Burinsa ya cika

   Salamu alaikum waraha matullahi ta'ala wabaraka tihu, 
Sunana Sadiku yusuf. Nake gabatar muku da wannan labarai.

A cikin sharhin namu na yau zakuji abinda ke faruwa musamman dan gane da binne Alhaji Alhasan Dan Tata a birnin madina.

 Gwamnatin kano ta hada tawaga:

Kano ta hada wata tawaga mai karfi don halattar binne marigayin a madina, Wanda sun hada da:

1 Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
2 Gwamnan kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

 da manyan jiga jigan gwamnati, kuma harda Sarkin kano na sha biyar Alhaji Aminu Ado Bayero, shima anasa bangaren ya halicci ja na'izar, hukumar saudiyya ta amince da abinne marigayin wanda yai dai dai da wasiyyar da ya bari ,Allah ya cika masa burinsa na tabbata a kushewa a madina.

Inda ake dakon isowar gawar ta Aminu Alhasan Dan Tata a birnin na madina,iyalansa da yan uwa da abokan arziki duka suna wajen, da manyan baki harda mutane wanda suka futo ta ko'ina a duniya,duk sun halarci wajen janai'zar.

 An karrama wanda sukai hadarin mota

 A wani labarin kuma anyiwa iyalan wanda suka rasa ransu 
a hadarin mota su kimanin ashirin da biyar ,wato yan wasan da suka wakilci jihar Kano a kakar wasanni ta bana a hanyarsu ta dawowa bayan an kammala wasan.

 Iyalansu sun samu ta gomashi daga gwammnatin tarayya da ta jiha da kuma dai dai kun mutane ciki har da yan majalisu masu ci. Inda sanata "Barau Jibrin Maliya" yabada naira Milan ashirin da biyar.

Haka itama "Remu Tinubu" ta bada million dari haka itama tawagar gwammnatin tarayya ta bada nata taimakon ga iyalan.  Haka dai ake ta kawowa.

 Ita kuma gwammnatin Kano, tace baza'a manta da yan wasanba a dalin haka aka sanya sunan yan wasan a kwalejin wasanni  da kuma wasu mahimman gurare domin arika tunawa dasu da fatan Allah ya jikansu da rahama in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani amin.

Muna fata duk abinda aka bayar na gudummawa yaje inda ya dace kada ayi wakaci ka tashi da kudin Allah ya jikansu.

 Al'amuran yau da kullum:

 Sai sharhi kan al'amuran yau da kullum, yau zami dubane 
dangane, da Danjojin kan hanya wato futulin bada hannu,  da gwammnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf  ta samar dasu don bin doka da kai'dar titi,  kusan ko'ina cikin birnin Kano da kewaye ansa su.  

To amma wani abin ta kaici sai kaga mutane basa bin dokar wannan Danja , kowa inyazo baya san tsayawa, motoci manya da kanana har da babura masu kafa uku wato Adai daita sahu, da kuma kananan babura abin ba dadin  gani kuma hakan zai zama musabbabin hada hadari yakamata mutane su san cewa su akaiwa wannan danja dasu lura subi doka don samun saukin chinkoso.
 in mutum yayi hakuri baya wuce minti biyu azo kansa, sai mukula don samun cigaban birninmu baki daya, kuma in mutum ya lura zaiga cewa an kawata birnin da wa yan nan "Danjoji" da futulu. 

Anasa bangaren gwammna Alhaji Abba Kabir Yusuf yayi kira da kakkausar murya kan mutane su martaba doka ta kan titi a jihar kano don kaucewa fushin hukuma.

Inda yace za'a kafa kotun tafi da gidanka don hukunta duk wanda ta karya dokar hanya musammna karya dokar Danja wayo (traffic lights) da masu daga waya in suna tuki da masu aron hannu.

 Inda ya umarci hukumar (karota) ta jahar Kano takama ta hukunta duk wanda ya karya doka hakan yazama ba sani ba sabo.

Jama'a sai mukula mubi doka muhuta.


           Traffic lights 

Yan Sandan  zamfara sunkashe rikakken dan Bindiga:

 A wani labarin yan sandan jihar zamfara sun kashe rikakken dan bindiga da ya addabi wasu sassan jihar zamfara,wayo "Dan Bokolo" a cewar gwammnatin jihar ta bakin mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro wato Ahmad Manga inda yace:

"kisan nasa yasa ansamu gagarumar nasara saboda sun addabi jihar dake arewa maso gabas ta Nigeria wannan rikakken dan bindiga shine uban gidan (Bello Turji), yafi Bello Turji fitina kawai dai Bello Turji yafishi sunane inji Ahamad Manga. 

Wannan mutum yajanyo mutuwar akallah mutum dari ata bakinnasa."

 Ya rasa ransa:

Dan Bokolo yarasa ransane awata arangama da akai a kauyen Kurya tsakaninsa da yan sa kai na gwamnatin jihar.

Da kuma mayakan dan Bindigar, ana kallon kisan nasa a matsayin gagarumar nasara a wajen yaki da yan Bindigar.

Dan Bokolo ya dade yana addabar yankin zamfara wajen kai hare hare da kuma satar mutane domin kudin fansa,basa tausayin alumma kuma suna kiran kansu wai su musulmine ko wa yace haka mulunci yake.

 Shi mutumne mara imani ko kadan bai yadda da sulhuba kamar yadda dan uwansa "Bello Turji" yataba nunawa abaya inji wani mazaunin yankin.

 Allah ya kawo karshen zub da jini a arewacin Nigeria da diniya bakidaya amin summa amin.

Kuma hukima ta zage damtse tayi abin da ya dace a fire munafinci da son kudi asa kishin kasa a gaba, don ana zargin akwai hadin baki da jami'an gwamnati da kuma jami'an tsaro a vikin wannan lamari da yakici yaki cinyewa a wannan kasa mai tarin jama'a da din bin arziki.

 mai rubutu shine .Sadik Yusuf Kano.

 Za'a iya tun tubarmu a imel namu .
 Sadiku854@gmail.com. 

Comments

Post a Comment