Soja ya far wa Idi
Soja Ya Diranwa Idi, Ya Bankado Sirrin sa!
Assalamu alaikum masu kallo da karatu a dandalin NishadiSport.
A yau cikin Episode 5 na shirinmu na Yar Malam mai cike da sarƙaƙiya da dariya, mun dawo zamuyi duba dangane da sabon rikici tsakanin Soja da Malam Idi, wanda ya ƙara dagula al’amura!
🔥 Soja ya fuskanci Idi!
Soja ya diranwa Idi yana masa kashedi.
"Na sani cewa Mama, matar Nomau, tana da ciki – kuma nasan kai da danka baku da gaskiya akan lamarin nan Kuna kokarin ganin cikin ya zube! Domin mugunta irin taku, to ina da labarin komai"
Soja ya ce:
"In wani abu ya samu cikin nan, ba zan bar ku lafiya ba wallahi na lahira sai ya fiku jin fadi!" Idi yana kallonsa, Idi ya cika da mamaki, wai ya akai yasan da zancen wannan ciki na matar Malam Nomau.
Malam Idi yace:
"Wayyo! Waye ya faɗa maka haka? Kuma a ina kaji"
Sai Soja ya ce:
"Zancen duniya baya buya…ko kana nufin karyane zaka gane kuranka ni kaga tafiyata." Idi yabishi da kallo ya kuma cewa: "kowane munafikinne ya gayamasa ai ko da nasan wanda yafada da na aikashi lahira." Idi yaj kwafa ya tashi ya tafi.
Faster film din Yar Malam
⚖️ Idi ya garzaya wajen Mai Gari!
"Soja yana min barazana! Yana cewa wai ni da ɗana muna ko karin zubarwa Mama ciki! Kuma narasa wanda ya gayamasa wannan maganar"
Mai gari ya dube shi da tausayi, amma ya ce:
"Toh Idi, ai Soja ba shi da wani iko a garin nan. Garin ai nawane ba nashi ba ne in yakawo wani wargi zan saita shi ya bar garin.Zan koreshi"
Ana haka sai ga Soja ya shigo. Da ya ga Idi a wajen Mai gari, ya gane cewa an kai ƙara a kansa. Ya zauna a a gaban mai gari ya kwashi gaisuwa. Mai gari ya hara reshi idi kuma ya zuba masa ido.
Mai gari ya fara masa gargaɗi:
"Don me zaka takura wa Idi? Ka saurara, da duk wani abu mara dadi zuwa gareshi idan ba haka ba, na karaji kayimasa wani barazana sai mun koreka daga garin don garin nawane ba nakaba kuma sai inga wanda ya daurema gindi." Soja ya murtuke fuska gami da hararar Malam Idi.
Soja ya ce:
"Yallabai, ni ba fada nake ba. Amma so ake a haɗani da kai domin anga tamu tazo daya da kai akeso a shiga tsakani na dakai to ko waye yake kitsa wannan lamari to karya yake!" Yana magan yana kallon Malam idi.Me Gari yana saurarensa.
Me gari:
"To shikenan ya isa haka katashi ka ban gurin banason jin wata magana daga gareka." Soja ya tashi ya tafi suna muzurai shi da idi ana kallan kallo.
📿 Duniya da Lahira
Soja ya na tafiya yaci gaba da magana:
"Ana haɗa kai da Uban kasa a ci dukiyar maraya! Ai duniya ba tabbatacciya bace, lahira ce abun dogaro. Allah ya kyauta."
Kajifa shima fa harin dukiyar yake yake ta wannan ban bami.
🧓 Tattaunawar Sani da Mahaifinsa
A wani bangare kuma, Mahaifin Sani yana tambayar ɗansa game da neman gidansu Ladidi Malam yace:
"Ka ga gidansu Ladidi kuwa?" Sani na sauraronsa.
Sani ya amsa:
"Har yanzu ban ga gidan ba. Yan garin sun ƙi gaya min, wai suna tsoron Dogo ɗan gidan Idi domin mugune kowa yana jin tsoro."
Mahaifin Sani ya ce:
"Ba komai. Za mu ci gaba da addu’a har Allah ya ba mu mafita."
Sani ya nuna godiya:
"Na gode da addu’ar ku, Malam. In sha Allah, komai zai daidaita kuma Ladidi xata samu mafita da ikon Allah."
Malam ya ƙara da faɗi:
"Allah yana son masu hakuri da kyautatawa. Muna fatan al’umma su zama masu yafiya da jinkai, domin nutsuwa da tsira."
Soja fai yasake zuwa gun idi.
Yasamu malam Idi yana gewaya gurin wani aiki da yasa ayimasa sai ya hango shh tafe saj ya hada rai soja ya karasa gurin da idi yake.
soja:
"to, ka kai karata gun mai gari to in gayama ko gun wa zaka kai kara ba zanfasa tona ma asiriba domin kai da danka mugayene kun hada kai da me gari zakuyi zalinci." Idi ya daka masa harara ya kura masa ido. Sai yace:
"wallahi ka fita daga idona kuma naji wai kana bibiyar matar Nomau wai kanaso ka aura sanoda tsabar iya tuggu to ba zaiyiwuba."
Soja yace:
"To saj kahana ta aureni tunda 'yar kace muzuba ni da kai munafiki." Idi yace: "to mu zuba mugani ai ni yafi dacewa da na aureta ba kaiba."
Soja:
"Yo sai kabari sai ta haihu ta zaba ni ko kai in kana da zarra mu futo ta zaba." Suna ta fada marasa kunya kowa mugun kansane Allah ya kyauta.
Mama tana fama
Mahaifiyar Ladidi wato Mama tana gida bata da lafiya saboda tashin nutsuwa da fargaba ga ciki tana dauke dashi.
Suku ma su Malam Idi suna faman ganin sun rabata sa wannan ciki, shi kuma Soja yana fafutukar aurenta.
To waze nasara? Waze fadi? Ladidi kuma tana ko karin ganin ta kare Mama daga dik wani tuggu.
Shi kuma Munzali Gurgu yana fafutikar lallai sai Ladidi ta soshi. Sani shi kuma yana fadi tashin ganin ya temaki Ladidi dangane da bin umarnin mahaifinsa,to karmi tuya mu manta sa Albasa a kwai mahaukaci dan gidan mai gari shi kuma mai dukan mutane, sai kima kawa mai taimakon Ladidi.
Haka dai aketa fafatawa a wannan shiri na Yar Malam a YouTube channel dinmu Mai suna NISHADISPORT.
Kammalawa
Al’amura na ƙara ɗaurewa. Shin Soja zaiyi nasarane?
Shin zargin ciki da ake yi zai bayyana gaskiyarsa?
Sani da Ladidi fa, ko mafita na kusa?
Ku biyo mu a YouTube Channel ɗinmu: NishadiSport,
Ku yi subscribe, ku danna like, ku rubuta ra’ayinku a comment section.
Muna tare da ku har zuwa ƙarshe.
wallafawa: Sadik Yusuf
📍 nishadisport.blogspot.com
📧 sadiku854@
Muna godiya masoya da ziyartar wannan shafi
ReplyDeleteMuna jiran comment
ReplyDelete