dallah-dallah kamar haka:
🔻 Ragin Farashin Mai daga Matatar Dangote
An wayi gari da rage farashin mai daga matatar mai ta Dangote, inda aka rage daga ₦840 zuwa ₦820.
Wannan ragin ya fara aiki nan take, bisa dalilin faduwar farashin danyen mai a duniya, da kuma kokarin matatar wajen ganin jama’a sun samu sauki domin inganta tattalin arzikin al’umma.
Dominmutane suna fama da tsadar rayuwa ragin man zai dan rage musu radadi.
🔻 Ra’ayoyin Jama’a
A nasa bangaren, al’ummar Najeriya na nuna murna da wannan sauki.
A cewar wani mazaunin Kano, Isyaku Sani, ya ce:
“Allah ya sa wannan rangwamen ya dore domin in an samu ragi masu gidajen mai basa ragewa ammada zarar anji kari nan da nan sai sukara.”
Allah ya sawaka muna fata musamu saukin gudanar da rayuwa in man ya sauka to ya kamata mutane suma anasu bangaren su rage.
🔻 Sanata Natasha Akpoti Ta Janye Komawarta Majalisa
Sanata Natasha Akpoti, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta sanar da janye niyyarta ta komawa Majalisar Dattawa.
Wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta, inda ta bayyana cewa ta yi tuntuba da lauyoyinta wadanda suka bada shawarar ta dakatar da komawar, duk da umarnin wata kotu da ta jingine dakatarwar da aka yi mata har na tsawon wata 6.
Ta ce za ta sanar da sabon lokaci idan lokaci ya yi. Saboda haka magoya baya su yi hakuri su kwantar da hankalinsu zata sanar da wani lokaci nan gaba don asamu kwanciyar hankali a kasa baki daya.
🔻 Sabuwar Jam’iyyar Kawance don Yakar Gwamnatin APC
’Yan adawa daga Arewa da Kudu sun kafa sabuwar jam’iyyar kawance don tunkarar gwamnatin APC a zaben shekarar 2027.
Sun zargi gwamnati da gazawa a fannonin:
- Tsaro
- Tattalin arziki
- Da jagoranci na gari, gaba É—aya
Wasu tsofaffin ministoci da gwamnoni sun shiga wannan hadaka, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wani minista ma ya bukaci su hakura har Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu kafin su nemi takara.
🔻 An Hana ’Yan Gwan-gwan Sana’ar su a Kano
A Jihar Kano, an fara kama masu sana’ar gwan-gwan (jaribola), musamman masu tsintar kwali da leda.
Kungiyar su ta kasa reshen Kano ta koka da yadda ake gallaza musu wajen gudanar da san'ar saboda da itane suka dogara wajen gudanar da rayuwa.
Sun roki gwamnati ta shiga tsakani domin kare ’yancinsu.
🔻 Amurka Ta Rage Yawan Bizar da Ake Baiwa ’Yan Najeriya
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dauki matakin rage yawan biza da ake baiwa 'yan Najeriya.
Yanzu haka, bizar da ake bayarwa ba ta diflomasiyya ba, za ta kasance na tsawon wata uku kacal, kuma hakan domin rage yawan kwararar mutane zuwa Amurka.
🔻 Rikicin Sarautar Kano: Kiran Sulhu daga Dattijo
Wani dattijo mai suna Hamza Darma, ya roki Gwamnatin Kano ta dawo da zaman lafiya bayan rikicin sarautar Kano da ya kunshi sarki biyu — Aminu Ado Bayero da Sanusi II.
Ya bukaci gwamnati ta mika sunayensu ga shugaba Bola Ahamad Tinubu don yayi musu ambasada ga sarkin da aka sauke su samu matsayi a waje, sannan a sanya Sarkin Bichi – Nasiru Ado Bayero – a matsayin sarki na Kano, domin a samu dorewar zaman lafiya.
Darma ya kara da cewa rikicin na iya zama gagarumar fitina, musamman ganin yadda:
- Masu jajayen hula ke bin hakimai
- Harin da aka kai gidan marigayi Aminu Alhassan Dan Tata
- Harin da aka kai gidan sarki, Kofar Kudu da fashe motocin jami’an tsaro wurin
Ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya dauki mataki cikin gaggawa.
Tsokaci.
Gaskiya yakamata gwamnati ta saurari shawarar Hamza Darma, da ya bayar na a sauke sarki Sunusi Lamido da kuma Sarkh Aminu Ado, domin samun dai-daito a harkar sarauta a Kano.
Domin lamarin yana nema ya haifar da wata matsala wadda shawo kanta zai wahala idan ta barke,saboda in akai duba da abin da yake faruwa zaga magoya bayan bangarorin guda biyu suna kaiwa juna hari ana samun arangama a tsakani.
Haka wani lokaci da Aminu Ado yadawo daga wani guri yabi ta kofar Kudu,aiko sai mabiyansa suka farwa jami'an da suke aiki a gun suka far fasa motocin jami’an da suke bakin aiki, to yanzu meye anfanin wannan? kuma me hakan zai haifar.
Don haka gwamnati ta farka tai maganin wannan lamari Tun kagin ya gagari kundila, domin abin yana taba martabar Kano,Allah ya kawo sauki amin.
AL MAJIRAI
Kwararar Almajirai zuwa birni
A kwai wani lamari kuma da yake ciwa mutane tuwo a kwarya, na almajirai da suke bara kwararo-kwararo titi zuwa titi yara da manya tsofi da mata.
Musamman ma mata sune sukafi yawa a wannan lamari mai tayar da hankali, wasu kuma yaran iyayensu ne suke kawo su wai dasunan karatun (Allo).
Abin tausayi zakaga yaro yana ta yawo yana cewa atemakamasa zai ci abinci wani gun a bashi wani gun kuma a koreshi,yanzu a wannan rayuwa da muka samu kanmu a ciki a taya yaro zai koshi da abinci,ga bawajen kwana mai kyau,ba magani in mutum bashi da lafiya.
Yaya yaro zai tashi da jinkan ma haifansa,yan da kyau iyaye su sauke nauyin da Allah ya dora musu in bazasu iyaba to kada su haifa shine mafi dacewa.
In zai yiwu gwamnati ta dauki mataki na hana kawo yara zuwa vikin birni domin yin karatu da sunan addini duk wanda ya ketara doka a yimasa hukunci ko a samu al'umma mai inganci anan gaba,wannan shine abinda ya dace,kuma shawrace ga gwamnati.
🔚 Kammalawa
Mai rubutu: Sadik Yusuf
Za a iya tuntubarmu ta:
📧 Sadiku854@gmail.com
📱 WhatsApp: 08148166212
🖥️ http://nishadisport.blogspot.com
Na gode da sauraronku. Allah ya kare mu baki daya. Ameen.
Yayi shafin nan
ReplyDeleteGwamnati ki kula
ReplyDelete