๐ฌ Yar Malam – Season 1, Episode 7
Sharhi daga Sadik Yusuf
Tashar: NishadiSport (YouTube)
Assalamu Alaikum warahmatullah!
Ni ne naku, Sadik Yusuf, nake kawo muku sharhin shirin "Yar Malam" wanda ke gudana a tashar NishadiSport.
A yau zamu ci gaba da yadda al'amura ke tafiya a season 1, episode 7. Ku biyomu ku ji yadda za ta kaya tsakanin Dogo, Gurgu, da sabbin mutanen da aka kawo cikin rikicin.
๐น Rikici tsakanin Dogo da Gurgu
An fara da yadda abokin su Dogo wato Gurgu ya kawo musu wasu zababben yara daga birni. Wanda suke marasa kunya, marasa mutunci, kuma basu da tsoro. Zababurawa kenan yan birni.
Watarana, sai Baba ya tura su domin su chasha Soja, wanda shi ne makiyinsa.suna takun saka saboda rashin gaskiya da kowa yake kokarin danne 'dan uwansa.
Suka danna domin neman Soja,suka shiga gari suna nema,
sai Soja ya hango su tun kafin su iso, suna tare da wani abokinsa sai ya gudu ya buya sukai neman duniya basu ganshiba amma shi yana ganinsu.
Sai suka dawo gun wannan abokinnasa suka tambayeshi:
"Kai ina Soja ko kaga inda yayi?" Yana kyarma abokin nasa sai yace:
jiki yana rawa yana inda-inda "eh a ban ganshiba" suka daka masa tsawa kai!!. Sai sukayimasa kashedi cewa ya gayawa Soja in yasake suka hadu to kashinsa ya bushe, shi dai abokin nasa ya rufe fuska domin yasha mari, suka tafi.
Soja Ya gayawa dansa
Sai Soja ya samu dansa, Gurgu, ya gaya masa halin da ake ciki.na 'yan dabar da suke nemansa zasi masa duka.
Soja:
"Wato Munzali wasu yarane marasa mutunci sike nemana zasu min rashin kunya shine kaga ina sauri haka."
Munzali gurgu:
"Wane yarane kuma haka anan garin?" Soja yana waige sai yace: "wasu marasa kunyane nima ban sansuba."
Gurgu ya yi kwafa. Yace: "aiko akwai wasu yara zan turoma su fomin su baka kariya." Yauwa ka hanzarta inji Soja.
Gurgu yatafi domin ya gayawa Dogo.
Gurgu ya tafi da sauri ya gaya wa Dogo halin da ake ciki. Su Dogo kuma sun kira yaran da Gurgu ya kawo musu domin su tafi tare da shi. Suka tafi domin neman wanda suke neman babansa wato soja.
Dara taci gida ashe sune dai suke neman sojan baban gurgu sai muga ya abin zai zama muje zuwa mahaukaci Ya hau kura.
๐น Gano gaskiya: Soja uban Gurgu ne!
Da suka tafi tare da gurgu domin ya kaiwa soja su sai a bin ya juya. Abin mamaki, aka hadu da soja fa yaran Dogo suka ga mutumin da suke nema, Soja, shine uban Gurgu!
Aka yi carko-charko, lallai wannan shine ake kira, Dara taci gida! Ana kallan kallo kafin kowa yayi magana.
Soja:
"Munzali me ya hada ka da wannan marasa mutunci?" Ai sune nake baka labari suna nemana." Munzali ya kallesu.
Sai babbansu yace:
"Au tsohon ka ne? To ai mu Baba ne yace mu dakeshi." Soja yana kallon ikon Allah.
Munzali:
"baban nawa zaku daka to danme?" Suka kalleshi suka daka masa tsawa kai! Sai muhada har kai mudaka, gurgu ya samu ya lallabasu domin yaga bazai ja dasuba a wannan kadami suka samu suka tafi.
Yaran suka koma suka shidawa Malam Idi abinda ya faru. Tsakanisu da gurgu.
Idi yace :
"To, dan me ba za ku kaddamar masa ba? Ko don yana da nasaba da Gurgu ne? Zan gayawa Dogo, domin ya san abinda kuka aikata. Idan har bazaku yi aiki ba, zamu kore ku daga garinnan mu kawo wasu su maye gurbin ku mutanen banza nan."
Yana ta fada ta inda yashiga ba tanan yake fitaba.
๐น Gurgu ya kai ฦara gurin Maga Takarda
Gurgu ya je gurin Maga Takarda ya kai ฦara cewa yaran da ya kawo su aka tura domin a daki Soja, kuma soja ba banane kada a sake tabashi, domin shi ya haifeni.
Dogo yace:
To sai me ai ya kusa kashe min mahaifi don haka uba baifi ubaba. Gurgu ya taso shima doya taso zasu kaure da fada
Dogo ya daga hannu zai kai masa hari, amma Maga Takarda ya shiga tsakani ya ce:
"Ba wannan ne ya hada mu ba. Ku mayar da wuka cikin kube." Har an chukume za kaure.
Dogo ya ce:
"Uba ba fiye da uba ba! Shi ya kusa kashemin mahaifi, ai sai na dauki mataki!"
Maga Takarda ya raba su, Gurgu ya tafi cikin takaici.
๐น Yaran da Gurgu ya kawo sun fi ฦarfin sa
Yanzu Gurgu ya gane cewa yaran da ya kawo daga birni sun fi ฦarfin sa.
Sun fi biyayya ga Dogo da Maga Takarda, da kuma Baba.
Har tuna birni ma sun daina, suna rayuwa cikin mugunta da rashin tsoron Allah. Wannan shine kaikayi koma kan mashekiya, ka kawo mutane sunfi karfinka.
Gurgu yana kallo yana kuka, amma ba yadda ya iya.
๐น Soja da Gurgu sun tattauna
Soja, mahaifin Gurgu, ya tambaye shi:
"Wane irin abune ya hadaka da wadannan yaran marasa tsoron Allah? Kuma nayi mamakin wannan lamari."
Gurgu ya amsa:
"Su suka bukaci na kawo musu yara wanda zasu karesu daga dharrin wani wanda zai kawomusu cikas cikin lamarinsu." Yana saura ronsa Gurgu yaci gaba da magana:
"Kuma ni Ladidi nake so – ’yar uwar Dogo. Amma tana wulakantani saboda shi wanda suke so a daka yana hanata ta kulani ni kuma dana ga haka sai nayi kaimi da kawosu Don suyi maganin sa wannan shine dalilin haduwata dasu." Soja yaui murna da jin haka.
Soja yace:
"To yanzu na fahimta. Amma Malam Idi ba zai saurare mu ba. Yakamata mu shirya yadda za mu tinkare shi kasan bama shiri da shi amma kacigaba." Da nema nima zan je gun Malam Idi naga yadda abin zai kasance."
Munzali yace:
"Ni dai Baba, ina son Ladidi. Ko me za a yi, asa Malam Idi ya amince." "Bakomai Kawai kasha kuriminka indai inanan komai zai tafi dai-dai" inji Soja.
๐น Rikici a gidan Malam Idi
Gurgu ya tafi gidan Ladidi. Bai jima da zuwa ba sai ga Malam Idi ya fito.
Yayi masa mugun fada, har ya ce:
"Ni Ladidi nake so, ko da zan rasa raina!" Inji gurgu
Malam Idi yace:
"Sai ka rasa ran naka. Wadanda ka kawo sun san yadda ake cuta.Kuma su ne zamu sa su kaddamar maka saboda haka ka bar nan ko inkira yaran naka su lakadama dukan kawo wuka dakai da uban naka na isheku." Idi zai kirasu.
Gurgu ya gudu da sauri, Malam Idi ya kira su, suka iso amma Gurgu ya riga ya tsere.
Malam Idi ya ce:
"Gurgu ne nake so ku hukunta. Idan ya kara zuwa neman Ladidi, ku masa laga-laga!"
Yaran suka amsa:
"Munji, Baba. Komai yadda ka ce, shi za'a yi masa." Suka koma gurin zamansu.
๐บ Ku Ci Gaba da Kallo a NishadiSport
Ku biyomu domin jin cigaban wannan rikici mai sarkakiya.
Kada ku manta ku:
✅ Yi subscribe
✅ Ku yi like
✅ Ku bada sharhi da shawara
Mawallafi: Sadik Yusuf
๐ง Email: sadiku854@gmail.com
๐ฑ WhatsApp: 08148166212
๐บ Tashar YouTube: NishadiSport
๐ Blog: nishadisport.blogspot.com
Comments
Post a Comment